Abu biyar da Trump ya yi suka shafi hannun jarin kasuwannin duniya

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Image
A ɗaukacin wa'adin mulki na biyu na shugaban Amurka Donald Trump, ƴan kasuwa da dama na zuba miliyoyin dala a harkar, kafin ya kai ga yin sanarwa kan muhimman sauye-sauye.
BBC ta yi duba yadda harkokin kasuwanni ke ciki, da kuma yadda wasu tsare-tsaren shugaban suka shafe su.
Mun gano cewa ana yawan samun hauhawar farashi cikin sa'o'i kaɗan, wasu lokuta kuma mintoci kaɗan, kafin shugaban ya wallafa rubutu a kafofin sada zumunta ko kuma tattaunawa da manema labarai.
Wasu masu sharhi sun ce hakan na nuna alamomin cinikin cikin gida ba bisa ka'ida ba, inda mutane ke yin musu kan bayanan da ba su kai ga bainar jama'a ba.
Wasu kuma na cewa lamarin na da tsarkakiya kuma wasu 'yan kasuwa sun ƙware wajen hasashen irin matakan da shugaban ƙasar zai ɗauka.
Ga wasu misalai biyar mafi mahimmanci.
9 ga Maris 2026: 'Yaƙi ya kusa zuwa ƙarshe'
Wasu manyan abubuwa da aka gani sun faru ne a ɓangaren cinikayyar mai.
Kwanaki tara da fara yaƙin Amurka-Isra'ila da Iran, Trump ya faɗa wa gidan talabijin na CBS cewa rikicin "babba ne kuma ya kusa kare wa".
- 07:29 : Farashin mai ya ƙaru
- 08:16 : Trump ya ce yaƙin ya kusa ƙare wa
- 08:17 : Farashin mai ya yi ƙasa da kashi 25
Karo na farko da mutane su kan san da batun tattaunawar shi ne karfe 8:16, lokacin da ɗan jaridar ya wallafa tattaunawar a shafin X.
Masu sana'ar harkokin mai sun yi martani da cewa yaƙin zai kare nan kusa ba kamar yadda aka yi tsammani ba, inda farashi ya ragu da kashi 25.
Sai dai, alkaluman kasuwanni sun nuna cewa an yi tsammani za a sayar da mai a kan wani farashi na daban da misalin karfe 7:29 - wanda ya kasance mintoci 47 kafin ɗan jaridar ya wallafa tattaunawarsa.
Ƴan kasuwar da suka yi tsammanin haka da za su iya samun miliyoyin dala na cinikin mai.
23 ga Maris 2026: 'Yunkurin neman sulhu a yaƙi'
A ranar 23 ga Maris, kwanaki biyu bayan barazanar tarwatsa tashoshin makamashin Iran, Trump ya wallafa a kafar sada zumunta ta Truth Social cewa Washington ta yi "Tattaunawa mai ma'ana kuma mai kyau" da Tehran kan "Kawo karshen yaƙi baki ɗaya".
Lamarin ya bai wa ƴan diflomasiyya da kuma ƴan kasuwa mamaki.
- Karfe 10:48-10:50 : Farsashin mai karu
- Karfe 11:04 : Trump ya wallafa kan "yunkurin kawo karshen yaƙi baki ɗaya"
- Karfe 11:05 : Farashin mai ya ragu da kashi 11
Jim kaɗan, hannayen jarin da suka ƙaru a kasuwar mai ta Amurka - sun yi kasa cikin sauri.
9 ga Afrilu 2025: 'Dakatar da lafta haraji'
Idan muka bar ɓangaren yaƙin Gabas ta Tsakiya, akwai wasu tsare-tsaren kasuwanci da gwamnatin Trump ta aiwatar waɗanda suka janyo cece-kuce.
A ranar 2 ga Afrilun bara, Trump ya sanar da abin da ya kira Ranar Ƴanci - wato lafta haraji kan kayayyaki daga kowace ƙasa a duniya.
Kasuwannin hannayen jari a duniya sun yi kasa a lokacin.
Sai dai, bayan mako ɗaya, Trump ya sanar da dakatar da sabbin haraje-harajen ga dukkan ƙasashe na tsawon kwanaki 90, amma ban da China, inda kasuwar hannayen jari ya yi tashin gwauron zabi.
3 ga Janairu 2026: Kama shugaba Maduro

Asalin hoton, Reuters
A watan Disambar 2025, wani mai amfani da kafofin sada zumunta ya kirkiro da wani shafi mai suna Burdensome-Mix. A ranar 30 ga Disamba, ya kalubalanci cewa za a tumɓuke shugaban Venezuela daga kan mulki a karshen watan Janairun 2026.
Tsakanin 30 ga Disamban 2025 zuwa 2 ga Janairu Burdensome-Mix ya buga caca da sanya kuɗi dala 32,500 kan lamarin.
Lokacin da dakarun Amurka suka kama Maduro da tumɓuke shi kan mulki washegari, Burdensome-Mix ya yi nasarar samun kuɗi da ya kai dala 436,000.
Jim kaɗan bayan haka, sai shafin ya sauya sunansa sannan daga nan bai sake buga wani caca ba.
28 ga Fabrairu 2026: Ƙaddamar da hari kan Iran
- Fabrairun 2026: An kirkiro da shafuka shida kan kan kafar Polymarket mai hasashe kan harkokin kasuwanci
- 28 ga Fabrairu: Shafin ya yi nasarar kuɗi dala miliyan 1..2A
Waɗannan shafuka sun yi hasashen ctare da saka cacar cewa Amurka za ta far wa Iran ranar 28 ga Fabrairu. Lokacin da shugaba Trump ya tabbatar da kai hare-haren a safiyar ranar da abin ya faru, shafukan sun samu kuɗi da ya kai dala miliyan 1.2.
Biyar cikin shafukan guda shida ba su sake buga caca ba har kawo yanzu, sai dai ɗaya daga cikinsu ya sake yin hasashen cewa za a tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ranar 7 ga Afrilu, wanda kuma Washington da Tehran suka sanar a wannan rana.
Da wuya a iya tabbatarwa
Wasu kasuwannin cikin gidasun kasance ba bisa ka'ida ba ga yawancin Amurkawa tun lokacin da aka zartar da wata doka a 1933.
A shekarar 2012 ne dai aka tsawaita wa'adin dokar zuwa ga jami'an gwamnatin Amurka, duk da cewa kawo yanzu babu wanda aka gurfanar da shi a karkashin dokar.
Paul Oudin, wani farfesa wanda ya kware kan dokar harkokin kuɗi, ya ce dokokin suna da wahalar aiwatarwa.
Oudin ya ce "Hukumomin kudi ba za su gabatar da kara ba idan ba za su iya gano waye mai laifi ba."
Babu hukumar Amurka ko ɗaya da BBC ta tuntuba da ta amince da duk wani zargi kan cinikin cikin gida.








