Ƴan Afirka 7 da ke cikin jerin attajiran duniya a 2026

Attajiran Afirka

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Attajiran Afirka bakwai sun samu shiga jerin attajirai 500 na duniya da Mujallar Bloomberg ta fitar cuikin watan Mayu.

A kowace shekara mujallar kan fitar da jerin attajirai da matsayinsu a duniya, da kuma irin arfin jari ko kadararsu.

Cikin jerin attaijiran 500 na duniya da mujallar ta fitar, Amurka ce take da kaso mafi yawa na attajiran, yayin da nahiyar Afirka ke da mutum bakwai kawai da suka samu shiga jerin.

Don haka ne cikin wannan muala muka zaƙulo attajiran na Afirka bakwai da suka samu shiga cikin jerin, da muka taƙaitaccen tahirinsu da ta dukiyar tasu.

Aliko Dangote 34.9B

Aliko Dangote

Asalin hoton, Getty Images

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka ya kasance mutum na 67 a jerin attajiran duniya 500 da mujallar Bloomberg ta fitar.

Mujallar ta ce dukiyar Dangote ta kai darajar dala biliyan 34.9.

Bloomberg ta ce attajirin na Afirka na kan gaba a harkar masana'antu, wanda cibiyarsu ke birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriya.

Shi ke da kamfanin siminti mafi girma a ƙasashen Afirka kudu da hamadar sahara.

Sannan ya zuba gagarumin jari a fannin makamashi, bayan da ya gina kafatariyar matatar man fgetur mafi girma a Afirka, wadda ta fara aiki a 2024.

Attajirin na kuma da tarin kamfanonin samar da abinci,a kamar sikari da gishiri da sauran kayan abinci da takin zamani.

An haifi Dangote a jihar Kano da ke arewacin Najeriya a 1957, kakansa Alhassan Dantata ya kasance attajirin ɗan kasuwa a Afirka ta Yamma da ya shahara a cinikin goro da gyaɗa.

Mahaifin Dangote ya rasu ne tun lokacin yana da shekara 8, lamarin da ya sa ya tashi a hannun kakansa na ɓangaren mahaifiyarsa, wanda ke sayar da kayan gine-gine.

John Rupert 18.9B

Ruparts

Asalin hoton, Getty Images

John Rupert, fitaccen attajiri ne da ya mallaki kamfanin samar da agogunan ƙasaita na 'Cie Financiere Richemont'.

Kamfanin, wanda ke ƙasar Switzerland, kan ƙera agogunan alfarma da suka haɗa da Jaeger-LeCoultre da Cartier.

Fitaccen ɗan kasuwa ne ɗan Afirka ta Kudu da ya mallaki kamfanonin Remgro, mai samar da ababen hawa a Afirka ta Kudu.

Mujallah Bloomberg ta saka attajirin ɗan kasuwar a matsayi na 144 a duniya, wanda ƙarfin jarinsa ya kai dala biliyan.

Rupert mai shekara 75 a duniya, na samu mafi yawan kuɗaɗensa daga kamfanoninsa ne ƙera agogunan alfarma.

An haife shi ranar 1 ga watan Yunin 1950 a Stellenbosch, kuma shi ne babba a wajen mahaifinsa, Anto Rupert, wani fitaccen attajiri a lokacinsa da ya shahara wajen mallakar kamfanoni.

Mahaifiyar Rupert, ita ma ƴarkasuwa ce mai suna Huberte.

Abdussamad Isiyaka Rabiu 18.5B

Shugaban kamfanin BUA

Asalin hoton, BUA group

Wani ɗan Najeriya, kuma ɗan jihar Kano da ya samu shiga jerin attajiran duniya 500, shi ne Abdussamad Isyaka Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA.

Mujallar Bloomberg ta saka Abdussamad a matsayi na 152 a duniya, wanda jarinsa ya kai dala biliyan 18.5.

Babban kamfaninsa na siminta shi ne na biyu mafi girma Najeriya, wanda a 2025 ya samu ribar naira tiriyan 1.2.

Baya ga siminta BUA ya kuma shahara a samar d akayan abinci, inda kamfaninsa na samar da taliya ya kasanmce na biyu mafi girma a ƙasar.

Hamshaƙin attajirin mai shekara 65, ɗa ne ga fitaccen ɗankasuwa a Isyaka Rabiu, wanda ya yi fice a fannin gine-gine.

Natie Kisrh 15.3B

Wani ɗan Afirka ta kudu da ya samu shige jerin attajiran duniya 500 shi ne Natie Kirsh.

Mujallar Bloomberg ta ce Kisrh na da ƙarfin jarin da ya kai dala biliyan 15.3.

Fitaccen ɗankasuwar ya yi fice a kamfanonin samar da abinci, musamman kamfanin sayar da abincinsa mai rassa a jihohin Amurka 35.

Mujallar ta ce Kirsh ya samu mafi yawan dukiyarsa ne daga kamfani sayar da abincinsa na alfarma mai suna Jetro Restaurant Depot LLC,

An haifi Natie a shekarar 1932 a Potchefstroom da ke Afirka ta Kudu, inda ya taso a gidan ƴankasuwa, kafin daga baya shi ma ya fara nasa kasuwncin bayan kammala jami'a, lokacin yana ɗan shekara 26, inda ya bar kamfanin iyayensa.

Nicky Oppenheimer 14.8B

Nicky Oppenheimer

Asalin hoton, Getty Images

Cikakken sunansa shi ne Nicholas Frank Oppenheimer,wanda kuma ya kasance ɗan Afirka ta Kudu na uku da ya shiga jerin attajiran duniya 500, da Bloomberg ta fitar.

Shi ne mamallakin babbankamfanin sarrafawa da cinikayya da kuma haƙar zinare mafi girma a duniya, mai suna 'De Beers'.

Mujallar ta saka ɗan kasuwar a matsayi na 211, wanda jarinsa ya kai dala biliyan 14.8.

Ɗan kasuwar mai shekara 80 ya samu mafi yawan kuɗinsa daga sayar da kashi 40 na hannayen jarin kamfanin De Beers da ya yi ga kamfanin Aglo American kan dala biliyan 5.2 a watan Agustan 2012.

An haife shi a ranar 8 ga watan Yunin 1945 a binrin Johannesburg na Afirka ta Kudu daga iyalan da suka shahara a sana'ar haƙar ma'adinai.

Kakansa Ernest Oppenheimer, shi ne ya kafa kamfanin haƙar ma'adinai na Anglo Americana a1917 a kusa da Johannesburg.

Nugaib Sawiris 11.7B

Naguib Sawiris ɗan asalin ƙasar Masar ya samu shiga jerin manyan attajiran duniya 500, da mujallar Bloomberg ta fitar.

Mujallar ta ce ya samu fiye da dala biliyan huɗu sakamakon sayar da hannayen jari kamfaninsa na sadarwa mai suna Vimpelcom a 2011 da 2012.

Mista Sawiri mai shekara 71 na da tarin kuɗi da kadarori da ya mallaka a ƙasashen daban-daban.

Bloomberg ta ce ƙarfin jarinsa ya kai dala biliyan 11.7

An haifi Naguib Sawiris ranar 15 ga watan Yunin 1954 a Masar, kuma shi ne babba a wajen mahaifinsa,Yousiriyya Onsi Sawiris.

Mahaifinsa ya kasance ɗa ga wani fitaccen lauya a lokacinsa da ya mallaki kamfanin gine-gine a 1950, wanda ya zama babban kamfanin gina tinuna da hanyoyin ruwa a yankin Kogin Nilu na Masar.

Nassef Sawiris 10.1B

Nassef Sawiri

Asalin hoton, Getty Images

Mutum na ƙarshe cikin jerin ƴan Afirka da suka samu shiga jerin attajiran duniya shi ne Nassef Sawiri ɗan uwa ga Nugaib Sawiris.

Nassef ya mallaki kashi 39 na hannayen jarin kamfanin OCI, katafaren kamfanin samar da takin zamanin nan na Netherlands da ya kafa bayan ya ɓalle daga kasuwancin gidansu na gine-gine.

A shekerar 2021 an bayar da rahoton cewa ya samu ribar dala biliyan 6.3.

Haka kuma Bloomberg ta ce Nassef na kashi 7 cikin 100 na hannayen jarin kamfanin Adidas.

Mai shekara 65 na da jarin da ya kai dala biliyan 10.1, kuma ya samu mafi yawan duniyarsa ne daga kamfaninsa na samar da takin zamani mai suna OCI.

An haife shi a a birnin Cairo ranar 19 ga watan Janairun 1961, kuma shi ne ɗa na uku, kuma na ƙarshe wajen mahaifinsu Yousiriyya Onsi Sawiris.