Wane ne Muhammad Minshawi: "makarancin Qur'ani"mai matuƙar alkunya

Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي
- Marubuci, Omaima Al-Shazly
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic - Cairo
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 9
"Haske daga haske kuma duniyar da ta fito daga wata babbar duniyar. Ba abin da wani zai ce game da shi face cewar shi dan itace ne mafifici da ya fado daga mafificiya." Da wadannan kalaman ne makarancin kur'anin nan na kasar Masar Marigayi Fatih Al-Maliji ya bayyana dan'uwansa Muhammad Siddiq Al-Minshawi.
Wannan murya mai dadin sauraro cikin girmamawa, wadda ta shahara a ko'ina cikin kasashen Larabawa da Musulunci, ba wata baiwa ce ta musamman ba a cikin zuri'ar gidan Al-Minshawi. Sheikh Muhammad Siddiq ya fito ne daga cikin tsatson mahaddatan Alkur'ani mai girma, kamar yadda ya fada a wata hira da ya yi da gidan rediyon Masar.
An bayyana gidan da ya fito a matsayin "Gidan Kur'ani"; Kakansa, Sheikh (Sayyid), da kakansa, (Tayyib) Al-Minshawi, dukkansu suna daga cikin mashahuran masu karatun kur'ani mai tsarki a kasar Masar, amma sun riga sun wuce ba tare da an taskace karatunsu ba, kamar yadda kawunsa (Ahmed Al-Sayyid) Al-Minshawi ya shuɗe.
Wasu bayanai da aka samun sun isar mana da wasu daga cikin abubuwan da mahaifinsa Sheikh Siddiq ya gada, wanda ake yi wa laqabi da "Mai kula da Karatu" a Masar, wanda kuma BBC ta dauka aiki domin bude gidan rediyon sashen Larabci a farkon zamaninsa, kamar yadda Fadia Muhammad Siddiq Al-Minshawi ta bayyana, da kuma fayafayan muryar da Sheikh Muhammad Siddiq da kansa ake sakawa a sashen Larabcin na BBC wanda ake budewa da karatu daga al'kurani mai tsarki.
Akwai wasu karatutuka na baya-bayan nan a gidan rediyon Masar na kaninsa Sheikh Mahmoud Siddiq Al-Minshawi, wanda dan'uwansa Muhammad ya rike a wurinsa har sai da ya kware a karatun Alkur'ani, wanda kuma ke raye har yau (2026).
'Yar Al-Minshawi, Fadia, ta kamanta danginta da bishiya, wanda Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya kasance "reshe a sama," inda ta bayyana mahaifinta a matsayin "wata mai haske duniya karatu" kuma "wani dutsen tawali'u'
Ya ƙi zuwa gidan rediyo, sai rediyo ya zo masa.

Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي
An haifi Sheikh Muhammad Siddiq Al-Sayyid Tayeb Al-Minshawi a birnin (Al-Munsha) a cikin gundumar Sohag da ke Masar a ranar 20 ga Janairu, 1920.
Ya kasance tare da mahaifinsa a kodayaushe, "kamar inuwa," kamar yadda ya fada da kansa, kuma yana da shekaru bakwai ya kammala haddar rubu'in kur'ani tare da kawunsa, Ahmed El-Sayed El-Minshawi, wanda ya raka zuwa Alkahira tsawon shekara guda.
Makaranta daya tilo da Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya sani ita ce ta karatun Alqur'ani. Baya ga mahaifinsa da kawunsa, Muhammad ya koyi karatunsa tun yana karami a wajen Sheikh Muhammad Al-Namaki, Sheikh Muhammad Abu Al-Ala, da Sheikh Rashwan Abu Muslim.
Yayi matukar alfahari da irin karatun da yayi a wajen Sheikh Muhammad Al-Saudi, masanin karatun kur'ani a birnin Alkahira, har ya sanyawa daya daga cikin 'ya'yansa sunansa.

Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matashin Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya fara gabatar da karatunsa na bainar jama'a na farko a kauyen Ubar Al-Malik da ke gundumar Akhmim kusa da Al-Minsha. Kudin farko daya fara samu shi ne pisters na Masar 10 a 1931 lokacin yana ɗan shekara 11.
Haduwarsa da rediyo ta fara ne tun yana dan shekara talatin, ta hannun wani abokinsa da ya shaida wa Amin Hammad, daya daga cikin manya shugabannin gidan rediyon Masar game da shi. Hammad ya bukace shi da ya zo birnin Alkahira, amma matashin makarancin ya ki yarda da wannan tayin domin ba ya son tafiya wajen yankinsu wato Upper Egypt a watan Ramadan.
A wancan lokaci matashin mai karatun na azumin watan Ramadan ne a birnin Esna na lardin Luxor, don haka gidan rediyon Masar ya yanke shawarar tura wata tawaga zuwa wajensa waddza ta yi tafiya mai nisan kilomita kusan 700 acikin sa'o'i 10, inda ta aike da na'urorin na'urar nadar karatu karkashin kulawar darakta Saeed Abu Al-Saad.
Tawagar gidan rediyon ta dawo inda ta gabatar da wannan karatu ga wani kwamiti na musamman, ta yadda a hukumance aka amince da shi a matsayin mai karatu a gidan rediyon a shekarar 1953, kuma aka saka shi a cikin babban rukunin makaranta da ake saka karatunsa da karfe takwas na yamma, kuma bayan haka ne Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya koma "Siddiq Al-Arba'a" wanda muryarsa ta soma zagaya duniya tun daga lokacin.
''Masallacin Al-Aqsa shi ne rayuwarsa"

Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي
Ya kasance abu mai wahala makarancin ya tashi daga Sohag zuwa Alkahira don nadar karatu a kowane lokaci, domin Larabawa sun saba jin muryarsa duk ranar Laraba da yamma, don haka ya yanke shawarar komawa birnin Alkahira da zama.
Sheikh Al-Minshawi ya sami wurin zama a unguwar Citadel da ke tsohuwar Alkahira lokacin ne ya fara sanin babban birnin Masar. Yana son tafiya a kasa daga gidansa zuwa Masallacin Imam Hussein, kamar yadda iyalansa suka shaida wa BBC. Idan ya hau motarsa sai ya umurci direban da ya sauke shi a wuri mai nisa kafin masallacin domin ya taka masallacin na Imam Husaini.
Bayan haka ne ya koma Unguwar Hadayeq El Qubba a wani gidan kasaita dake kan titin Hafni Nasif, kafin ya koma wani gida a unguwar da ya gina, ya gina wani dan karamin masallaci a karkashinsa bisa shawarar wani abokinsa Kirista, kamar yadda ya fada a wata hira, kuma ya sanyawa sunan mahaifinsa Sheikh Siddiq Al-Minshawi.

Asalin hoton, Ahmed Tarek El-Menshawy
Alkahira ita ce mafarinsa na yawo a duniya, inda ya fara ziyararsa ta farko zuwa kasar Indonesia a shekarar 1955. Kasar Siriya ita ce kasa ta farko ta Larabawa da ta karbi bakuncinsa a shekarar 1956 bisa gayyatar da gidan rediyon kasar ya yi masa a can, inda ya zagaya tsakanin kasashen Iraki, da Jordan, da Saudiyya, da Libiya da kuma Aljeriya.
A wata hira da gidan rediyon Masar ya yi da shi kasa da shekara biyu kafin rasuwarsa, ya bayyana cewa ya yi karatu a masallatai uku mafiya daraja a Musulunci: Masallacin Harami da ke Makka, da Masallacin Annabi da ke Madina, da kuma Masallacin Al-Aqsa da ke Kudus.
Diyarsa Fadia ta shaida wa BBC cewa yana jin dadin tafiye-tafiyensa zuwa masallacin Al-Aqsa, wanda yakan ziyarta kuma yana "sonsa sosai".
Ta kara da cewa yana matukar sha'awar masallacin Al-Aqsa saboda tsarin gininsa da kuma zamansa wuri mai tsarki, kuma a duk lokacin da ya tashi zuwa Kudus ya kasance "a cikin kololuwar farin ciki," wanda ke bayyana a cikin karatunsa, sabanin karatunsa a duk wani wuri da muryarsa ta fito.
Fadia ta bayyana irin tsananin soyayyarsa da masallacin inda ta ce "Masallacin Al-Aqsa shi ne rayuwarsa," har sai lokacin da ya daina karatu a cikinsa, bayan yakin kwanaki shida na 1967 tsakanin Isra'ila da kasashen larabawa da mamayar Gabashin Kudus.
"Cikar kamala"

Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي
Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya yi suna da karatu cikin sauti na kaskantar da kai da taqawa, har aka yi masa laqabi da makaranci mai kuka. Dr. Nabil Hanafi, masanin tarihi kuma masanin fasaha, ya kira shi "Sarkin Karatu", yana mai bayyana muryarsa a matsayin "wata kyakkyawar murya mai dauke da sigar alhini da kunne ba zai iya gajiya da saurare ba."
Hanafi ya kara da cewa a cikin wata makala ta jaridar Al-Qahira cewa muryarsa ta hada abubuwa masu karfi da dadi da kuma jin dadin kowane sinadari, wanda hakan ya sanya muryar tasa ta zama wata ta daban a duniyar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Masar da kuma duniyar musulmi a karnin da ya gabata.
Ismail Dweidar daraktan gidan radiyon kur'ani mai tsarki ya shaidawa BBC cewa Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya nadi dukkan kur'ani a shekarar 1965, shekaru hudu kacal kafin rasuwarsa, kuma fiye da shekaru 10 bayan da gidan rediyon ya amince masa.
An nadi kur'ani a cikin muryarsa a cikin kaset 82 wanda wani kwamitin sauraren karatu ya yaba, wanda ya hada da Dr. Muhammad Abdullah Madi, mataimakin kungiyar Azhar, Sheikh Amer Othman, Shehin Malamin Al-Kur'ani na Masar, Sheikh Mahmoud Baraniq, Farfesan Karatu, Sheikh Ibrahim Shehata, wanda kuma yana daya daga cikin manyan malamai da malaman karatu da sauran su.
Duk da wannan yabo, Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya mika bukatarsa ga babban mai kula da shirye-shiryen al'adu, bayan ya saurari dukkan faifan da ya dauka, ta ya sake nadar kaset-kaset 32, wadanda a cikinsu yake ganin zai iya gabatar da karatun da ya fi wanda ya riga ya gabatar, wanda babu kura-kurai kuma sune ake saurare har yau.

Asalin hoton, مكتبة أبناء الشيخ المنشاوي
A cewar Dawidar, wasikar bukatar Al-Minshawi yana cewa:
"Na saurari karatun da aka nada a cikin muryata a cikin ruwayar Hafs, sai na ga domin in kammala karatun ta yadda nake jin cikar abin da ake bukata don manufar da aka yi wannan karatun, ina son sake nadar kaset-kaset din kamar yadda bayani ya gabata."
Kwamitin ya amince da bukatarsa ta "kokarin neman kamala," a cewar daraktan gidan rediyon kur'ani mai tsarki. Makarancin ya sake nada kaset 32 a shekarar 1966, kuma kwamitin ya saurare su, ya yaba musu, ya kuma amince da su a shekarar 1967.
Duk da haka, faifan bidiyo da aka inganta ba su kai ga kunnen masu sauraro ba sai bayan shekaru 60, saboda "karatun na farko ba shi da lahani kuma mutane sun yarda da shi," har sai da Dweidar ya yanke shawarar bude wannan "taska" fiye da rabin karni bayan mutuwarsa.
Kamar yadda 'ya'yan Sheikh Muhammad Siddiq suka ce, akwai faifan kur'ani a cikin muryar Al-Minshawi da har yanzu ba a bayyana ba, daya daga cikinsu yana da riwayar Al-Duri daga Abu Amr Al-Basri a shekara ta 1963, wani kuma ya zo a ruwayar Warsh ta Nafi'u a shekara ta 1965, da na uku na ruwayar na Nafi'u
Ɗa kamar ɗan'uwa, ɗan'uwa kuwa kamar ɗa

Asalin hoton, موقع صحيفة الأهرام
Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi ya yi aure sau biyu. A karon farko shi ne da 'yar kawunsa, Bahia, lokacin yana da kimanin shekaru 16. Auren wuri al'ada ce ta mutanen zamanin, musamman a Yankin upper Egypt.
Shekarun da ya yi aure kusan shekarun da aka yi auren babban dansa ne, wanda yake kallon kusa da shi "kamar shi dan'uwa ne a gare shi," a cewar Fadia 'yar Sheikh Muhammad Al-Minshawi, yayin da bambamcin da ke tsakanin shi Sheikh Muhammad da kaninsa Sheikh Mahmoud shekaru 23 ne.
Sheikh Muhammad ya haifi 'ya'ya uku da Uwargida Bahiyya tun a farkon rayuwarsa, namiji daya da mace biyu, kafin daga bisani ya auri Na'ima wadda suka haifi maza da mata 9 tare da ita, ya dai haifi 'ya'ya 12 maza 6 mata 6.
Duk da cewa Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi bai yi karatu a makarantar boko ba, amma ya himmantu wajen tarbiyyantar da dukkan 'ya'yansa, kuma ya ba su kulawar makaranta, tare da kwadaitar da su wajen kammala haddar Alkur'ani da "karfafawa".
Sai dai babu daya daga cikinsu wanda ya bi sahun mahaifinsa wajen zama kwararre a karatun Alkur'ani, kamar yadda Fadiya ta kara da cewa, a cikin wata tambaya "Wa zai iya bin Sheikh Muhammad?!
''Ihun mata daga saman rufin ''

Asalin hoton, أرشيف الصحافة المصرية بموقع مكتبة الاسكندرية
'A shekarunsa na baya, Sheikh Muhammad Siddiq al-Minshawi ya yi fama da ciwon makogwaro, kuma likitoci sun shawarce shi da kada ya matse muryarsa a lokacin karatu. Sai dai ya ci gaba da karatun Al-Qur'ani har zuwa wata biyu kafin rasuwarsa, bayan da ya yi fama da haɓo.
Allah ya yi wa Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi rasuwa a Asibitin Maadi da ke birnin Alkahira a ranarJuma'a 20 ga watan Yuni 1969 yana da shekaru 49 a duniya.
An yi jana'izarsa a kauyensu na Al-Munsha'a a zamanin rayuwar mahaifinsa Sheikh Siddiq wanda ya yi alkawarin kula da jikokinsa.
Dr. Nabil Hanafi, masanin tarihi kuma masanin fasahar kere-kere, ya bayyana cewa yana gidan iyalansa da ke birnin Qus a gundumar Qena a cikin Upper Eygpt, lokacin da mutane suka yi mamakin yada aka saka karatun da Sheikh Muhammad Siddiq da karfe takwas na yammacin ranar Asabar.
Jama'a na dakon karatun Sheikh Abdul Basit Abdul Samad ne kamar yadda aka saba a yammacin ranar Asabar, "yayin da jama'a suka saba jin muryar Sheikh Al-Minshawi a yammacin ranar Laraba ta kowane mako, sai kawai ji sanarwar rasuwar shehin malamin bayan kammala karatun."
Hanafi ya kara da cewa: "Ba zan taba mantawa ba, muddin ina raye, kururuwa da kukan da mata suka yi a saman rufi a wannan dare, a lokacin da suka samu labarin cewa "Sahibin Laraba" ya rasu bayan ya saka mutane farin ciki da karatunsa."
Karatun Sheikh Muhammad Siddiq Al-Minshawi na ci gaba da yawo a gidajen radiyo a duk fadin duniya tare da yawo a cikin al'ummomin da suke ganinsa a zaman wata ilhama, wata rayuwa ta daban kuma murya ta musamman a duniyar karatu.
Wani daga cikin masu sha'awar karatunsa ya siffanta shi da cewa: "Matafiyi daga doron duniya har zuwa wajen mala'iku, kuma shi ne wannan muryar ta tuba dake ce maka: Zauna, ga wata zuciyar da ke magana da Alkur'ani










