Masu riƙe da muƙamai 5 da aka taɓa yin garkuwa da su a arewacin Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin ceto Alƙalin Babbar Kotu a jihar Kebbi mai shari'a Faruku Hassan Bunza da ƴanbindiga suka sace.

A ranar Asabar ne da daddare ne wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka auka gidan alƙalin tare da sace shi.

Bayanai sun ce alƙalin ya koma gidansa daga bulaguron da ya yi zuwa jihar Sokoto kafin faruwar lamarin.

Kwamishinan ƴansandan jihar CP Umar Muhammad Haɗejia ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar.

Tuni dai iyalansa suka yi kira da jami'an tsaro da hukumomi su tsananta ƙoƙari domin ceto shi.

Sace alƙalin na zuwa ne kwana guda bayan da wasu ƴanbindiga suka sace shugaban ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar Zamfara mai maƙwabtaka.

Ba wannan ne karon farko da ƴanbindiga a arewacin ƙasar ke sace masu riƙe da muƙamai ba.

A wannan muƙala mun duba wasu fitattun masu riƙe da muƙamai da ƴanbindigar suka taɓa sacewa a arewacin ƙasar.

Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu

A ranar Juma'a a daddare ne wasu ƴanbindiga suka ƙaddamar da hari a garin Bunguɗu a jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Nura Umar Bungudu da kuma wasu daga cikin makusantansa.

Bayan shugaban ƙaramar hukumar, maharan sun yi garkuwa da wani ma'aikacin asibitin tarayya da ke Gusau da wani mai sana'ar cire ta kuɗi ta POS a yankin.

Haka kuma rahotannin sun ƙara da cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro, ciki har da ƴansanda da ƴan sa-kai.

Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce jami'anta na bibiya tare da yunƙurin ceto shi.

Hon Sani Bello, ɗanmajalisar wakilai

A ranar 2 ga watan Agustan 2016 ƴanbindiga suka sace Hon. Sani Bello ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Mashi/Dutsi a jihar Katsina a gonarsa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Bayanai sun ce ƴanbindigar sun saki bayan kwanaki uku a hannu, bayan biyan kuɗin fansa.

Daga bisani ƴansandan sun ce sun samu nasarar kama maharan a wani yanki na jihar Katsina, waɗanda kuma suka tabbatar da cewa su ne suka maka Hon. Bello.

Shugaban UBEC

Shi ma tsohon shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta Najeriya, UBEC, DR Mahmood Abubakar ya taɓa faɗa wa komar ƴanbindiga a lokacin da yake kan muƙaminsa.

A lokacin faruwar lamarin ƴanbindigar sun harbe direbansa, wanda ya mutu nan take.

Daga baya jami'an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da su daga hannun masu garkuwar, tare da kama wasu daga ciin masu garkuwar.

Manyan sarakunan da ƴanbindigar suka taɓa sacewa

Baya ga masu riƙe da muƙaman gwamnati ma akwai wasu masu riƙe da sarautun gargajiya da suka taɓa faɗawa komar ƴanbindigar.

Wasu daga cikinsu, sun fuskanci cin zarafi, yayin da wasu ma suka mutu a hannun ƴanbindigar.

Ga wasu daga cikin jerin manyan sarakunan arewacin Najeriya da ƴanbindigar suka taɓa sacewa.

Sarkin Gobir

Sarkin Gobir na garin Gatawa, Marigayi Alhaji Isa Bawa na ɗaya daga cikin fitattun masu riƙe da mukamai daga faɗa hannun ƴanbindiga a arewacin Najeriya, wanda kuma har ya mutu a hannunsu.

Wani ɗan sarkin na ya ce an kama mahaifin nasa ne a wani kwanton-ɓauna a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa gida daga wani taro da ya halarta.

Marigayin ya shafe makonni masu yawa a hannun masu garkuwar waɗanda suka riƙa yi masa bidiyon cin zarafi.

Sarkin Bungudu

A cikin watan Satumban 2025 ne wasu ƴan bindiga suka sace Sarkin Bungudu da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya, mai martaba Alhaji Hassan Attahiru.

Ƴan bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda BBC ta ji daga ɗaya daga cikin ƴaƴansa da kuma basarake a masarautar Zannan Bungudu Abdulmalik Zubairu.

Bayanai sun ce an kashe ɗaya daga cikin jami'in ƴan sandan da ke tare da shi a musayar wuta da ƴan bindigar a hanyar Abuja daga Kaduna.

Mai martaba Alhaji Hassan Attahiru yana cikin sarakunan Zamfara masu daraja ta ɗaya.

Sarkin Kajuru

A ranar 11 ga watan Yulin 2025 ma ƴanbindiga sun sace sarkin Kajuru a jihar Kaduna Alhaji Alhassan Adamu.

An sace sarkin da wasu iyalansa su 13 a wani harin da 'yan bindigar suka kai a masarautarsa.

Bayanan da suka fito a lokacin sun nuna cewa sarkin ya gudanar da taro kwana daya kafin nan, kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa.

Yan kwanaki bayan haka kuma aka sako sarkin mai shekaru 85.

Sarkin Jaba

Makonni biyu bayan sace Sarkin Kajuru ne shi ma Sarkin Jaba Jonathan Danlin Gyet Maude ya faɗa hannun ƴanbindiga.

Sai dai shi Sarki Jonathan Maude an sace shi ne yayin da ya kai ziyara wata gonarsa a yankin Panda na Jihar Nasarawa.

Masu garkuwar sun buƙaci naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa a lokacin.

An kuma sako shi bayan kwana guda yayin da ƴanbindigar suka ci gaba da tsare wasu mutum 13 da suka sace tare da shi.

Sarkin Rubochi

A watan Nuwamban 2019 ƴanbindiga suka yi awon gaba da sarkin garin Rubochi da ke hukumar Kuje ta Abuja.

An sace Etsu Mohammed Ibrahim Pada ne da misalin karfe biyu na daren Talata 27 ga watan Numamban 2019 bayan da suka kutsa kai cikin gidansa.

Babu bayanai da su ka nuna cewa an biya kuɗin fansa kafin a sako shi.

Sarkin Wammako

A jihar Sakkwato da ke arewacin Najeriyar an taɓa sace sarkin Wamakko Alhaji Salihu Baraden Wamakko a ranar 9 ga watan Maris ɗin 2015.

Kamar Sarkin Kajuru, shi ma maharan sun ɗauke shi ne a masarautarsa.

Basaraken yaya ne ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Kuma shi ma an sako shi bayan wani lokaci.

Sarkin Bukkuyum

Har wayau a ranar 21 ga watan Maris ɗin 2015 mahara suka sace Sarkin Bukkuyum mai Martaba Alhaji Muhammadu Usman a jihar Zamfara.

Ƴan bindigar sun sace sarkin a masallacin kofar gidansa bayan Sallar Magriba ranar wata Juma'a.

Kafin nan sai da suka yi harbe-harbe na tsorata jama'a kafin su yi awon gaba da sarkin mai daraja ta daya.

Sai dai kasa da mako guda da garkuwa da sarkin ne yan bindigar suka sako shi.