Zelensky ya gode wa Trump kan goyon bayan Amurka ga Ukraine
Shugaba Zelensky na Ukraine ya godewa shugaba Trump kan abin da ya kira cikakken goyon bayan Amurka bayan ganawar da suka yi a fadar White House.
Ya wallafa sako a shafin sada zumunta, kan cewa sun tattauna kan lasisin Ukraine na kera makamai masu linzami, da sauran dabarun yaki da Rasha.
Shi ma Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya isa fadar ta White House jim kadan bayan tafiyar Zelensky.
Wannan karon an yi tattaunawar ne a cikin sirri ba kamar wadda aka yi a shekarar da ta gabata a Oval office ba da ya janyo cece-kuce.
Alamu sun nuna Zalensky ya ji dadin ganawar da ya fito cike da farin ciki.
Wannan ne karon farko da Netanyahu ke ganawa da Mr Trump tun bayan ƙaddamar da harin haɗin gwiwa kan Iran.