Manyan birane 10 da suka fi daɗin zama a duniya a 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wan sabon kundin nazarin yanayin tattalin arzikin duniya na mujallar 'The Economist' ya bayyana birane 10 da suka fi daɗin zama a duniya a wannan shekara ta 2026.

Rahoton an shekara-shekara ya yi nazarai kan birane 173 na duniya kafin fitar da rahoton nasa.

Mujallar kan yi nazarain abubuwa a biranen da suka haɗa da kwanciyar hankali da tsarin kiwon lafiya da al'adu da muhallai da ilimi da kuma abubuwan more rayuwa kafin tantance matsaytin da zai bai wa kowane birni.

Rahoton ya ƙara fito da yadda ƙasashen Turai ke ci gaba da kankane wuraren da suka fi dadin zama a duniya, yayin da yankin Australia ke biye.

BBC ta duba rahoton tare da bibiyar mazauna wasu daga cikin biranen domin jin yadda suke gudanar da rayuwa a cikinsu.

Waɗanne birane ne?

1.Copenhagen

Babban birnin ƙasar Denmark ne kan gaba a jerin, wadda kuma ta kasance a matsayin shekara biyu a jere.

A cewar Mujallar Copenhagen na da kyakkyawan tsarin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ingantaccen tsarin ilimi da abubuwan more rayuwa, kuma birnin na cikin mafiya kyawawan al'adu da ɗabi'un mazaunansa.

Ga mazauna birnin, rayuwa a birnin na cike da abubuwan jin daɗi da yalwar lokaci da kuma yin abubuwan nishaɗi haɗe da sauƙin rayuwa.

"Za ka iya hawa keke ka je wurin aiki, sannan bayan ka tashi ka je wurin ninƙaya, daga baya kuma ka koma gida domin cin abincin dare. Wannan abu ne na yau da kullum a nan duka a rana guda," a cewar Laura Amira Qassem, wata ɗalibar likitanci kuma mai bincike wadda ta shafe shekara takwas tana zaune a birnin.

Ta ƙara da cewa Ingantattun titunan kekuna da tsaftar ruwan birnin da ya dace da ninƙaya, kuma girman birnin da ya dace da tafiya a ƙafa ko hawa keke''

Wani abu da Laura ta ce ba ta taɓa gani ba.

2. Vienna

Duk da cewa a shekarar da ta gabata ne birnin na ƙasar Australia ya ra rasa matsayinsa na ɗaya, amma ingantaccen tsarin kiwon lafiya da iliminsa ya sa shi a matsayi na biyu, cikin birane mafiya dadin zama a duniya.

Ga mazauna Vienna kuwa, rayuwa a birnin ta ta'allaka ne kan sauƙin zirga-zirga, ko ta hanyar ababen hawa ko kuma tafiya a ƙafa, da kuma jin daɗin rayuwar tituna.

Franziska Hochmüller, wadda ke aiki da Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Vienna, ta ce:

"Ayyukana na yau da kullum sun haɗa da hawa ɗaya daga cikin shahararrun jiragen ƙasan birnin zuwa wurin aiki."

"Maimakon in kasance ina duba wayata, na fi son karanta littafi ko kuma kallon kyawawan gine-ginen da nake wucewa a hanyata. Wannan na tunatar da ni a kowace rana yadda rayuwa a Vienna take da ban mamaki, duk da cewa abubuwan da ke cikinta na yau da kullum ne."

3. Melbourne

Birni na uku mafi daɗin zama a 2026 kamar yadda mujallar 'The Economists' ta bayyana shi ne Melbourne.

A matsayinsa na birni na biyu mafi girma a duniya, Melbourne ya kasance ɗaya daga cikin birane masu kyawawan al'adu da tsarin muhalli mai kyau.

Ga mazauna birnin, bambancin al'adu na daga cikin abubuwan da ke ɗaukar hankali da sanya nishaɗi, inda kowace unguwa ke da nata salo da kuma irin kamanninta al'adunta.

Anne-Marie Lennon, babbar manajar babban kantin sayar da kayyaki na Crowne Plaza Carlton, wadda ta yi aiki a Birtaniya da Ireland da Australia, ta ce:

"Melbourne babban birni nemai yanayin rayuwa irin na ƙaramin gari, inda mutane ke kusantar juna."

"Mutane a nan suna son sanin juna sosai. Haka kuma akwai al'adu da abinci da kiɗe-kiɗe da kayan kwalliya da fasaha. Kowace unguwa tana da nata yanayi da kuma asalin da ya bambanta ta da sauran unguwanni."

4. Sydney

Sydney wanda shi ne babban birnin ƙasar Australiya ya kasance ya kasance a matsayi na hu,du cikin wannan jeri.

Mazauna birnin sun ce birnin na ƙunshe da tarin abubuwa na yanayi, da ɗimbin al'adu, da sauƙin rayuwa.

Steve Kemper, Ministan Ayyuka da yawon buɗe Ido na Jihar New South Wales (NSW), ya ce: "duk inda kake a birnin Sydney ba za ka yi nisa da kyawawan wurare da abubuwan gani ba, kama daga ruwa zuwa kyawawan tsaunukan Blue Mountains ko kuma rairayin bakin teku."

Ya ƙara da cewa haɗuwar al'adu daban-daban da unguwanni iri-iri da abinci masu daɗi da kuma salon rayuwa su ne abubuwan da suka sa Sydney ta zama ta musamman. Birni ne na duniya da ke ɗaukar yanayi na zaman mutane cikin kwanciyar hankali''.

"Sydney kuma birni ne mai yawan jama'a daga mabambantan al'adu da asali. Akwai abinci iri-iri masu kyau da kuma mutane daga sassa daban-daban na duniya, haka kuma a lokaci guda birnin na da yanayin natsuwa kuma ba ya cunkushe da jama'a sosai. Wannan haɗuwa ta siffofi abu ne da ba kasafai ake samu a babban birni ba," kamar yadda ya yi ƙarin haske.

5. Zurich

Birnin Zurich na ƙasar Switzerland ne a matsayi na biyar cikin jerin biranen duniya mafiya daɗin zama a 2026 a cewar mujallar 'The Economists'.

Mazauna birnin sun ce haɗuwar ingantaccen tsarin rayuwa da kuma sauƙin zuwa wuraren da ke da yanayi na halitta su ne ginshiƙan rayuwa mai inganci da birnin na Zurich.

Manuela Leonard, wadda haifaffiyar Zurich ce, ta ce " binrin Zurich ya wadata da kyawawan tafkuna da koguna masu ɗaukar hankali''.

''A kowace rana nakan yi tafiya a gefen Tafkin Zurich da Kogin Limmat ko Kogin Sihl, kuma hakan yana ba ni damar samun lokaci na kaina," in ji Leonard.

"Ruwan kogunan mai tsabta ne, sannan akwai wuraren hutawa fiye 1,200 da aka tanada a sassa daban-daban na birnin," in ji ta.

Duk da cewa ta shafe rayuwarta gaba ɗaya a Zurich, Leonard ta ce har yanzu tana ci gaba da mamakin yadda birnin yake da tsabta da kuma yadda ake kula da shi sosai.

Sauran biranen 5 da ke kan gaba

  • Geneva
  • Osaka
  • Adelaide
  • Vancouver
  • Tokyo