Man Utd na da damar sayen Leao da Bowen, Barcelona na son Kiwior

Hoton Rafael Leao

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ce take da damar da ta fi ta sayen Rafael Leao, mai shekara 26, inda aka sanya wa dan wasan na gaba na gefe na AC Milan da Portugal farashin fam miliyan 43. (Gazetta Dello Sport)

Haka kuma United din za ta iya neman dan wasan gaba na West Ham da Ingila Jarrod Bowen, mai shekara 29, idam Hammers din suka fadi daga gasar Firimiya. (Football Insider)

Chelsea ta amince ta sayi tsohon dan baya na gefe na Brighton Valentin Barco, mai shekara 21, dan kasar Argentina daga kungiyar Strasbourg mai alaka da Blues din. (Mail)

A shirye mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker, dan Brazil mai shekara 33, yake ya tafi Juventus inda zai sake hadewa da tsohon kociyansa a Roma Luciano Spalletti, ko da kuwa Juventus din ba ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ba. (Corriere Dello Sport)

Chelsea na son tsohon dan bayanta Thiago Silva, mai shekara 41, ya koma ya zama kociya a kungiyar bayan da ya bar Porto - amma kuma AC Milan ta yi wa dan Brazil din tayin kwantiragin shekara daya don ya ci gaba da yi mata wasa. (ESPN Brasil)

Kila Leeds United ta sayi dan wasan tsakiya na Southampton Shea Charles, mai shekara 22, bayan da dan wasan na tawagar Ireland ta Arewa ya rasa damar samun shiga gasar Firmiya saboda badakalar leken asiri da aka samu Southampton da ita. (Football Insider)

Barcelona na nazari a kan tsohon dan bayan Arsenal Jakub Kiwior, wanda yanzu yake Porto, saboda tana ganin dan wasan na tawagar Porland mai shekara 26, zai iya dacewa da ita a neman da Zakarun na La Liga suke yi na sabon dan baya. (Sport)

Brighton da Crystal Palace na daga kungiyoyin Firmiya da suke son dan wasan tsakiya na Bayern Munich Arijon Ibrahimovic mai shekara 20, ganin yadda Bajamushen ya taka rawar-gani a zaman aro da ya yi a Heidenheim. (Teamtalk)

Aston Villa na son mai kai hari na Denmark William Osula, mai shekara 22, amma kuma Newcastle ta ce ba na sayarwa ba ne bayan da ya samu shiga cikin gwanayen da kociyan kungiyar Eddie Howe yake sanyawa a wasa sosai. (Football Insider)

MMai neman mukamin shugaban Fenerbahce Hakan Safi yana son sayen mai kai hari na Marseille Mason Greenwood, dan Ingila mai shekara 24, a shirin da yake na bunkasa kungiyar ta Turkiyya. (Goal)