Milan na zawarcin Spence da Romero, Liverpool ta dage kan Sano

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan na ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar ɗauko mai tsaron baya na Ingila daga Tottenham, Djed Spence, mai shekara 25, da kuma ɗan bayan tsakiya na Argentina Cristian Romero, mai shekara 28. (Corriere dello Sport)
Liverpool ce ke kan gaba a fafutukar zawarcin ɗan wasan tsakiya na Japan Kaishu Sano daga Mainz. Rahotanni sun ce kungiyar na shirin kashe har yuro miliyan 60 (£50.9m) domin ɗaukar ɗan wasan mai shekara 25, wanda kuma ɗaukar hankalin Arsenal da Tottenham da kuma Borussia Dortmund. (Teamtalk)
Arsenal ta nuna sha'awar ɗaukar mai tsaron bayan Ingila na Aston Villa, Ezri Konsa, mai shekara 28. (Guardian)
Haka kuma Liverpool ta tuntubi Bournemouth game da matashin ɗan wasan gaba na Brazil Rayan, mai shekara 19, yayin da take son sake haɗa shi da tsohon kocinsa Andoni Iraola. (Teamtalk)
Mai tsaron ragar Argentina Walter Benitez, mai shekara 33, na iya raba gari da Crystal Palace domin komawa tsohuwar kungiyarsa ta Faransa, Nice. (Nice-Matin)
Newcastle United na tattaunawa da mai tsaron ragar Brighton, Carl Rushworth, mai shekara 25. Haka kuma kungiyar na tattaunawa da ɗan Ingila James Trafford, mai shekara 23, wanda ke taka leda a Manchester City. (Mail - requires subscription)
Fulham ta shiga sahun Coventry City da Chelsea wajen bibiyar ɗan wasan gefe na Ivory Coast daga Strasbourg, Martial Godo, mai shekara 23. (Africafoot)
Ipswich Town ta yi ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan gefe na Ghana daga Leicester City, Abdul Fatawu, mai shekara 22. (Telegraph)
Crystal Palace na sha'awar sayen mai tsaron bayan Augsburg, Chrislain Matsima, mai shekara 24. Ɗanwasan na Faransa na cikin jerin 'yan bayan tsakiya da kungiyar ke nazari a kansu. (Standard)
A wani labarin kuma, Leeds United na ci gaba da neman mai tsaron ragar Japan na Parma, Zion Suzuki, mai shekara 23, duk da cewa kungiyar ta Italiya ba ta son sayar da shi. (Tuttomercatoweb - in Italian)











