Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Afirka ta fara ɗaura ɗambar tsayawa da ƙafarta ne?
Daga sabuwar matatar tsaftace zinari da aka gina a Habasha zuwa wani katafaren aikin matatar mai da ake shirin aiwatarwa a Kenya wanda zai lakume biliyoyin daloli, ƙasashen Afirka da ke ƙaruwa suna ƙoƙarin samun ƙarin riba daga albarkatun ƙasashensu ta hanyar sarrafa su a cikin gida maimakon fitar da su a matsayin ɗanyen kaya.
Wannan sauyi na daga cikin wani gagarumin yunƙuri da ke gudana a faɗin nahiyar, wanda ke da nufin ƙarfafa masana'antun cikin gida, samar da ayyukan yi, da kuma rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje waɗanda aka sarrafa daga albarkatun Afirka.
A Habasha, ana sa ran wata matatar tsaftace zinari da ta ci sama da dala miliyan 50 za ta bai wa ƙasar damar tace zinari nata a cikin gida kafin ta fitar da kayayyakin da aka ƙara wa daraja zuwa kasuwannin duniya.
Har ila yau, gwamnatin ƙasar tana haɗin gwiwa da attajirin ɗan Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, wajen bunƙasa wata masana'antar samar da takin zamani, yayin da aka kuma fara aikin gina bututun man fetur da zai haɗa Habasha da Jibuti.
Ana sa ran aikin bututun man fetur, wanda kimarsa ta zarce dala miliyan 660, zai sauƙaƙa safarar man fetur daga tashar jiragen ruwa ta Jibuti zuwa cikin Habasha.
A gefe guda kuma, Kenya na ci gaba da shirye-shiryen gina wata katafariyar matatar mai, wadda ake sa ran za ta zama irinta ta farko a Gabashin Afirka, tare da kiyasin kuɗin da za a kashe a kanta zuwa kusan dala biliyan 16.
Gaba ɗaya, waɗannan ayyuka suna nuna wani sauyi mai ƙara ƙarfi da ke gudana a Afirka, inda gwamnatoci da masu zuba jari ke fara kallon abin da ya wuce hakar albarkatun ƙasa kawai, suna mai da hankali kan sarrafawa, masana'antu, da bunƙasa tattalin arzikin ƙasashensu.
"Dole ne Afirka ta gina makomarta da kanta."
Ba kasafai ake samun shugabannin kasuwanci da ake danganta su da wannan buri ba kamar Aliko Dangote.
"Ba za mu iya gina babbar Afirka ba idan muna dogaro da wasu," in ji Dangote.
"Wani daga wajen Afirka ba zai zo ya gina mana babbar Afirka ba. Mu Afrikawa ne kaɗai za mu iya yin hakan."
Dangote, wanda jarinsa ya bazu a fannoni irin su siminti, makamashi, taki da harkokin sufuri, a yanzu yana da hannu a wasu daga cikin manyan ayyukan masana'antu mafi girma da buri a nahiyar.
A Habasha, yana zuba jari a wata masana'antar takin zamani, sannan yana daga cikin masu ruwa da tsaki a aikin gina bututun mai da zai haɗa Jibuti da garin Dawaale da ke kan iyakar Habasha.
A Kenya kuma, yana goyon bayan wani aikin matatar mai da ake sa ran zai sauya fannin makamashi na yankin.
Dangote ya yi imanin cewa ya kamata ƙasashen Afirka su sarrafa albarkatunsu a cikin gida, maimakon fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafawa ba sannan su sake shigo da kayayyakin da aka kammala daga ƙasashen waje.
"Lokaci ya yi da Afirka za ta farka daga barci ta mai da hankali wajen bunƙasa tattalin arzikinta," in ji shi.
Ya kuma yi jayayya cewa shingayen kasuwanci na ci gaba da kasancewa daga cikin manyan abubuwan da ke hana tattalin arzikin nahiyar bunƙasa.
"Babban abin da ke hana tattalin arzikin Afirka ci gaba shi ne takunkumin da ake sanyawa zirga-zirgar mutane, kayayyaki da ayyuka tsakanin ƙasashen Afirka. Ina fata Yarjejeniyar Kasuwanci Cikin 'Yanci ta Nahiyar Afirka za ta taimaka wajen magance wannan matsala."
Masana sun ce ƙoƙarin ƙara wa albarkatu ƙima ta hanyar sarrafa su ba sabon abu ba ne.
Dokta Marit Kitaw, jami'a a sashen harkokin tattalin arziki na Hukumar Tattalin Arzikin Majalisar Ɗinkin Duniya ta Afirka kuma ƙwararriya a manufofin ma'adinai, ta danganta wannan sauyi da fara shirin Africa Mining Vision a shekarar 2009.
Manufar wannan shiri ita ce magance wata matsalar da ta daɗe tana akwai: duk da cewa ƙasashe da dama a Afirka suna da yalwar ma'adinai, fitar da albarkatun ƙasa kai tsaye yana samar da ƙaramin amfani ga tattalin arziki.
A cewar Dokta Marit, kuɗaɗen da ake samu daga ma'adinai ba su kasance suna haifar da bunƙasar masana'antu mai faɗi ba, kuma ba su inganta rayuwar jama'a sosai ba.
Mwendia Nyaga, mai ba da shawara kan harkokin makamashi, ya ce wani abin da ke ƙarfafa wannan sauyi shi ne matsin lambar karuwar yawan jama'a.
Yayin da miliyoyin matasan Afirka ke shiga kasuwar aiki a kowace shekara, gwamnatoci na fuskantar ƙarin matsin lamba wajen samar da ayyukan yi da faɗaɗa damar tattalin arziki.
"Tsawon shekaru, ƙasashe masu tasowa suna fitar da albarkatun ƙasa, sannan kuma suna shigo da kayayyakin da aka kera daga waɗannan albarkatun," in ji Nyaga.
"Tunanin maye gurbin kayayyakin da ake shigo da su daga waje da waɗanda ake samarwa a cikin gida bai samu karɓuwa sosai ba. Sauye-sauyen manufofin da muke gani yanzu na iya taimakawa wajen canza wannan al'ada."
Daga Fitar da Zinari Zuwa Tace Shi a Cikin Gida
Zinari ya zama ɗaya daga cikin fitattun misalan da ke nuna ƙoƙarin da Afirka ke yi na hawa matakan sarrafa kayayyaki masu ƙara daraja.
Daga Afirka ta Kudu da Ghana zuwa Uganda, Burkina Faso da Habasha, ƙasashe da dama suna zuba jari wajen gina matatun zinari a cikin gida maimakon aika ɗanyen zinari zuwa ƙasashen waje domin a sarrafa shi.
A halin yanzu, ƙasashen Afirka 14 ne ke da matatun tace zinari.
Matatar Rand Refinery ta Afirka ta Kudu ita ce mafi girma kuma mafi dadewa a nahiyar. Tun bayan kafa ta a shekarar 1920, ta tace kusan kashi ɗaya bisa uku na zinari da aka tace a duniya.
Habasha na daga cikin sabbin ƙasashen da suka shiga wannan sahu.
Ana sa ran Kamfanin Tace Karafa Masu Daraja na Ƙasa na Habasha, da ke yankin masana'antu na Bole Lemi a Addis Ababa, zai tace zinari domin kasuwannin cikin gida da na duniya.
Jami'ai sun ce idan matatar ta yi aiki da cikakken ƙarfinta, za ta iya tace har tan 600 na zinari a duk shekara.
Dokta Marit ta ce amfanin wannan ba ya tsaya ga kuɗaɗen shiga daga fitar da kaya kawai.
Ta ce: "Wannan na samar da ƙarin guraben ayyukan yi ga matasa da mata, yana taimakawa wajen bunƙasa ƙwarewar cikin gida, sannan kuma yana sauƙaƙa musayar fasaha da ilimin zamani."
Masana sun yi gargaɗin cewa tace ma'adanai kaɗai ba za ta sauya tattalin arzikin Afirka ba.
Sun ce nasara za ta dogara ne da gina cikakkun tsarin masana'antu da ke da alaƙa da albarkatun ƙasa.
Dokta Marit ta kawo ajiyar dutsen fosfet na Habasha a matsayin misali.
Ta yi nuni da cewa maimakon fitar da fosfet a matsayin ɗanyen kaya, Habasha za ta iya amfani da shi wajen samar da takin zamani a cikin gida, wanda zai samar da ƙarin ribar tattalin arziki tare da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Habasha ta fara shirye-shiryen gina wata masana'antar takin zamani a Jihar Somali, cikin haɗin gwiwa da Kamfanin Dangote Group.
Ga ƙasar da ta daɗe tana dogaro da takin zamani na waje, wannan aiki na nuna yadda za a iya haɗa albarkatun ƙasa da masana'antu domin ƙara ƙima ga kayayyaki.
Masanin tattalin arziki Marid Tulu ya ce tsaron abinci, samar da makamashi da bunƙasa masana'antu suna ƙara kasancewa da alaƙa da juna.
Ya yi nuni da cewa yayin da Afirka ke faɗaɗa samar da makamashi da hanyoyin more rayuwa na tattalin arziki, ƙasashen nahiyar za su samu damar sarrafa albarkatunsu a cikin gida tare da bunƙasa masana'antun da ke samar da kayayyaki masu daraja da ƙarin riba.
Me ya sa haɗin kan tattalin arzikin yanki yake da muhimmanci?
Me ya sa haɗin kan tattalin arzikin yanki yake da muhimmanci?
Masana da dama na ganin cewa yunƙurin bunƙasa masana'antu a Afirka zai yi nasara ne kawai idan ƙasashen nahiyar suka yi aiki tare maimakon kowacce ta yi ƙoƙarin gina irin wannan masana'anta ita kaɗai.
Dokta Marit ta ce kasuwannin yanki suna da muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Ta yi tambaya da cewa: "Idan Habasha tana da matatar tace zinari, me ya sa Tanzaniya za ta kashe kuɗi wajen gina wata irin ta daga tushe?"
A cewarta, maimakon haka Tanzaniya za ta iya aika zinarinta Habasha domin a tace shi a can. Ta ƙara da cewa ana buƙatar ƙarfafa haɗin kan kasuwanni, amfani da ababen more rayuwa tare, da kuma jawo masu zuba jari.
Tuni dai ana ganin misalan irin wannan haɗin gwiwar.
A Kudancin Afirka, hanyar Lobito Corridor tana haɗa Angola, Zambia da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta hanyar layukan dogo da tashoshin jiragen ruwa domin sauƙaƙa jigilar ma'adanai da sauran kayayyaki.
A Gabashin Afirka kuwa, Habasha, Kenya da Sudan ta Kudu suna aiki tare a kan shirin LAPSSET Corridor, ɗaya daga cikin manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a nahiyar.
Magoya bayan waɗannan ayyuka na cewa za su rage kuɗin sufuri, su sauƙaƙa isa ga kasuwanni, sannan su ƙarfafa haɗin kan tattalin arziki tsakanin ƙasashe.
Sai dai duk da wannan ci gaba, masana sun yi gargaɗin cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale ga manufar bunƙasa masana'antu a Afirka.
Rashin isassun ababen more rayuwa, wahalar samun jari, ƙarancin wutar lantarki da kuma shamakan kasuwanci na ci gaba da kawo cikas ga samar da kayayyaki da bunƙasar masana'antu a ƙasashe da dama.
Nyaga ya ce akwai wani tsohon tsarin tattalin arziki da ya daɗe yana aiki.
Ya ce: "An saba fitar da albarkatun ƙasa a matsayin ɗanyen kaya, sannan a sake shigo da kayayyakin da aka sarrafa daga waɗannan albarkatu daga ƙasashen waje a farashi mafi tsada."
A cewarsa, sauya wannan tsarin zai ɗauki lokaci.
Duk da haka, yawan al'ummar Afirka da ke ƙaruwa cikin sauri, musamman matasa, na iya zama babban ginshiƙi wajen bunƙasa masana'antu.
Nyaga ya ce: "Babbar damar da muke da ita ita ce mutanenmu. Muna da jama'a masu aiki, tattalin arzikin da ke haɓaka cikin sauri da kuma kasuwar masu saye da ke ƙara faɗaɗa. Wannan babbar dama ce ƙwarai."
Tsawon shekaru da dama, tattalin arzikin ƙasashen Afirka ya dogara ne kan fitar da albarkatun ƙasa da kuma shigo da kayayyakin da aka sarrafa daga waɗannan albarkatu.
A yau kuwa, gwamnatoci, masu zuba jari da masu tsara manufofi suna ƙara tambayar ko wannan tsarin har yanzu shi ne mafi alheri.
Ko waɗannan yunƙuri za su yi nasara ko a'a, hakan zai dogara ne kan samar da jari, inganta ababen more rayuwa, ƙarfafa haɗin gwiwar yankuna da kuma aiwatar da manufofi yadda ya kamata.