Yadda ƴan bindiga suka kashe Sheikh Yahaya Masussuka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da kisan sanannen malamin addinin Musulunci Sheikh Yahya Masussuka a gidansa da ke yankin Dutsen-Ma.

A wata tattaunawa da BBC, baturen ‘yansanda reshen Dutsen-Ma ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kashe mashahurin malamin da yammacin Litinin a kofar gidansa.

CSP Auwalu Gwadabe ya ce malamin ya rasu ne sanadiyyar raunuka na harbin bindiga bayan an kai shi asibiti.

Haka nan sakataren malamin, Dr Mustapha Haruna ya tabbatar da rasuwar Masussuka a babban asibitin Dutsen-Ma.

Shi kuwa daya daga cikin sanannun malaman da ke bin akida daya da Masussuka, wato Sheikh Usman Dangungu ya nuna kaduwarsa da kisan, inda yake cewa za su bar bincike ya bayyana wadanda suka aikata lamarin.

Kafin kisan nasa, Sheikh Masussuka na daga cikin malaman addinin Musulunci wadanda koyarwarsu ke haifar da cece-ku-ce a arewacin Najeriya da kasashe masu makwaftaka.

Malaman Musulunci da dama na sukar shi saboda akidarsa ta rashin yarda da hadisan Annabi Muhammad, inda yake danganta duk wata koyarwarsa ga Alqur’ani.

Lamarin ya kai ga cewa a cikin watan Nuwamban 2025 gwamnatin jihar Katsina ta yi sammacin malamin bisa zargin da aka yi masa na ‘cin zarafin malamai da kuma batanci ga hadisan Annabi Muhammad”.

Yadda aka kashe Sheikh Masussuka

Sanarwar da rundunar yansandan Najeriya a jihar Katsina ta fitar ta hannun mai magana da yawunta DSP Abubakar Aliyu ta ce an kashe Sheikh Masussuka ne da misalain karfe 7:30 na yamma a kofar gidansa da ke karamar hukumar Dutsen-Ma a jihar Katsina.

Sanarwar ta kara da cewa “wani harin ’yan bindiga ne ya yi ajalin malamin tare da wani abokinsa Adamu Abubakar”.

Sakataren Malamin ya ce Masussuka ya fita daga gida ne da nufin tafiya wurin da ya saba gudanar da karatunsa.

Sanarwar ‘yansanda ta ce jim kadan bayan faruwar lamarin ne aka garzaya da malamin da abokinsa zuwa wani asibiti da ke kusa, inda malaman asibitin suka tabbatar da rasuwar mutanen biyu.

Haka nan sanarwar ta kara da cewa kwamishinan ‘yansanda na jihar ya sanar da fara gudanar da bincike domin zakulo wadamda suka yi kisan.

Fahimtar Masussuka

Kamar yadda ba ya ɓoye fahimtarsa, Sheikh Masussuka mutum ne mabiyin fahimtar Ƙur'ani zalla, wani abu da ya sa yake yawan sukar hadisai da ya ce "suna taɓa ƙimar Annabi Muhammad SAW."

A baya ya yi suna da wata sara da yake kira da "Ritaya Dole", da ya ce ya ƙudiri aniyyar sanya wa koyarwar mabiya fahimtar "Salaf" ko kuma da ake kira Ahlussunnah, ko kuma ƴan ƙungiyar Izala, burki.

Wannan al'amari ne ake ganin ya ƙara rashin jituwar da ke tsakanin malamin da mabiya fahimtar Salaf ɗin inda suka yi ta musayar yawu a wa'azozinsu da soshiyal midiya.

Sheikh Masussuka na da gidan rediyo da talbijin da kuma makarantu a garin Dutsen-Ma na jihar Katsina, inda ya ce ya kafa su ne da manufar yaɗa koyarwar Alƙur'ani.