Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 28/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 28/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar

  1. Jirgin ruwan alfarma da ke rangadin duniya ya dakatar da tafiyarsa sakamakon tsadar fetur

    Wani jirgin ruwa na alfarma da ke rangadin duniya ya dakatar da tafiyarsa sakamakon tsadar man fetur, lamarin da ya bar ɗaruruwan fasinjoji a maƙale a ƙasar Cambodia.

    Kamfanin Amurka da ke gudanar da jirgin, Villa Vie Odyssey, ya kawo ƙarshen tafiyar shekaru biyu da aka shirya, tare da umartar fasinjoji su sauka a tashar jiragen ruwa ta birnin Sihanoukville na Cambodia.

    Wasu daga cikin fasinjojin sun biya sama da dala dubu 400 domin samun ɗakunan alfarma a wannan doguwar tafiya da yanzu aka soke.

    Lamarin ya haddasa takaici da ruɗani ga fasinjojin da suka yi tsammanin ci gaba da zagayen duniya na tsawon shekaru.

  2. TUC ta yi watsi da tayin alawus na naira 70,000, ta nemi ƙarin albashi

    Ƙungiyar Kwadago ta Ma’aikata Masu Fasaha ta Najeriya (TUC) ta yi watsi da tayin gwamnatin tarayya na alawus na N70,000, tana mai neman a yi wa ma’aikata ƙarin albashi nan take tare da aiwatar da yarjejeniyoyin da har yanzu ba a cika ba da aka kulla da ma’aikatan lafiya ƙarƙashin ƙungiyar JOHESU.

    Ƙungiyar ta ce alawus na wucin gadi ba zai iya magance matsin tattalin arziƙin da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta ba, tana mai jaddada cewa ya kamata gwamnati ta ƙara albashi maimakon ƙaddamar da matakan tallafi da ka iya kasancewa ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba.

    TUC ta kuma zargi gwamnatin tarayya da gaza cika alƙawurran da ta ɗauka na biyan wasu ma’aikata alawus ɗin da aka amince da shi a shekarar 2023, tare da yin watsi da yarjejeniyar da aka kulla watanni bakwai da suka gabata kan sake fasalin tsarin albashin ma’aikatan lafiya da ke ƙarƙashin JOHESU.

    Ƙungiyar ta bayyana matsayinta ne cikin wata sanarwa da Shugabanta, Festus Osifo, da Sakatare Janar, N. A. Toro, suka fitar a ranar Laraba bayan taron Majalisar Gudanarwa ta Ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar 8 ga Oktoban 2026.

    A cewar sanarwar, TUC ta rubuta wa gwamnatin tarayya ta hannun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, tana neman a gaggauta yin bitar albashin ma’aikata saboda hauhawar tsadar rayuwa.

    Ƙungiyar ta kuma yi hujjar cewa babu buƙatar gwamnati ta jira kammala tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa kafin ta ƙara albashin ma’aikata, tana mai cewa babu wata doka da ta kayyade iyakar albashin da ma’aikata za su iya samu daga masu ɗaukarsu aiki.

  3. Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin kafa ’yan sandan jiha

    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani kudiri da zai bai wa gwamnatin jihar damar kafa nata rundunar ’yan sanda ta jiha.

    Jagoran masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce matakin ya biyo bayan amincewa da gyare-gyaren da Majalisar Wakilai ta tarayya ta yi domin bai wa jihohin ƙasar damar kafa rundunonin ’yan sanda nasu.

    A wani ci gaba mai alaƙa da wannan, majalisar ta kuma amince da buƙatar Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rage kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026 domin ya dace da sauye-sauyen da aka samu a hasashen kuɗaɗen shiga na jihar.

    Tun da farko, jihar ta amince da kasafin kuɗi na tiriliyan N1.477 domin gudanar da ayyukanta a shekarar 2026.

    Sai dai majalisar ta ce raguwar kuɗaɗen da jihar ke samu daga rabon kuɗaɗen tarayya bayan sauye-sauyen dokokin haraji ne ya sa aka ga bukatar sake duba kasafin.

    Sabon kasafin da aka yi wa kwaskwarima ya ragu daga tiriliyan N1.477 zuwa tiriliyan N1.222, kuma majalisar ta amince da shi domin ya dace da halin da kuɗaɗen shiga na jihar ke ciki a halin yanzu.

  4. Zaɓen Isra'ila:Ƙawancen jam’iyyun da Firaminista Netanyahu ke jagoranta na kan gaba

    Yayin da aka ƙirga kusan kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen Isra’ila, ƙawancen jam’iyyun da Firaminista Benjamin Netanyahu ke jagoranta ta Likud na kan gaba da kujeru 54.

    Wannan ya nuna tazarar kujeru 5 tsakaninsa da ƙawancen da Gadi Eisenkot ke jagoranta.

    Sai dai har yanzu ƙawancen na Mista Netanyahu na bukatar ƙarin kujeru 5 domin samun rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.

    Firaminista Natenyahu ya ce su na buƙatar samar da kakkarfar gwamnatin da za ta kare muradunsu, kuma haramun ne su amince da gwamnatin da ya bayyana da '' masu nunawa Yahudawa kiyayya'' kamar dai jam'iyyun larabawa.

    Jam’iyyun Larabawan Isra’ila ne suka samu gagarumar ƙaruwa a wannan zaɓen, lamarin da ka iya sanya su taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati.

  5. Ƴan sanda sun tarwatsa dubban masu zanga zanga a Indonesiya

    'Yan sanda a Jakarta, babban birnin Indonesiya, sun harba hayaƙi mai sa hawaye tare da amfani da motar feshin ruwa, domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da yadda gwamnati ke tunkarar gobarar daji da ke ci gaba da ƙamari.

    Dubban ɗalibai da ƙungiyoyin fararen hula sun taru a Jakarta da sauran biranen ƙasar, suna buƙatar gwamnati ta ayyana gobarar a matsayin iftila'i.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ɗauki alluna masu ɗauke da taken: "Idan mun ƙone, ku ma za ku ƙone tare da mu."

    Indonesiya na fuskantar mafi munin gobarar daji da hayaƙin da ta haifar cikin fiye da shekaru goma, lamarin da ya ƙara yawan cututtukan numfashi tare da gurbata iska a ƙasashe maƙwabta kamar Malaysia da Singapore.

  6. Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin jiragen ƙasa a Sifaniya ya haura 60

    Aƙalla mutum 64 ne suka mutu, yayin da 80 suka jikkata bayan wasu jiragen ƙasa masu saurin gaske guda biyu sun yi taho mu gama a kudancin birnin Madrid, babban birnin Sifaniya, a cewar hukumomin yankin.

    Hatsarin ya shafi wani jirgin ƙasa da ya tashi daga Madrid zuwa Seville da kuma wani jirgin da rahotanni suka ce yana tsaye cak a lokacin da lamarin ya faru.

    Rahotanni sun ce taragai biyu sun kauce daga kan layin dogo, yayin da ake kula da waɗanda suka jikkata a filayen da ke kusa da wurin.

    A watan Janairu, wani hatsarin makamancin wannan da ya afku a kan wannan hanyar ya kashe mutum 46, lamarin da ya haifar da muhawara kan matakan tsaron hanyoyin jirgin ƙasa a Sifaniya.

    Firaministan ƙasar, Pedro Sanchez, ya bayyana alhini da kaɗuwa kan lamarin.

  7. A zamanin wane shugaban ne ƴan Najeriya suka fi fuskantar talauci?

    A makon da ya gabata ne wata mahawara ta kaure tsakanin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da abokan hamayya kan wane ne ya gadar da talauci ga ƴan Najeriya.

    Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalolin yunwa da talauci da ake gani yanzu sun samo asali ne daga matsalolin da gwamnatocin baya suka bari, yayin da gwamnatinsa ke ƙoƙarin gyara tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar sauye-sauye kamar cire tallafin mai da gyaran kasuwar canji.

    A gefe guda kuma, 'yan adawa da wasu tsoffin shugabanni sun zargi gwamnatin Tinubu da ƙara tsananta talauci. Misali, Olusegun Obasanjo ya soki sauye-sauyen tattalin arziƙin gwamnatin, yana mai cewa faɗuwar darajar naira da cire tallafin mai sun ƙara jefa mutane cikin talauci.

    Shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya alaƙanta manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, musamman cire tallafin mai da sauye-sauyen kasuwar canji, da waɗanda suka ƙara jefa ƴan Najeriya cikin talauci da wahala.

  8. Wane ne kan gaba tsakanin Netanyahu da Eisenkot a zaɓen Isra'ila?

    Hukumar zaɓen Isra’ila, ta ce an ƙirga fiye da kashi 70 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa ya zuwa yanzu, amma har yanzu babu wani ɓangare da ya samu rinjayen kujerun majalisar dokoki da ake buƙata.

    Haɗakar jam’iyyun Benjamin Netanyahu har yanzu ce ke da mafi yawan ƙuri’u, amma yawan kujerunta ya ragu zuwa 54.

    Yawan kujerun jam’iyyar babban abokin hamayyar Mista Netanyahu, Gadi Eisenkot, ya ƙaru zuwa 47, yayin da jam’iyyun da ke ƙarƙashin “Arab List” suka ƙara yawan kujerunsu zuwa 19.

    Haɗakar jam’iyyun da za ta kafa gwamnati na buƙatar aƙalla kujeru 61 a majalisar Knesset domin samun rinjaye.

    Tuni dai manyan ƴantakarar biyu suka fara yunƙurin neman goyon bayan ƙuri'un Larabawa domin samun damar kafa gwamnati.

  9. An saki tsohuwar matar mataimakin shugaban ƙasar Zimbabwe bayan zargin yunƙurin kashe shi

    Tsohuwar matar mataimakin shugaban ƙasar Zimbabwe ta shaƙi iskar ƴanci, bayan da aka tsare ta na tsawon shekaru bakwai a yayin da ta ke fuskantar shari’a kan zargin yunƙurin kashe shi.

    An gurfanar da Marry Mubaiwa a gaban kotu a shekarar 2019, bayan tsohon mijinta Janar Constantino Chiwenga ya zarge ta da ƙoƙarin kawo cikas ga nema masa magani yayin da yake jinya a ƙasar Afirka ta Kudu.

    Yayin da yake bayar da umarnin a sake ta, alkalin kotun ya ce Mubaiwa ta fuskanci matsaloli na ƙwaƙwalwa da na gangar jikinta da ma na tattalin arziki sakamakon tsawon lokacin da shari’ar ta ɗauka.

    Hukuncin ya zo ne bayan da masu gabatar da ƙara suka nemi a ɗage shari’ar na wata guda domin samun damar tuntuɓar shaidu.

    Lauyan Mubaiwa ya bayyana hukuncin a matsayin nasarar da ta zo a makare, yana mai cewa an tauye haƙƙoƙin wadda yake karewa sakamakon jinkirin da aka samu wajen gudanar da shari’ar.

    An zargi Mubaiwa da ƙoƙarin kashe Chiwenga ne lokacin da yake kwance a wani asibiti a birnin Pretoria na Afirka ta Kudu.

    Daga bisani mataimakin shugaban ƙasar ya tafi China inda ya shafe watanni huɗu yana jinya.

    Bayan kama ta, an tsare Mubaiwa kuma an hana bayar da belinta.

  10. An soma tattaunawa kan kafa sabuwar gwamnati a Serbia bayan nasarar ƙungiyar ɗalibai

    Ana ci gaba da tattaunawa a Serbia game da wanda zai jagoranci sabuwar gwamnati, bayan nasarar da jam'iyyar Student list ta samu a zaɓen 'yan majalisa na ranar Lahadin da ta gabata.

    Jam'iyyar, wadda ta samo asali daga wani gangamin zanga-zanga, za kuma ta yanke shawara kan yadda za a zaɓi ministoci.

    Ƙalilan ne daga cikin sabbin 'yan majalisar da aka zaɓa ke da gogewar siyasa a baya.

    Wakilin BBC ya ce Alexander Vucic, tsohon shugaban ƙasar da ya sha kaye a zaɓen, ya yi gargaɗin cewa zai iya kiran magoya bayansa su fito kan tituna, bayan da masu zanga-zanga suka kutsa kai cikin wata tashar talabijin da ke mara masa baya.

    Mataimakiyar shugaban jam'iyyar ta students list Katarina Stankovic, ta shaida wa BBC cewa sabuwar gwamnatin za ta bayar da fifiko ne kan magance cin hanci da rashawa, bayan shekara goma sha huɗu na mulkin Jam'iyyar Serbian Progressive Party ta tsohon shugaba Vucic.

  11. Mun samu masu neman zuba jari daga ƙasashe 120 na duniya - Dangote

    Matatar Mai ta Dangote ta ce ta samu masu neman zuba jari daga ƙasashe 120 na duniya, ciki har da dukkan ƙasashe 54 na Afirka, bayan rufe shirin sayar da hannayen jarinta a ranar Talata.

    Kamfanin ya ce hakan wani babban ci gaba ne ga kasuwannin hannun jari na Afirka, yana mai cewa tayin ya haɗa masu zuba jari daga dukkan nahiyoyi shida, tare da samar da damar mallakar wani babban kadarar masana’antu ga mutane da dama.

    A cikin wata sanarwa, Shugaba Kamfanin Dangote Industries Limited, Alhaji Aliko Dangote, ya ce yadda aka amsa tayin sayen hannun jarin ya nuna cewa ’yan Afirka na da niyyar zuba jari a masana’antun da aka gina a Nahiyar tare da cin gajiyar ci gaban masana'antun.

    Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, David Bird, ya ce yadda masu zuba jari daga ƙasashen duniya suka amsa tayin na nuna ƙwarin gwiwarsu da girman matatar, da ƙwarewarta wajen gudanar da ayyuka, da kuma burukanta na gaba.

  12. Mun kashe dala biliyan 47 zuwa yanzu a yaƙin Iran - Amurka

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda ya yi nazarin bayanan Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon), ya ce sojojin Amurka sun kashe fiye da dala biliyan 47 ya zuwa yanzu a yaƙin da Iran.

    Waɗannan bayanai sun nuna cewa kuɗin ya fi hasashen da Ma’aikatar Tsaron Amurka ta fitar a watan Yuli da kashi 25 cikin 100.

    A cewar Reuters, mafi girman kashe kuɗin ya haɗa da sama da dala biliyan 29 da aka ware domin maye gurbin harsasai da makaman da aka yi amfani da su, da kuma fiye da dala biliyan 6 da aka kashe kan kayan aikin soja.

    Waɗannan alƙaluma ba su haɗa da hasashen kuɗin gyaran sansanonin Amurka da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi na Iran suka lalata ba.

  13. Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma'aikata Naira 70,000 alawus din sufuri

    Gwamnatin Najeriya ta amince da riƙa biyan ma’aikata alawus na sufuri na Naira 70,000 duk wata na tsawon watanni shida, wanda zai fara daga watan Nuwamba 2026, domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziƙi.

    Hakan na ƙunshe ne a cikin matsayar da aka cimma a ƙarshen wani taron sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a ranar Talata a Abuja.

    Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyukan Yi ta ƙasar ta kira taron ne domin tattauna batutuwan da suka shafi walwala da jin daɗin ma’aikata, bayan NLC ta buƙaci a inganta yanayin aiki da kuma ba da tallafin rage matsin tattalin arziki.

    Tawagar gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Ministan Kwadago Dokta Muhammad Dingyadi, da Darakta Janar na Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu, da kuma shugaban ƙungiyar ƙwadago NLC, Mista Joe Ajaero, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

    Matsayar ta bayyana cewa tallafin zai shafi ma’aikata a dukkan matakai na gwamnati na tsawon watanni shida.

    Taron ya kuma amince cewa za a biya alawus-alawus na watanni 19 da ma’aikatan lafiya ke bi cikin watanni uku, wanda zai fara daga watan Disamba 2026.

    Dangane da batun mafi ƙarancin albashi na ƙasa, ɓangarorin biyu sun amince cewa za a kafa Kwamiti, wanda zai fara zamansa nan take.

    Ɓangarorin sun kuma amince cewa za su sake haɗuwa bayan wata guda domin tantance yadda ake aiwatar da abubuwan da aka cimma.

  14. Ɗan takarar shugaban ƙasa da ya sha kaye a zaɓen Brazil ya tsere zuwa Amurka

    Ɗan takarar shugaban ƙasa da ya sha kaye a zaɓen Brazil Flavio Bolsonaro, ya tsere zuwa ƙasar Amurka.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa a yanzu Mista Bolsonaro yana jihar Florida.

    A baya, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana cewa za ta bai wa Mista Bolsonaro da iyalansa biza.

    Kotun Koli ta hana shi fita daga ƙasar yayin da ake gudanar da bincike a kansa, bisa zargin halasta kuɗaɗen haram.

    Shugaba Lula da Silva, wanda ya doke Bolsonaro da sama da ƙuri'u miliyan huɗu a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana tserewar tasa a matsayin abin "kunya."

  15. Netanyahu na iya fuskantar barazana a zaɓen Isra'ila

    Sakamakon jin ra’ayin waɗanda suka kaɗa ƙuriunsu a zaɓen Isra'ila ya nuna cewa babu wanda ya samu nasara kai tsaye a muhimmin zaɓen majalisar dokokin ƙasar, inda duka Firaminista Benjamin Netanyahu da tsohon babban hafsan sojoji Gadi Eisenkot ba wanda ke kan hanyar samun rinjayen kujerun da za su ba su damar kafa gwamnati ba tare da wata haɗaka ba

    Wasu gidajen yaɗa labarai na Israila sun yi hasashen cewa jam’iyyar Yashar ta Gadi Eisenkot tare da wasu jam’iyyun adawa na Yahudawa guda uku da ke cikin ƙawancensa na"Change Bloc" za su samu kujeru 51 a majalisar dokokin Isra’ila, wato Knesset, mai kujeru 120,

    Haka kuma, jam’iyyar Likud ta Benjamin Netanyahu tare da abokan ƙawancenta na masu ra’ayin riƙau ra’ayi da kuma masu kishin adinin Yahuduwa suma za su samu kujeru 51.

    A yanzu samun wanda yayi nasara zai dogara ne kan muhimmiyar rawa da wasu jam’iyyun Larabawa biyu za su taka.

    Hukumar Zaɓen ƙasar ta bayyana cewa lokacin da aka rufe rumfunan zaɓe da daddare yawan waɗanda suka fito zaɓe ya kai kashi 77.7 cikin 100, wanda shi ne mafi girman adadin masu zaɓe a wannan lokaci tun shekarar 1999.

  16. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Laraba, wadda ake yi wa kirari da tabawa ranar samu.

    A yau ma za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa kamar a Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.