Shin ya kamata a sha magani da lemun kwalba?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da wasu ba su damu ba, ga wasu kuwa shan magani babban tashin hankali ne.

Daga jiƙawa da ruwa zuwa ɓallawa domin ya yi sauki haɗiyewa, akwai dabaru da dama da mutane daban-daban ke amfani da su domin sauƙaƙa wa kansu shan magani, musamman wanda ake ba su a asibiti

Wasu kuma sun gwammace su sha da kunu ko koko, ko kuma ma su saƙala shi a cikin loman tuwo.

To sai dai baya ga haka, wasu ƴan gayu na amfani da lemon kwalba mai zaƙi ko tsami-tsami wajen shan maganin saboda kada su ji ɗaci ko da ya taɓa musu baki.

To amma ko hakan ya dace?

A tattaunawarsa da BBC, Dr. Isma'il Abubakar, wani likita a Kano ya bayyana cewa lemun kwalba da sauran abubuwan sha masu sinadarai na iya yin tasiri ga yadda magani ke aiki. Haka kuma, shan magani a lokacin cin abinci ko bayan cin abinci na iya canza yadda jiki ke narkar da shi.

Ko me ya sa wasu suka gwammace su haɗiyi maganinsu da lemun kwalba ko wani abun sha baya ga ruwa?

Abun da ke sa wasu shan magani da wani abun sha ban da ruwa

Lititan ya ce akwai dalilai da dama da ke sa mutane su riƙa amfani da lemun kwalba ko wani abin sha banda ruwa ko abinci wajen shan magani da suka haɗa da

Ɗanɗano

Likitan ya ce yawancin kwayoyi ba su da daɗi, wasu ma suna da ɗaci sosai, wanda ke sa mutane su nemi wani abu mai zaƙi domin rufe ɗanɗanon.

Sauƙin haɗiye ƙwaya

Wasu mutane, musamman yara da tsofaffi, na samun wahalar hadiye magani da ruwa kaɗai. A irin wannan yanayi, abinci ko abin sha mai zaƙi ko mai kauri na iya zama kamar hanya mafi sauƙi a gare su in ji Dr. Ismai'il

Al'ada ko abin da aka saba gani a gida

"Idan mutum ya taso yana ganin ana haɗa magani da tuwo ko shayi ko lemun kwalba ko wani abun sha dai baya ga ruwa, yana iya ɗauka cewa hakan ne daidai hanyar amfani da shi.

Mene ne Illolin shan magani da lemun kwalba?

Dr Isma'ila ya ce shan magani da wani abin sha ban da ruwa yana daga cikin kuskuren da ake yawan yi a gida, wanda a wasu lokuta ke rage tasirin magani ko kuma ya haddasa matsala ga lafiya ba tare da an lura ba.

Ya kuma lissafo sauran illoli kamar haka

Rage tasirin magani

Wasu abubuwan sha kamar lemun kwalba, shayi ko gahawa suna ɗauke da sinadarai da ke iya dagula aikin magani a jikin mutum. Wannan na iya rage ƙarfin magani, ya hana shi yin aiki kamar yadda aka tsara.

Jinkirin aiki a jiki

"Lokacin da aka sha magani da wani abin mai sinadari, jiki na iya ɗaukar lokaci kafin ya narkar da shi. Wannan yana sa magani ya yi aiki a hankali fiye da yadda aka tsara shi."

Ƙara haɗarin illa a jiki

Likitan ya ce a wasu lokuta, shan magani da wani abun sha ban da ruwa na iya haifar da illa kamar ciwon ciki ko jiri ko tashin zuciya. Wasu abubuwan da magani zai haɗu da su na iya zama mai hatsari ga zuciya ko hanta.

Canza yadda jiki ke ɗaukar magani

Wasu abubuwan sha na iya canza yadda jiki ke ɗauka ko rarraba magani a jini. Wannan na iya sa magani ya yi ƙarfi fiye da kima ko kuma ya yi rauni fiye da yadda ake bukata in ji Dr Isma'il.

Rage kariya ga cuta

Likitan ya ƙara da cewa idan magani bai yi aiki yadda ya kamata ba saboda abin da aka sha maganin da shi, cutar da ake sha wa maganin na iya ci gaba ko ta ƙara tsanani, maimakon ta ragu.

Yadda ya kamata a sha magani

Likitan dai ya jaddada cewa ruwa mai tsfta shi ne mafi aminci wajen shan magani domin shi kaɗai ne ba ya shiga cikin sinadarai na magani saboda ruwa na taimaka wa ƙwaya ta narke cikin sauƙi, ta shiga jiki yadda aka tsara, ba tare da rage ƙarfinta ko canza aikinta ba.

Ga sauran shawarwarin da ya bayar kan yadda ya kamata a sha magani kamar haka;

A bi umarnin likita ko rubutun magani

Likitan ya ce kowane magani yana da tsarin amfani. Wasu ana shan su kafin abinci, wasu bayan abinci, wasu kuma a lokaci na musamman. Rashin bin wannan na iya rage tasirin magani.

A guji shan magani da lemun kwalba ko duk wani abun sha banda ruwa.

Waɗannan abubuwan sha na iya canza yadda magani ke aiki a jiki in ji likitan. Wasu sinadarai da ke cikinsu na iya rage ƙarfi ko jinkirta shigar magani cikin jini.

A guji haɗa magani cikin abinci kafin a haɗiye sai da shawara

Wasu magunguna suna buƙatar ciki ya kasance babu abinci domin su yi aiki da sauri. Wasu kuma suna buƙatar abinci domin kare ciki. Don haka dole a tambayi likita kafin haɗawa cikin abinci in ji shi.

A sha magani a daidai lokaci

Tsayawa kan lokaci yana taimaka wa magani ya ci gaba da aiki a jiki ba tare da tazara da zai rage ƙarfinsa ba.

Kada a ninka ƙwaya idan an manta

Idan aka manta shan magani, bai kamata a ninka kashi na gaba ba. Yin hakan na iya haifar da illa ga jiki.

A kammala shan magani kamar yadda aka rubuta

Ko da mutum ya ji sauƙi, dole ne ya kammala adadin da aka ba shi domin tabbatar da cewa cuta ta kau gaba ɗaya in ji likitan.

A cewar likitan, yawancin matsalolin da ake samu wajen shan magani suna faruwa ne saboda rashin bin waɗannan ka'idoji.

Ya ce "Bin waɗannan ka'idoji na taimaka wa magani ya yi aikinsa yadda ya kamata."