Za a daina ɗaukar fasinjojin jirgin ƙasa kyauta a Tehran daga gobe
Wani mai magana da yawun Majalisar Birnin Tehran na Iran ya ce daga gobe, ranar Laraba, za a daina ɗaukar fasinjojin jirgin ƙsa da na bas ɗin BRT kyauta, inda farashi zai koma yadda yake a tsarin da ake bi kafin rikici.
Alireza Nadali ya ce an amince da shirin “gyaran tsarin tikitin sufuri” a taron majalisar, sannan an tura shi zuwa kwamitoci na musamman domin ƙarin nazari.
Ya bayyana cewa shirin ya samu amincewar mambobin majalisa 13 bayan an gabatar da shi da sa hannun mambobi 10 a zaman da aka yi yau.
Ya ƙara da cewa har sai an kammala cikakken nazari kan wannan shiri, batun ci gaba da ɗaukar fasinjoji kyauta ba zai ƙara kasancewa a ajanda ba.