Me addinin Musulunci ya ce kan wajibcin layyar mata?

Hoton tarin raguna

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Muslmai a fadin duniya na shirin bikin Babbar Sallah, lokacin da masu hali ke yanka dabbobi domin yin layya, kamar yadda addini ya tanada, wadda koyi ne da Annabi Ibrahim.

Layya dai sunna ce mai karfi ga duk Musulmin da ke da hali, kuma ya kai lokacin da aka ware domin yin layyar a raye.

A mafi yawan lokuta a kasar Hausa, maza ne magidanta aka fi ganin suna hankoron yin layya, inda kowane magidanci ke kokarin ganin ya yanka abin da yake da karfin yankawa ta yadda zai wadatar da iyalansa da kuma raba wa makwafta da ‘yan’uwa.

Duk da dai akan samu mata da ke yin layyar jefi-jefi, amma ba kamar mazan ba.

Shin akwai bambanci ne tsakanin hukuncin layyar mace da namiji?

BBC ta tattauna da Malama Zahra'u Muhammad, kan hukuncin layya ga ƴa mace.

Me addinin Musulunci ya ce?

Malama Zahra'u ta ce layya ga mace sunnah ce mai ƙarfi kamar yadda take a kan namiji, kuma babu wani abin da ya yi mata shamaki idan tana da hali.

Ta ce idan mace na da hali ma za ta iya yi wa sauran makusantanta kamar yadda uba yake yi a gida, inda ta ƙara da cewa ko da miji zai yi layya, bai halatta macen da ke da hali ta ƙi yi ba.

"Layya ga mace sunnah ce mai ƙarfin gaske, kamar yadda take kan namiji, babu wani bambanci tsakanin mace da namiji," in ji Malama Zahra'u.

Malamar ta ce ko da mace ba ta da aure za ta iya yin layya idan tana da hali.

"Mace ko budurwa ce ya halasta ta yi wa kanta ko da ba ta da aure," in ji ta.

"Ko da maigida zai yanka, bai halasta mace tana da kuɗi ta ƙi yin layya ba, kowa so yake ya samu kusanci zuwa ga ubangiji".

Ko ya halasta mace ta yanka ragon layya da kanta?

A mafi yawan lokuta ko da mace ta samu damar yin layya, sai dai wani namiji ya yanka mata, wataƙila saboda tsoro da rashin ƙwarin gwiwa.

Malamar ta ce babu laifi don mace ta yanka ragon layyarta da kanta, idan har ta san yadda za ta yi ba tare da tsoro ba, kuma hakan ya fi dacewa.

"Allah bai ƙayyade sai namiji ba kawai - a wajen ibada."

Ta ce yawancin malamai sun amince cewa mace za ta iya yanka da kanta.

Yadda ya kamata a yi da naman layya

Malama Zahra'u ta ce yana da kyau ga duk wanda ya yi layya ya raba sadaka ga ƴan'uwa da masu ƙaramin ƙarfi.

Ta ce ya kamata a kasa nama gida uku domin a raba ga mabuƙata da wanda za a ci da kuma wanda za ba ƴan'uwa.

Sai dai malamar ta ce ba dole ne sai mutum ya ba da sadakar naman ba idan bai da niyya, amma akwai lada a cikin yin hakan.