Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 8 da suka sa Arsenal ta lashe kofin Premier
Jiran da Arsenal ta daɗe tana yi ya zo karshe.
Bayan jiran shekara 22 da Gunners ta yi daga karshe ƙungiyar ta sake lashe kofin Premier League.
Yanzu ta kawar da baƙin cikin karewa a mataki na biyu sau uku a jere a jere, sannan ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta daƙile yunkurin Pep Guradiola na fatan lashe kofin bana, bayan da ya ɗauki Carabao da kuma FA Cup a kakar nan.
BBC Sport ta duba manyan lokuta da suka taimaka wajen sauya wasannin Arsenal daga ƙungiyar da ke kusa ɗaukar kofin zuwa wadda yanzu ita ce da babban kofin tamaula na Ingila na kakar nan.
Arsenal ta yi cefane tun kafin fara kakar 2025/26
Bayan ganin yadda aka yaba wa kokarin Liverpool F.C. yayin da ta ɗauki Premier League a kakar da ta gabata, inda ta tabbatar da lashe kofin yayin da ya rage saura wasa huɗu a kammala gasar, daga lokacin Arsenal ta kuduri aniyar kara karfin ƙungiyar kafin fara kakar bana.
Hakan ne ya sa ta sayo sabbin ƴan wasa takwas zuwa Emirates, yayin da ɗan wasanta, Thomas Partey wanda kwantiraginsa ya kare ya bar Arsenal.
Ɗan wasan tawagar Sweden, Viktor Gyökeres shi ne babban ciniki da ƙungiyar ta yi daga Sporting ta Portugal kan kuɗi fam miliyan 64, wanda ya sa Arsenal ta samu gogaggen lamba tara da ta daɗe tana nema.
A lokaci guda kuma Martín Zubimendi ya koma Emirates daga Real Sociedad, yayin da aka kara karfin baya ta hanyar ɗaukar aron Piero Hincapié daga Bayer Leverkusen. Haka kuma Noni Madueke daga Chelsea da Eberechi Eze daga Crystal Palace sun koma Arsenal kafin fara kakar 2025/26.
Kashe sama da fam miliyan 250 ba tare da samun wani gagarumin kuɗin shiga daga sayar da ƴan wasa ba abu ne mai girma, amma yayin da kakar ta ci gaba, muhimmancin waɗannan sababbin ƴan wasan ya bayyana da tasiri karara.
Yanzu da aka tabbatar da lashe kofin Premier League, kuma ana jiran wasan karshe a UEFA Champions League da Paris St Germain, kashe kuɗin na nuna alamar an yi amfani da su yadda ya kamata.
Martinelli ya farke ƙwallon da ya kawo tsaiko a City
Wannan ya faru ne a wasa na biyar da fara kakar bana, amma ƙwallon da Gabriel Martinelli ya ci a minti na 93 da ta bai wa Arsenal damar tashi kunnen doki da Manchester City a watan Satumba ta zama mai matukar muhimmanci.
A lokacin, an ɗauki sakamakon a matsayin ƙwazo ma sauki ga Arsenal, bayan da ta hana Pep Guardiola samun wata muhimmiyar nasara, tare da rage tazarar maki tsakaninsu da Liverpool, wadda ke jagorancin gasar da tazarar maki biyar.
Bayan da Erling Haaland ya bai wa City ƙwallo tun da wuri, abin lura shi ne yadda Manchester City ta koma tsare baya a wasan, musamman a zagaye na biyu. Guardiola har ma ya koma tsarin masu tsaron baya biyar, saboda ya ga alamar Arsenal za ta iya rama ƙwallon da aka fara zura mata a raga.
Da ace City ta iya jurewa a wasu karin mintuna a karawar da ta tsira da maki ukun, kuma da Guardiola ya sha yabo kan yadda ya yi wasan tsare baya da salon da ya tunkari Arsenal a shirin lashe kofin Premier League na bana.
Sai dai maimakon haka, sai aka yi ta yaba wa Arsenal kan hare-haren da ta yi ta kai wa manchester City da damarmakin da ta yi ta ɓararwa daga baya ƴan wasan da suka shiga fafatawar daga Eberechi Eze da Martinelli suka yi bani in baka da ta kai Martinelli ya farke ƙwallon daf a tashi a cikin karin lokaci.
Gabriel ya ci ƙwallo daf a tashi a Newcastle
Mako ɗaya tsakani, Arsenal ta sake yin wata murna cin ƙwallo cikin ƙarin lokaci.
Duk lokacin da Gunners ta kai ziyara St James' Park, ba ta yi wa ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama dadi a shekarun baya, inda ta sha kashi sau uku ba tare da zura ƙwallo ko ɗaya ba a raga a wasa ukun da suka gabata.
Saboda haka lokacin da Nick Woltemade ya ci wa Newcastle United kwallo a farkon wani wasa mai zafi, wanda kuma aka soke bugun fenaritin Arsenal da ta samu, bayan duba VAR, mai yiwuwa magoya bayan Arsenal sun fara tunanin rasa maki uku.
Sai dai Mikel Merino ya farke wa Arsenal ƙwallon a minti na 84, sannan kuma Gabriel Magalhães ya kara ta biyu da kai daga bugun ƙusurwa a minti na 96, abin da ya sa magoya bayan Gunners da ƴan wasa da jami'an ƙungiyar suka ɓarke da ihu da kuwwa da kuma murna.
Sai kawai Liverpool ta yi tuntuɓe a hannun Crystal Palace washegarin ranar, ba zato ba tsammani Arsenal ta rage tazarar maki zuwa biyu kacal tsakaninta da saman teburin gasar.
Eze ya ci Tottenham ƙwallo uku rigis da Arsenal ta bayar da tazarar maki shida
Bayan watanni biyu, kuma bayan jerin nasara 10 a jere a dukkan fafatawa — ciki har da wasa takwas ba tare da an zura mata ƙwallo ba — Arsenal ta hau saman teburin Premier League cikin kwarin gwiwa.
Sai dai 2-2 da ta yi da Sunderland ya kawo karshen wannan jerin karawa ba tare da an zura mata ƙwallo ba, amma Gunners ta shiga wasan hamayya na arewacin London a watan Nuwamba tana da damar kara buɗe tazarar maki shida bayan Manchester City ta sha kashi 2-1 a hannun Newcastle United a Tyneside.
Duk wani tunani da Tottenham ke yi na dakile burin abokiyar hamayyarta na lashe gasar ya gushe da wuri, yayin da Arsenal ta ci ƙwallo biyu tun kafin a je hutu, daga baya ta kara ta uku a zagaye na biyu a wasan.
Richarlison ya ci wa Tottenham ƙwallo daya, amma Gunners ce ta samu maki uku a karawar, inda Eberechi Eze — wanda ƙiris ya rage ya koma ƙungiyar da Thomas Frank ya horar kafin fara kakar bana, daga baya ya rattaba hannu da Arsenal.
Eze ɗin ya kammala cin ƙwallo uku rigis a wasan na hamayya - abin da ya bai wa Arsenal mafi girman tazarar maki bayan wasa 12 a kokarin lashe Premier League na kakar nan.
Rashin nasara a hannun Man United ya tabbatar da cikas ga Man City a farkon 2026
Yayin da Patrick Dorgu ya yi murnar cin ƙwallonsa da ya buga ta wuce Gianluigi Donnarumma daga nan wasan hamayya na Manchester ya zo karshe.
Manchester United ta ci ƙwallaye biyu a Old Trafford, yayin da Manchester City ke fuskantar wani sabon koma baya, sakamakon mummunan kalubale da fara sabuwar shekarar.
Bayan da ta yi kokarin dawo da kanta cikin fafatawar neman kofin gasar a lokacin Kirsimeti, ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta kasa samun nasara a wasanninta huɗu a farko lik a shekarar 2026.
Canjaras da Sunderland ya biyo bayan rasa maki a gida a hannun Chelsea da Brighton & Hove Albion, lamarin da ya bai wa Arsenal damar buɗe tazarar maki bakwai a saman teburin gasar — duk da cewa ita ma ta yi wasu ƴan kuskure a nata bangaren.
Gabriel ya tsira da ba a bashi jan kati ba, saboda gware da ka da ya yi wa Haaland
Zuwa watan Afrilu, tazarar maki ta kai shida, amma kasancewar Manchester City na da wasa ɗaya kwantai, yayin da Arsenal ta je Etihad domin fafatawar saman teburin gasar, dukkan bangarorin biyu za su iya cewa kofin yana hannunsu.
Manchester City ce ta yi nasara daga karawar mai cike da armashi, inda Erling Haaland ya ci ƙwallon a minti na 20 a zagaye na biyu.
Sai dai watakila mafi muhimmancin lokaci ya zo ne a karshen wasan, yayin da rikicin da ya daɗe yana gudana tsakanin Haaland da Gabriel Magalhães ya kai kololuwa.
Dukkaninsu sun tsaya suna kallon juna ido-da-ido kafin mai tsaron bayan Arsenal din ya tura kansa gaba kaɗan. Kasancewar Haaland bai faɗi kasa ba mai yiwuwa ne ya ceci Gabriel daga jan kati.
Ko da yake abin yabawa ne yadda Haaland ya ɗauki lamarin, hakan ya yi wa Arsenal wata babbar alfarma, domin da an kori Gabriel saboda rashin da'a da ƙungiyar Mikel Arteta ta rasa ɗaya daga cikin fitattun masu tsaron bayanta a wasanni uku masu zuwa.
Kuskuren Guehi ya sa City ta ɓarar da maki biyu a Everton
Nasara da Manchester City ta samu a hannun Burnley ta sa ta hau saman teburin Premier League bisa yawan ƙwallaye.
Zuwa lokacin da suka buga wasan su na gaba a gasar Premier League a filin Hill Dickinson Stadium da Everton, Arsenal ta riga ta buga wasa biyu kuma ta yi gaba da maki shida.
Ko da yake idan da City ta yi nasara a wasanninta biyu da za ta iya haɗa maki iri ɗaya da na Arsenal, wadda ke kan gaba a jan ragamar teburin.
Duk da haka, babu wata alamar matsin lamba a kan City a wasan, inda Jeremy Doku ya zura ƙwallo kafin hutun rabin lokaci, wanda ya sa da yawa suka yi tunanin za su tafi da maki uku a gidan Everton.
Sai dai komai ya canza a minti na 68 lokacin da Marc Guéhi ya yi kuskure da Thierno Barry ya farke wa Everton ƙwallon.
Daga nan wasan ya juya gaba ɗaya, inda ƙungiyar David Moyes ta zura kwallaye uku cikin mintuna 13.
Ko da yake City ta dawo ta farke a lokacin karin lokaci da suka tashi 3-3, asarar maki biyu ta sa Arsenal ta sake samun fa'ida a fatan lashe kofin Premier League.
Hana ƙwallo ya shiga raga da Raya ya yi da takaddamar VAR
A bisa ƙa'ida, tafiya zuwa gidan West Ham United da ke faatan tsira daga faɗuwa zuwa Championship ya kasance ɗaya daga wasa cikin mafi wahala a karawa uku na ƙarshe da Arsenal ta fuskanta.
Wasan ne da Mikel Arteta ke bukatar mako uku, domin kada Manchester City ta dawo cikin fafatawar neman kofin gasar, amma Arsenal ta sha wahala wajen doke West Ham a wasan hamayya na ƴan birnin Landan.
Karawar babu ci har zuwa lokacin da ɗan wasan West Ham, Matheus Fernandes, ya yi bani in baka da Pablo Fornals, sai ya tsinci kansa a yadi shida daga shi sai David Raya kawai a gabansa.
Fernandes ya yi ƙoƙarin zura ƙwallo ta gefen kusurwa, amma Raya ya hana ƙwallon ya shiga raga, hakan wasan ya ci gaba babu ci har saura minti 10 a tashi.
Daga nan ne Gunners ta ci ƙwallo ta hannun Leandro Trossard a minti na 83.
Amma wasan bai ƙare ba daga lokaci, inda West Ham ta ci gaba da matsa lamba a ƙoƙarin neman farkewa. Gabriel Magalhães ya yi kokarin hana Callum Wilson ƙwallo, amma ɗan wasan West Ham ya sake samun dama daga bugun kusurwa, inda ya zura ƙwallo mai ƙarfi ta cikin taron ƴan wasa a lokacin karin lokaci.
Sai dai farin cikinsu bai daɗe ba. Mai duba bidiyo (VAR) ya shiga lamarin, kuma bayan dogon nazari an soke ƙwallon saboda laifin da aka yi wa David Raya, inda Pablo Fornals ya rike shi a lokacin bugun kusurwa.
Haka kuma an duba wasu yiwuwar laifuka da suka haɗa da ƙorafin fanareti kan ketar da Leandro Trossard da Declan Rice suka yi, amma aka watsar da batun.