An kashe ɗansanda da ke dab da ritaya a faɗan daba a Kano
Wani jami’in ‘yan sanda da ke aiki a sashen Hotoro, wanda aka bayyana sunansa a matsyain Sani S.O ya mutu yayin wani faɗan ƙungiyoyin ‘yan daba a jihar Kano, watanni kaɗan kafin ya yi ritaya daga aiki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun ce an tura jami’in tare da abokan aikinsa domin tarwatsa faɗan da ya ɓarke tsakanin ƴan daban, sai dai an ce wani daga cikinsu ya harbe shi da bindiga.
Rahoton ya ce an garzaya da shi asibiti bayan harbin, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
An bayyana marigayin a matsayin jami’i mai nagarta da ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a rundunar ‘yan sanda, kuma yana dab da ritaya cikin makonni kaɗan.
A halin yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙaruwar rikice-rikicen ‘yan daba a sassa daban-daban na birnin Kano, ciki har da Hotoro da Fagge da Koki.