KAI TSAYE, Yaƙin Iran, Amurka da Isra'ila da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya ta ranar Talata 20/5/2026.

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya ta ranar Laraba 20 ga watan Mayun 2026.

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Usman Minjibir da Nabeela Mukhtar Uba

  1. An kashe ɗansanda da ke dab da ritaya a faɗan daba a Kano

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami’in ‘yan sanda da ke aiki a sashen Hotoro, wanda aka bayyana sunansa a matsyain Sani S.O ya mutu yayin wani faɗan ƙungiyoyin ‘yan daba a jihar Kano, watanni kaɗan kafin ya yi ritaya daga aiki kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Rahotanni sun ce an tura jami’in tare da abokan aikinsa domin tarwatsa faɗan da ya ɓarke tsakanin ƴan daban, sai dai an ce wani daga cikinsu ya harbe shi da bindiga.

    Rahoton ya ce an garzaya da shi asibiti bayan harbin, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

    An bayyana marigayin a matsayin jami’i mai nagarta da ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a rundunar ‘yan sanda, kuma yana dab da ritaya cikin makonni kaɗan.

    A halin yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙaruwar rikice-rikicen ‘yan daba a sassa daban-daban na birnin Kano, ciki har da Hotoro da Fagge da Koki.

  2. Yaƙin Iran ya janyo rububin motoci na lantarki a duniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da makamashi ta duniya ta ce yaƙin Iran ya janyo ƙaruwar sayen motoci masu amfani da lantarki a duniya da kusan kashi 28 cikin 100.

    Hukumar ta danganta wannan ƙaruwa da hauhawar farashin mai da ta biyo bayan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila.

    Rahoton ya ce tsadar mai ta sa mutane da dama sun koma amfani da motocin lantarki domin rage kashe kuɗin sufuri.

    A cewar hukumar, kusan ƙasashe 30 sun samu ƙarin masu sayen motocin da ke amfani da lantarki a watan Maris, ciki har da ƙasashen Latin Amurka inda aka samu ƙaruwa da kashi 75 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

    Rahoton ya kuma nuna cewa sauƙin farashin motoci na lantarki ya ƙara taimakawa wajen yawaitar sayensu a kasuwanni daban-daban.

    Sai dai rahoton ya nuna bambanci a Amurka, inda aka samu raguwar sayen motoci na lantarki a ƙarshen shekarar da ta gabata, duk da ci gaban da aka samu a wasu yankuna na duniya..

  3. Idan aka sake kai mana hari, yaƙi zai bazu fiye da yankin Gabas ta Tsakiya - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran ta fitar da wata sanarwa da ke gargaɗin cewa idan Amurka da Isra’ila suka sake kai hari kan Iran, rikicin zai iya bazuwa fiye da yankin Gabas ta Tsakiya.

    A cikin sanarwar, rundunar ta mayar da martani ga barazanar sake kai hari da shugaban Amurka, Donald Trump, da wasu jami’an Isra’ila suka yi inda ta ce sake kai hari kan Iran zai haifar da faɗaɗa yaki zuwa sassa da dama na duniya.

    Ta ƙara da cewa duk wani farmaki zai fuskanci martani mai tsanani.

    A wani ɓangare kuma, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana a shafinsa na X cewa Iran ta koyi darussa da yawa kuma ta ƙara ƙwarewa, yana mai cewa idan aka koma kai musu hari, to Amurka za ta ga abin mamaki.

    A gefe guda, shugaba Donald Trump ya ce a baya cewa ya dakatar da wani harin soji kan Iran a daidai lokacin da ake shirin aiwatar da shi, bayan roƙon wasu shugabannin yankin, lamarin da ke ƙara nuna yadda rikicin diflomasiyya da tsaro ke ci gaba da ɗaukar hankali a tsakanin ƙasashen biyu.

  4. Tsohon ministan sufuri Alƙali ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a APC

    ...

    Asalin hoton, Sa'idu Ahmed Alkali/Facebook

    Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC, Sa'idu Ahmed Alkali, ya sanar da janye kansa daga shiga zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar za ta gudanar ranar 21 ga watan Mayun 2026.

    A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Umar Alkali Jibrin ya fitar, Sanata Alƙali ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira rashin gaskiya da karya dokokin zaɓe a jihar.

    Sanarwar ta bayyana cewa Alƙali ya cika dukkan sharuɗɗan shiga takarar gwamna, ciki har da sayen fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara tare da wuce tantancewar da jam’iyyar ta gudanar. Sai dai ya ce yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwani na majalisar wakilai da sanatoci a yankunan Gombe/Kwami/Funakaye, Billiri/Balanga da Gombe ta Tsakiya a ranakun 16 da 18 ga watan Mayu ya sa ya rasa ƙwarin gwiwa kan sahihancin tsarin zaɓen.

    A cewarsa, "zaɓukan sun gudana cikin maguɗi, rashin gaskiya da kuma karya sashe na 86 na dokar zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi cewa dole ne a gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyya."

    Ya ce an gudanar da zaɓukan ba tare da isassun kayan aiki da jami’an zaɓe da masu sa ido da sauran shirye-shiryen da suka dace ba, lamarin da ya nuna cewa babu adalci ko gaskiya a tsarin.

    Duk da janyewar tasa daga takarar, Sanata Alƙali ya tabbatar da ci gaba da biyayya da goyon bayansa ga jam’iyyar APC domin samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.

  5. Amurka za ta sha mamaki idan ta koma yaƙi da mu - Iran

    ...

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya mayar da martani ga kalaman barazanar shugaban Amurka, Donald Trump, dangane da yiwuwar sake kai hari kan Iran, inda ya ce: “Amurka za ta sha mamaki idan ta koma fagen yaƙi da mu.”

    Araghchi ya yi wannan gargaɗi ne a wani sabon saƙo da ya wallafa a shafin X inda ya ce

    “Watanni bayan fara yaƙin da aka yi da Iran, Majalisar Dokokin Amurka ta amince da lalata jirage masu yawa da darajarsu ta kai biliyoyin daloli. Yanzu kuma an tabbatar a hukumance cewa rundunar sojinmu mai ƙarfi ita ce ta farko a duniya da ta harbo shahararren jirgin yaƙin F-35 ta Amurka.”

    A ƙarshen saƙon nasa, ya yi iƙirarin cewa:

    “Da darussan da muka koya da kuma ilimin da muka samu, ku tabbatar cewa komawa fagen yaƙi zai kawo ƙarin abubuwan mamaki.”

    A jiya ne shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa a daidai lokacin da ake shirin kai wani babban harin soji kan Iran, ya bayar da umarnin dakatar da harin bayan roƙon shugabannin yankin.

  6. Jiragen man China sun ratsa ta mashigar Hormuz bayan jinkirin fiye da wata biyu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu manyan jiragen dakon mai guda biyu na ƙasar China da ke ɗauke da ganga miliyan huɗu na ɗanyen mai sun ratsa ta mashigar Hormuz a ranar Laraba.

    Bayanan jigilar ruwa daga kamfanonin Kepler da LSGA sun nuna cewa manyan tankokin man guda biyun da ke ɗauke da ɗanyen man Gabas ta Tsakiya sun bar mashigar Hormuz bayan sun shafe sama da wata biyu suna jira a yankin Tekun Fasha.

    A cikin kwanakin baya-bayan nan, jiragen ruwa kaɗan ne kawai suka rika bi ta wannan muhimmiyar hanyar ruwa.

    Sai dai nasarar da jiragen suka samu wajen wucewa, tare da sauyin salon magana daga Fadar White House, ya sa farashin mai ya ɗan sauka kaɗan.

    A ranar Talata, shugaban Amurka, Donald Trump, ya jaddada cewa ana dab da cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran, duk da cewa ya ce duk wata yarjejeniya da za a cimma dole ne ta hana Iran mallakar makamin nukiliya.

  7. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.