Abin da ya sa Barcelona ta mamaye La Liga

Barca

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 7

A gasar La Liga a Sifaniya an saba ganin ƙalubale da matsi da sauye-saye har da gazawar wasu ƙungiyoyin. Amma wannan shekarar ba haka ta kasance ba.

Maimakon haka, nasarar da Barcelona ta yi da ci 2-0 a kan Real Madrid ta sa ta lashe gasar La Liga ta bana cikin yanayi mai kyau, kuma a gida a gaban babbar abokiyar hamayya, kuma da tazarar maki 14.

Wasan El Clásico a ranar Lahadi ya zama na farko cikin kusan shekara 100 da aka ɗauki kofin tsakanin manyan ƙungiyoyin Sifaniya a tarihi.

Wannan kuma shi ne kofi na La Liga da kocin Barcelona Hansi Flick ya lashe a cikin kakar wasansa biyu da yake jagoranci.

BBC Sport ta yi nazari kan yadda Barcelona ta sake lashe La Liga a wannan kakar.

Barcelona ta ci gaba da lashe dukkan wasanninta na gida

Marcus Rashford celebrates a goal for Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashford ya taka rawar gani

Ƙungiyar da Flick ke jan ragama tana kan ganiya tun daga watan Fabrairu, wadda ta lashe wasa 11 a jere ba tare da rashin nasara ba.

Wasa huɗu aka doke ta a La Liga a kakar nan, sannan ta lashe dukkan karawar da ta yi a gida a bana.

Ƙungiyar ta yi takaici da aka fitar da ita a copa del Rey a zagayen daf da ƙarshe da kuma a Champions League a kwata fainal, amma duk da haka ta ɗauki La Liga.

Barcelona ta yi nasara 42 daga cikin karawa 53 a wannan kakar, wanda ya kai nasarar kashi 79% — kuma kawai Bayern Munich ce ke gaban ƙungiyar Sifaniya da mafi kaso (83%) a cikin manyan gasar ƙasashen Turai biyar.

Dangane da yawan ƙwallaye, Bayern Munich ita ce kawai ƙungiyar da ta fi Barcelona zura ƙwallaye a raga a dukkan fafatawa da kuma a Bundesliga.

Lokacin da Hansi Flick ya koma Barcelona a watan Mayu 2024, Real Madrid ta riga ta lashe Champions League da La Liga, sannan ta ƙara da ɗaukar Kylian Mbappé zuwa cikin ƴan wasanta mai cike da taurari.

Amma cikin shekara biyun, Sai Barcelona ta lashe kofuna biyar daga cikin shida a gasar cikin gida ƙarƙashin kocin ɗan Jamus, yayin da Real Madrid ta shiga kakar wasa ta biyu a jere ba tare da samun kofi ba.

Tasirin Flick kan ƴan wasan Barcelona

Barcelona lift the trophy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barcelona have won back-to-back La Liga titles
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babban dalilin da ya sa Barcelona ke ƙara samun ci gaba shi ne tasirin Flick ga kowane ɗan wasa da kuma yadda yake amfani da su cikin tsarin wasansa.

Kocin ɗan asalin Jamus ya sake fasalin Barcelona tun daga lokacin da ya karɓi ƙungiyar, inda ya kawo tsari da ladabi, sannan ya dawo da salon kai hari kai tsaye.

Wannan ya faru ne a daidai lokacin da sabon ƙarni daga La Masia ta fara fitowa fili, inda Lamine Yamal ke jagoranta.

Flick ya hanzarta shigar da Lamine Yamal cikin masu fara buga wa ƙungiya tamaula, ya ba shi cikakken ikon murza leda da ƙirƙirar dabaru da ke ƙara bayyana ƙwarewarsa.

Masu tsaron baya biyu ne a tare ke tare shi, amma hakan baya hana shi yanke su ga sa hanzari da kai damar maki da kuma cin ƙwallaye, kai ka ce lokacin Lionel Messi ne.

Salon da matashin ke yi a tamaula ya mayar da gefen dama a Barcelona zuwa mafi hatsarin ɓangare a Spain.

Duk da raunin da ya samu kwanan nan, ɗan wasan mai shekara 18 ya ci ƙwallo 24 a wasa 45 a wannan kakar.

Tare da Lamine Yamal, Flick ya kuma dogara da wasu ƴan ƙwallon da ya ɗauko daga makarantar ƙungiyar kamar su Pau Cubarsí da Fermín López.

An yi amanna da Rashford a Barcelona

Marcus Rashford celebrates

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford has contributed to three goals (two goals, one assist) in his last three La Liga games

A ƙarƙashin jagorancin Flick, Raphinha, duk da cewa yana shan fama da jinya a bana, amma ya ƙara zama ɗan wasan da ya yi fice a ƙungiyar ta Sifaniya da wasannin Turai.

Haka kuma Pedri ya ci gaba da kasancewa ginshiƙi a tsakiyar fili, yana bunƙasa tsarin wasan da aka gina cikin salon taka leda mai ban sha'awa da kai hare-hare da sauri.

A gefe guda, Robert Lewandowski ya sake dawo da ƙwarewarsa a tsarin Flick. Tare da inganta taimakawa wajen hare-hare.

Mai shekara 37 daga Poland ya sake zama mai haɗari da sa ƙwazo a wasanninta. Har yanzu ba a tabbatar da makomarsa ba, yayin da kwantiraginsa zai ƙare a watan Yuni.

Eric García ya fito a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasa mafi amfani da dabara a kakar nan, yana iya motsawa da sauri da kai ƙwallon duk inda ya yi niya, yayin da Gerard Martín ya zarce hasashe da aka yi a kansa, bayan da aka ba shi muhimmiyar rawar da zai taka.

Ko da a lokutan da Barcelona ta ci karo da koma baya, Barcelona ta ci gaba da mayar da martani da bin wasanninta daki-daki. Bayan rashin nasara a hannun Girona da Real Madrid a watan Oktoba, ta koma kan ganiya sakamakon lashe wasanni da yawa a jere a La Liga.

Flick ya kuma yarda da juya ƴan wasa a wurin da ya dace da kuma salon matasalar da ya fuskanta, kuma duk wanda aka sauya masa mataki sai kaga yana yin abinda ya dace. Marcus Rashford yana ɗaya daga cikin waɗannan 'yan wasa.

Duk da cewa ba koyaushe yake cikin 'yan wasan da ake fara wasa da shi ba, Flick ya kan yi amfani da shi daga benci a muhimman lokuta, kuma ƙididdiga ta nuna yana cikin mafi kyawun ƴan gaba a manyan kungiyoyi uku a Sifaniya — Barcelona da Real Madrid da kuma Atlético Madrid.

Rashford ya zura ƙwallo mafi muhimmiyar a Barcelona a ranar Lahadi, wani bugu ya yi na gwanaye da ƙwallon ta faɗa raga a gefen kusurwa da ta buɗe wasan El Clásico.

Wannan ya zama lokaci mai ƙyau ga ɗan wasan mai shekara 28, wanda aka yi yarjejeniya, ƙungiyar Catalonia za ta iya sayan shi kan Yuro miliyan 35 (£30m) — duk da cewa har yanzu ba a yanke shawara ko za su mayar da shi ko kuma za su biyan kuɗi daga Manchester United.

Flick ya kuma samu yabo saboda yadda yake kula da ƴan wasansa.

Kocin ya ba Ronald Araújo hutu a watan Disamba domin ya kula da lafiyar kwakwalwarsa, ya bayyana lamarin a matsayin sirri. Flick bai bayyana ƙarin bayani ba kuma ya nemi kafafen yaɗa labarai su mutunta sirrin ɗan wasan.

Real Madrid ta durƙushe

Jude Bellingham slumped over with his hands on his knees during the loss to Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Real Madrid have lost six La Liga games this season

Yayin da Barcelona ke ƙara zama kan ganiya da inganta wasanninta, Real Madrid ta fara rasa maki a fafatawar da a kullum ake sa ran za ta ci nasara.

Wasu sakamakon wasanni sun ba ta matsala a watan Nuwamba da suka hada da na Elche da Rayo Vallecano da Girona, inda suka kara yaga ɓarakar Real Madrid da kuma matsayin kocin Xabi Alonso.

Waɗannan sakamakon ne suka yi tushen da Alonso ya bar Real Madrid a watan Janairu, jim kaɗan bayan da ƙungiyar ta sha kashi a hannun Barcelona a Spanish Super Cup.

Duk da haka a lokacin tana biye da abokiyar hamayya da tazarar maki huɗu a teburil La Liga.

Sai dai tazarar maki ta karu a tsakanin ƙungiyoyin biyu karkashin Álvaro Arbeloa, wanda ya gaji Alonso yanzu Real tana bayan Barcelona, wadda ta lashe La Liga na bana da tazarar maki 14 tsakaninsu.

A makon da ya gabata tun kan El Clásico, Real Madrid ta faɗa ruɗani, bayan da aka samu rigingimu tsakanin ƴan wasa, koda yake an ɗauki matakan ladabtarwa.

Real Madrid ta faɗa wannan koma bayar saboda raunin wasu ƴan wasanta da rashin amfani da damar makinta ga rashin jituwa tsakanin ƴan ƙwallo babu shugabanci a tsakaninsu, kociya ya kasa tasiri wajen kafa doka da oda ga kuma kaka ta biyu a jere ba tare da lashe kofi ba.

Ƙarin yiwuwar samun nasarori a Barcelona

Lokacin da Hansi Flick ya zo Barcelona a shekarar 2024, ya bayyana a fili cewa yana son salon ƙungiya ya mayar da shi kai hare-hare a koda yaushe da kuma kara jaddada ainihin salon taka leda da aka gina ƙungiyar.

Ya ce ra'ayinsa sun yi iri ɗaya da na Johan Cruyff da Pep Guardiola.

Waɗannan ƙa'idojin sun zama ginshiƙi a salon wasan Barcelona tun bayan da ya karɓi aikin kuma sun taimaka wa ƙungiyar wajen lashe La Liga karo na biyu a jere.

Barcelona ta nuna juriya a duk tsawon kakar bana. Ta fuskanci matsaloli har da raunin 'yan wasa da suka sa dole ta yi canje-canje a tsarin ƙungiya amma ba ta taɓa wani abu ya kawo mata cikas ba.

Flick ya yadda da batun haɗin kai da ladabi da juriya da kuma gogewa ta yadda yake jagorantar ragamar Barcelona.

Duk da rashin nasara a gasar zakarun Turai, inda Atlético Madrid ta fitar da ita a zagayen kwata fainal a Champions League, duk da haka Barcelona ta lashe La Liga da Spanish Super Cup, hakan ya nuna ci gaban da take samu a tamaula.

Da yake ƙungiyar tana cike da matasan ƴan ƙwallo masu hazaka, ana iya cewa makomar Barcelona tana da matuƙar haske da kyakkyawan fata.