Maguire zai iya barin Man U,Bayern Munich za ta rike Olise

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid na shirin shiga cikin jerin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan Portugal Mateus Fernandes, mai shekara 21, bayan West Ham ta rasa matsayinta a gasar Premier. (Sun), external

Brighton ta ki amincewa da tayi karo na biyu daga Tottenham Hotspur kan dan wasan Netherlands Jan Paul van Hecke, mai shekara 25.(Talksport), external

Watakila a amincewa Harry Maguire barin Manchester United a wannan bazara watanni bayan da dan wasan Ingila mai shekara 33 ya rattaba hannu kan sabon kwantaragi. (Football Insider), external

Inter Milan ta yi wa Liverpool tayin siyan dan wasan Ingila Curtis Jones, mai shekara 25, amma a halin yanzu kudin bai kai abinda Liverpool din ta ke son a biyata ba.(Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Watakila Liverpool ta sayar da dan wasan Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 27, a kokarinsu na siyan dan wasan Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, daga RB Leipzig. (Teamtalk), external

Bayern Munich ta ce ba ta da niyyar sayar da Michael Olise bayan Real Madrid ta ce za ta bada fan miliyan 130 kan dan wasan Faransa mai shekara 24.(Bild - in German), external

Bernardo Silva ya ce komawa Barcelona "wani zabi ne a wurinsa " bayan ya bar Manchester City amma har yanzu dan wasan Portugal, mai shekara 31, bai yanke shawara kan makomarsa ba.(Marca - in Spanish), external

Mai tsaron ragar Tottenham da Italiya Guglielmo Vicario, mai shekara 29, ya bayyyana a matsayin sabon mai tsaron raga daJuventus take son ta dauka .(Gazzetta dello Sport - in Italian), external