Lokuta biyar da arewa da gabashin Najeriya suka haɗu a siyasance

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan sabon ƙawancen siyasa da aka ƙulla tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, tuni wasu suka fara hasashen ko za ta ɓille.

A kwanakin baya ne fitattun ƴan siyasar guda biyu suka koma jam'iyyar NDC, sannan Peter Obi ya zama ɗan takararta ɗaya tilo, sannan ya zaɓi Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin wanda zai mara masa baya domin fuskantar babban zaɓen 2027.

Kafin komawarsu NDC, da farko sun fara shiga jam'iyyar haɗaka da ADC, kafin su biyun suka fice, suka koma NDC, inda suka ce rashin jituwa da kuma shari'o'in da ADCn ke fuskanta ne dalilansu na ficewa.

Sai dai haɗuwarsu a inuwa ɗaya ta haifar da muhawara, musamman a kafofin sadarwa.

Sai dai ba wannan ba ne karon farko da ake samun haɗakar siyasa tsakanin ɗan arewacin Najeriya da ɗan gabashin ƙasar domin fitowa takara tare ko mara wa wani baya.

Tun kafin samun ƴancin kai, shugabannin siyasa daga Arewa da gabashi sun riƙa ƙulla ƙawance domin kafa gwamnati ko shiga zaɓe da ma sauran harkokin mulki ko siyasa, inda a wasu lokutan ake samun nasara, wasu kuma ba a samu.

Wannan ya sa BBC ta yi tariyar lokutan baya da aka samu irin wannan ƙawance siyasar a baya.

Tafawa Ɓalewa da Azikiwe: Ƙawancen NPC da NCNC (1959)

Tun a Jamhuriya ta 1, an ƙulla ƙawancen siyasa tsakanin arewacin Najeriya da gabashin ƙasar a wani mataki da za a iya kira da ƙawancen siyasa ta farko da aka sani a tarihin ƙasar.

A haɗakar, wadda aka yi a shekarar 1959, jam'iyyar Jam'iyyar Northern People's Congress wato NPC ce a ƙarƙashin jagorancin Ahmadu Bello ta samu mafi yawan kujeru amma ba ta kai yawan da za ta kafa gwamnati ita kaɗai ba.

Wannan ya sa ya nema haɗa ƙawancen siyasa da jam'iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons wato NCNC ta Nnamdi Azikiwe domin kafa gwamnatin a matakin tarayya.

Wannan kawance ne ya share fagen samun ƴancin kai a shekarar 1960, inda ɗan jam'iyyar NPC Abubakar Tafawa Balewa ya zama Firaminista, yayin da Azikiwe ya zama shugaban ƙasar Najeriya na farko.

Ƙawancen ya yi tasiri matuƙa, kasancewar da ƙawancen aka fara gwamnatin tarayyar Najeriya ta farko, kuma har yanzu ana tattaunawa kan nasarorin da aka samu a zamanin.

Shagari da Ekwueme: Takarar shugaban ƙasa (1979)

Bayan hamɓarar da gwamnatin Jamhuriya ta 1, sai da aka kwashe kusan shekara 10 ana mulkin soja a ƙasar, kafin daga bisani shugaban ƙasa na mulkin soja, Olusegun Obasanjo ya yanke shawarar miƙa mulki ga farar hula a shekarar 1979.

A lokacin ne jam'iyyar National Party of Nigeria wato NPN ta tsayar da Alhaji Shehu Shagari daga jihar Sokoto takarar shugaban ƙasa.

Bayan tsayar da shi ne kuma sai jam'iyyar ta ɗauko Dr. Alex Ekwueme daga tsohuwar jihar Anambra, wadda ke gabashin Najeriya domin ya mara wa Shagari baya a matsayin mataimakinsa.

Ƙawancen ya yi nasara da tasiri, inda tikitin ya samu nasara, wanda ya ƙara taimakawa wajen haɗa kan ƙasar, musamman tsakanin ƙabilar Ibo da arewacin ƙasar bayan yaƙin basasa ya haifar da zaman tankiya.

Kuma Shehu Shagari da mataimakinsa sun cigaba da kasancewa a tare har zuwa lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a shekarar 1983.

Buhari da Okadigbo: Takarar shugaban ƙasa a ANPP (2003)

A shekarar 2003 ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi takarar siyasarsa ta farko, inda ya tsaya takarar a jam'iyyar ANPP domin fafatawa da shugaban ƙasa na lokacin, Olusegun Obasanjo wanda yake neman wa'adin mulki na biyu.

A lokacin ne Buhari ya zaɓi Dr. Chuba Okadigbo daga jihar Anambra a matsayin mataimakinsa.

Ko da yake sun sha kaye a hannun Shugaba Olusegun Obasanjo, tikitin ya nasara sosai domin sun samu ƙuri'a 12,710,022.

Atiku da Peter Obi: Takarar shugaban ƙasa a PDP (2019)

Alaƙar siyasa ta baya-bayan nan ita ce wadda aka yi tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi domin shiga zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2019.

Jam'iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da Peter Obi ya zama mataimakinsa.

An tsara tikitin ne domin haɗa ƙarfin siyasar Atiku a Arewa da kuma tasirin Obi a Kudu maso Gabas.

Sai dai shi ma tikitin bai samar da nasarar da ake so ba ta lashe zaɓe, amma tikitin ya yi tashe sosai a fagen siyasar ƙasar.

Peter Obi da Kwankwao: Takarar shugaban ƙasa a NDC (2026)

Ƙawancen siyasa da ke tashe a yanzu kuma shi ne haɗakar siyasa tsakanin tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da mai mara masa baya Rabiu Musa Kwankwaso.

Peter Obi ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour, yayin da shi kuma Rabiu Musa Kwankwanso ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP, dukkansu a babban zaɓen Najeriya na 2023, amma ba su samu nasara ba.

Wannan karon ne suka haɗu domin ƙulla ƙawance da za su shiga zaɓen 2027 domin fafatawa da gwamnati mai ci ta APC, wadda Bola Tinubu ke jagoranta.

Haka kuma sun ƙulla alƙawarin cewa idan NDC ta samu nasara, Peter Obi wa'adi ɗaya zai yi, sai ya ba Kwankwanso dama ya ɗaura, domin a cewarsu, akwai buƙatar a girmama tare da ɗabbaƙa tsarin mulkin karɓa-karɓa a siyasar Najeriya.

'Ƙawancen arewa da gabashi ya fi tasiri a Najeriya'

A wata tattaunawa da tashar Arise News, fitaccen ɗan jarida kuma dakartan labarai na tashar, Summer Sambo ya ce a tarihin Najeriya, ƙawancen siyasa tsakanin arewa da gabashin Najeriya ya fi haifar da ɗa mai ido.

Ya yi misali da haɗakar da aka yi a shekarun baya tsakanin Nnamdi Azikiwe da Ahmadu Bello da Tafawa Ɓalewa a Jamhuriya ta 1, da wadda aka yi a Jamhuriya ta 2 tsakanin Shehu Shagari da Alex Ekwueme.

"Ƙawancen siyasa a tarihin Najeriya da suka fi kyau da armashi su ne waɗanda aka yi tsakanin ƴan siyasar arewaci da gabashin ƙasar a shekarun baya," in ji a tattaunawarsa da tashar.

Ya ce ƙawance tsakanin Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso bai kamata ya zami wani sabon abu ba, inda ya ƙara da cewa lamari da aka daɗe ana yi tun a zamanin Jamhuriya ta 1.

"Irin wannan tsarin ne ya kamata mu riƙa a siyasar wannan lokacin. Siyasar aminci da nagarta, ba siyasa mara kangado ba, wadda ake yi tamkar Najeriya za ta shiga wani gagarumin yaƙi ne. Sannan kuma sai wasu suka cewa ba za a ba gabashin ƙasar damar shugabanci ba."