Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal da PSG na zawarcin Gibbs,Klopp ba ya son ya yi aikin koci a wata kungiya
Dan wasan Nottingham Forest Morgan Gibbs-White, mai shekara 26, yana cikin jerin 'yan wasan da Arsenal ke so a matsayin wanda zai iya maye gurbin dan wasan Aston Villa, Morgan Rogers , mai shekara 23, amma Gunners na fuskantar hammaya kan Gibbs-White daga Paris St-Germain.(Sun), external
Dan wasan PSG da Georgia Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 25,na cikin 'yan wasan da Florentino Perez ke son ya dauko idan ya yi nasara a zaben shugaban kungiyar Real Madrid kamar yadda wasu majiyoyi da ke da kusanci da kungiyar suka bayyana. (Teamtalk), external
Sabon kocin Real Madrid Jose Mourinho na son ya dauko Bernardo Silva bayan da dan wasan Portugal,mai shekara 31,ya bar Manchester City a karshen kakar wasa. (AS - in Spanish), external
Wakilin Jurgen Klopp ya ce Bajamushen ba ya son ya yi aiki a matsayin koci a wata kungiya bayan da dan takarar shugabancin Real Madrid Enrique Riquelme ya ce ya shirya zawarcin tsohon kocin Liverpool idan aka zabe shi.(Sky Sports Germany), external
Kawo yanzu Tottenham na son dan wasan Brazil Savinho mai shekara 22 kuma dan wasan zai so haka bayan da Manchester City ta ki amincewa da yunkurin da Tottenham ta yi a kakar wasa ta bara. (Mirror), external
Federico Chiesa na Liverpool ya ce yana bukatar ya kara buga wasa kuma dan wasan na Italiya mai shekara 28, zai tattauna da sabon kocin Reds Andoni Iraola kafin ya yanke shawara kan makomarsa. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external
Liverpool ba za ta sayar da Rio Ngumoha ba duk da cewa Bayern Munich na neman dan wasan na Ingila mai shekara 17 a bazara. (Sky Sports), external
Dan wasan Newcastle United da Ingila Harvey Barnes, mai shekara 28, ya bayyana a matsayin dan wasan da Aston Villa ke sha'awa. (Football Insider), external
Leeds United da Ipswich Town na hammayar da juna wajan daukar mai tsaron ragar Ingila Nick Pope mai shekara 34 daga Newcastle. (Sun), external