Arsenal da Juventus na hamayya kan Reijnders, Man United na son Tonali

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal da Juventus suna sanya ido kan ɗan wasan tsakiyar Manchester City Tijjani Reijnders, mai shekara 27, yayin da ɗan wasan na Netherlands ke samun taƙaitacen lokacin buga wasa tun zuwansa a bazarar da ta gabata. (TeamTalk)
Manchester United na da ƙwarin gwiwar kulla cinikin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Newcastle da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 26, da ɗan wasan Atalanta da Brazil Ederson mai shekara 26 a bana. (Sky Sports Italia)
Chelsea ta bi sahun Arsenal wajen zawarcin ɗan wasan gaban Bournemouth ɗan ƙasar Faransa Eli Junior Kroupi, amma Cherries ta ce ɗan wasan mai shekaru 19 ba na sayarwa bane. (Mail)
Ɗan wasan Fulham ɗan ƙasar Wales,Harry Wilson mai shekara 29, yana cikin jerin sunayen ƴan wasan da kocin Aston Villa Unai Emery zai yi zawarci a bazara bayan da aka ba shi kasafin kudin sayan ƴan wasa fam miliyan 100 sakamakon nasarar da kulob ɗin ya samu a gasar cin kofin Europa League. (Mirror)
Har ila yau Everton na sha'awar Wilson, wanda za a iya ɗaukarsa a cinikin kyauta idan kwantiraginsa ya kare a watan Yuni. (Sky Sports)
Brighton na tattaunawa da Olympiacos kan cinikin Costinha ɗan ƙasar Portugal mai shekara 26 wanda ke ɗauke da farashin fam miliyan 11. (Athletic)
Newcastle za ta yi zawarcin ɗan wasan gaban Porto ɗan ƙasar Belgium Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21, idan ɗan wasan gaban Ingila Anthony Gordon, mai shekara 25, ya bar kulob ɗin a bazara. (Mail)
Manchester United na kallon ɗan wasan baya na Newcastle Lewis Hall a matsayin wanda zai iya bunƙasa tawagar ƴanwasanta a kakar wasa mai zuwa, yayin da Bayern Munich da Liverpool su ma su ke sanya ido kan ɗan wasan na Ingila mai shekara 21. (Teamtalk)
Inter Milan na nazarin zawarcin golan Arsenal ɗan ƙasar Spain Kepa Arrizabalaga mai shekara 31. (Gazzetta)
Naɗin Xabi Alonso a matsayin kocin Chelsea na iya lalata fatan Atletico Madrid na ɗaukar Marc Cucurella, mai shekara 27, inda kocin mai shekara 44 ke sha'awar ci gaba da riƙe ɗan wasan bayan na Spain. (Mundo Deportivo)
Arsenal na shirin miƙawa ɗan wasan baya na ƙasar Netherlands Jurrien Timber mai shekara 24 da sabon kwantaragi. (Caught Offside)
Liam Delap yana gab da barin Chelsea, inda Everton ke kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan na Ingila mai shekara 23. (Football Insider)











