Karin kumallo ko abincin dare: Wanne ya fi amfani ga lafiyar jiki?

Kosai da tuwo

Asalin hoton, maryaaamah_/IG

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Cin karin kumallo mai yawa da kuma taƙaita abincin dare na iya taimakawa wajen rage ƙiba, kamar yadda masu bincike suka bayyana.

A yayin wannan binciken, masana kimiyya sun tsara abincin mahalarta gwajin cikin tsanaki domin kwatanta tasirin cin karin kumallo mai yawa da kuma cin abincin dare da yawa.

Tawagar masu bincike daga Jami'ar Aberdeen ta gano cewa mutanen da suka rage yawan kuzarin abinci (kalori) da suke ci sun kasance suna samun adadin kalori iri ɗaya a duk lokacin da suka ci mafi yawan abincinsu na ranar.

Sai dai kuma sun lura cewa sha'awar cin abinci ta ragu matuƙa bayan mahalarta gwajin sun fara cin karin kumallo mai yawa, wanda hakan ya sa ya fi sauƙi mutum ya kula da daidaiton abincinsa.

Masu binciken sun kuma gabatar da ra'ayin cewa dare shi ne mafi munin lokacin cin abinci, domin a wannan lokaci tsarin narkar da abinci na jiki yana sauya abincin zuwa sinadarai yayin da jiki ke aiki cikin yanayi na hutawa, musamman idan mutum yana barci.

Yadda aka gudanar da binciken

An bai wa mahalarta 30 da suka shiga wannan bincike karin kumallo da abincin rana da kuma abincin dare na tsawon sama da wata biyu, inda aka ƙara musu kuzarin abinci mai adadin kalori 1,700 a kowace rana.

A cikin wata na farko, sun kasance suna cin karin kumallo mai nauyi wanda ke ɗauke da kusan rabin adadin kalorin da suke buƙata a rana, sannan su ci abincin rana da na dare masu sauƙi.

Amma a wata na gaba, an sauya tsarin ta yadda suka riƙa cin abinci da dare maimakon da safe.

Masana sun auna yadda jikin ɗan Adam ke sarrafa abinci da kuzari (metabolism) daidai gwargwado ta amfani da ruwa da aka ƙara masa wasu sinadarai masu nauyi fiye da na ruwa na yau da kullum, wanda za a iya bibiyar yadda yake fita daga jiki cikin sauƙi.

Me binciken ya gano?

Tuwo

Asalin hoton, maryaaamah_/IG

Sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar kimiyya ta Cell Metabolism, ya nuna cewa lokacin da aka ci abinci mai yawa bai haifar da wani bambanci ba, musamman ta fuskar yawan kalorin da jiki ke ƙonawa, saurin tafiyar sinadarai a jiki (metabolic rate), ko kuma rage nauyi.

Sai dai babban bambancin da aka gani shi ne a matakin yunwa da sha'awar cin abinci, inda cin karin kumallo mai nauyi ya fi taimakawa wajen rage yunwa da sarrafa sha'awar cin abinci.

Abincin safe

Asalin hoton, maryaaamah_/IG

Jagorarar binciken, Farfesa Alexandra Johnstone ta ce wannan binciken na da matuƙar muhimmanci ga duniya, musamman dangane da adadin abincin da mutum ke ci

"Binciken ya nuna muhimmancin sarrafa sha'awar cin abinci ta hanyar cin karin kumallo mai nauyi.

Idan mutum ya fara ranarsa da lafiyayyen karin kumallo, akwai yiwuwar ya ci gaba da kasancewa cikin kuzari da motsa jiki tare da iya sarrafa yunwa da sha'awar cin abinci a tsawon ranar."

Karin kumallon da aka ba mahalarta binciken ya ƙunshi miya da yogurt da ƙwai da tsire (nama), dukkansu kuwa suna ɗauke da sinadarin protein mai yawa wanda ke taimakawa mutum ya ji ya ƙoshi na tsawon lokaci.

Har yanzu ba a tantance ainihin dalilin da ya sa cin karin kumallo mai nauyi ke rage sha'awar cin abinci ba.

Sai dai masu binciken sun ce lamarin ya fi rikitarwa fiye da kawai mutum ya cika cikinsa da safe sannan ya kwanta da yunwa da dare.