Aston Villa ta taya Amad, Arsenal na nazari kan Fernandez-Pardo

Danwasan Manchester United da Ivory Coast attacker Amad Diallo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyoyin Italiya da dama sun nuna sha'awar ɗanwasan gaba na Newcastle Nick Woltemade, mai shekara 24, kuma Napoli ce ta fi nuna buƙatar karɓar aron ɗanwasan na Jamus. (Sky Sports)

Sunderland na son karɓar aron ɗanwasan Manchester City Jack Grealish kuma tana da tabbacin cimma yarjejeniya kan ɗanwasan na Ingila mai shekara 30. (Football Insider)

Arsenal na nazari kan ɗanwasan gaba na Lille Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21, kuma sai ta lale fam miliyan 60 kan ɗanwasan na Belgium. (Caught Offside)

Ɗanwasan gaba na Crystal Palace Ismaila Sarr, mai shekara 28, na son zuwa Liverpool yayin da ƙungiyoyin biyu ke ci gaba da tattaunawa kan ɗanwasan na Senegal. (Sun)

Sunderland na nazari kan ɗanwasan gaba na Levante Karl Etta Eyong, mai shekara 22, kuma sai ta biya fam miliyan 26 kan ɗanwasan na Kamaru. (Sun)

Fiorentina ta tuntuɓi Leeds United kan buƙatar ɗanwasan gaba na Italiya Wilfried Gnonto. (Athletic - subscription required)

Sunderland na dab da karɓo ɗanwasan gaba na Marseille Igor Paixao, mai shekara 26, amma ƙungiyar ta Faransa ba ta son rabuwa da ɗanwasan na Brazil. (Teamtalk)

Aston Villa ta taya ɗanwasan Manchester United da Ivory Coast attacker Amad Diallo, mai shekara 24. (225 Foot - in French)

AC Milan ta cimma yarjejeniya da Nottingham Forest kan ɗanwasan gaba ɗan ƙasar Ingila Omari Hutchinson. (Sky Sports)