An wanke Neymar da soso da sabulu kan zargin fyade

Neymar

Asalin hoton, Getty Images

'Yan sanda a Brazil sun tuhumi wata mata da ta ce Neymar yayi mata fyade, a wani Otal da ke birnin Paris na kasar faransa, da yawo da hankalin shari'a.

Ana tuhumar Najila Trindade tare da mijinta Estivens Alves da bai wa 'Yan sanda labaran karya, da kuma kokarin bata wa shahararren dan wasan kwallon kafar suna.

Kotun dai ta wanke dan kwallon da ke taka leda a Paris St-Germain ta kasar faransa.

Sai dai lauyan da ke kare matar Cosme Araújo ya ce ya yi mamakin hukuncin da kotun ta yanke.

Cosme Araújo ya kuma yi watsi da tuhumar 'yan sandan, inda ya karyata zargin da ake yi wa wadda yake karewa na hada baki da Mista Alves domin samun wasu kudade daga hannun dan wasan dan asalin Brazil.

Wannan labarin dai ya dauki tsawon makonni yana jan hankalin mutane a kafafen jaridu ciki har da magoya bayan sa.

Kafin fitowar wannan labarin, Neymar ya wallafa wani faifan bidiyo da hotuna a wani shafin sa na sada zumunta, inda yake cewa ya kamata ya shaida wa duniya babu wani abu da ke da alaka da fyade da ya shiga tsakanin sa da matar.

Sai dai ya ce ya hadu da wannan mata a kafar Internet, inda ya shirya mata tafiya zuwa Faransa domin su gana.

Bayan da ta koma kasar Brazil ne Trindade ta wuce ofishin 'yan sanda, domin mika korafin cin zarafin da Neymar din yayi mata.

Daga bisani ne kuma matar ta bayyana wa duniya abin da ke tsakanin ta da dan wasan.

Bayan da aka yi hira da ita a wani gidan talibijin din kasar, da kuma sako wani faifan bidiyo da ke nuna musayar yawun da ya wakana a tsakanin ta da Neymar din.

Daga bisani ne kuma 'yan sanda suka tuhume ta da laifin ba ta suna. Inda ita kuma ta ke zargin 'yan sandan da karbar rashawa, inji AFP

Neymar ya musanta zarge-zargen da ake masa tun daga fari, inda yace ana yunkurin ba ta masa suna ne.

Ofishin Antoni Janar da ke Sao Paulo ya ce an dakatar da karar ne, sakamakon rashin kwararan hujjoji.