Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 18ga watan Yulin 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. An yi kutse a shafin intanet ɗin fadar shugaban kasar Kenya

    An yi zargin cewa wasu masu kutse ta intanet sun kutsa cikin shafin intanet ɗin fadar shugaban Kenya, William Ruto, tare da neman a biya su kudin bitcoin biyar, wanda darajarsa ta kai kimanin shilling miliyan 41 na Kenya (dala 320,000) kafin su saki shafin a cewar rahotannin kafafen yada labaran cikin gida.

    Masu kutsen sun canza shafin gaba na intanet ɗin inda suka maye gurbin bayanan hukuma da saƙonnin cin mutunci ga shugaban kasar tare da barazanar fitar da wasu muhimman bayanan gwamnati.

    A halin yanzu, shafin president.go.ke ba ya aiki, kuma yana nuna saƙon cewa ana gudanar da gyare-gyare kuma za a dawo da shi nan ba da jimawa ba.

    Har yanzu hukumomin Kenya ba su yi wani jawabi kan wannanba.

    Lamarin na zuwa ne watanni kaɗan bayan wani babban harin kutse a watan Nuwamban 2025 wanda ya shafi wasu shafukan intanet na gwamnati a abin da hukumomi suka bayyana a matsayin hari na hadin gwiwa

  2. Kuwait ta ba da rahoton tashin gobara biyu sakamakon hare-haren Iran

    Kuwait ta ce hare-haren da Iran ta kai ranar Asabar sun haddasa tashin gobara a wurare biyu a ƙasar, lamarin da ya jikkata wasu daga cikin jami'an kashe gobara.

    Tun da farko dai an ba da rahoton cewa Iran ta kai hari kan wata tashar samar da wutar lantarki da kuma cibiyar tace ruwan teku a ƙasar.

    Hukumar kashe gobara ta Kuwait ta bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafin X cewa jami'anta na aiki kan kashe gobara biyun da suka tashi sakamakon sabbin hare-haren Iran ɗin.

    Hukumar ta kuma ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa cibiyoyin kiwon lafiya domin samun kulawa..

  3. Shugaban Lebanon ya tafi Washington don ganawa da Trump

    Shugaban ƙasar Lebanon, Joseph Aoun, ya bar birnin Beirut zuwa Washington, inda ake sa ran zai gana da shugaban Amurka Donald Trump, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.

    Ziyarar tasa na zuwa ne bayan kammala zagaye na shida na tattaunawar Lebanon da Isra'ila, wanda aka gudanar a ofishin jakadancin Amurka da ke Rome a Italiya a ranakun 13 da 14 ga watan Yuli.

    Fadar shugaban ƙasar Lebanon ta ce Aoun zai yi tattaunawa da wasu manyan jami'an Amurka kan halin da ƙasar ke ciki da kuma hanyoyin ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita wuta, musamman a kudancin Lebanon.

    Ana kuma sa ran za a tattauna batun janye sojojin Isra'ila daga wuraren da har yanzu suke mamaye da su a Lebanon, wanda ke daga cikin manyan batutuwan da ke gaban ƙasashen biyu.

  4. Ba za mu lamunci ana tattaunawa ana kai hare-hare ba - Iran

    Iran ta ce ba za ta ci gaba da amincewa da salon gudanar da tattaunawa tare da ci gaba da kai hare-hare a lokaci guda ba, tana mai gargaɗin cewa idan Amurka ta ci gaba da yaƙin cikin kwanaki biyu ko uku masu zuwa, za ta ɗauki matakin mayar da martani mafi tsauri na ba sani ba sabo.

    Mai ba Jagoran addinin Iran shawara kan harkokin soja, Mohsen Rezaei, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi ta talabijin, inda ya ce manufar “ana tattaunawa ana kuma yaƙi” ta zo ƙarshe.

    Ya ƙara da cewa Iran tana mutunta gwamnatoci da al'ummomin duniya, amma za ta ci gaba da kai farmaki kan sojojin Amurka da sansanoninsu idan rikicin ya ci gaba.

    Rezaei ya ce Iran na nuna taka-tsantsan ne saboda tsoron rikicin ya bazu zuwa wasu yankuna, yana mai cewa hakan na iya haddasa sabbin rikice-rikice tsakanin ƙasashe daban-daban, ciki har da Turkiyya da Isra'ila, China da Taiwan, da kuma Rasha da Turai.

    A cewarsa, Iran ba ta son ganin yankin ya faɗa cikin wani babban rikici.

    Ya kuma yi kira ga al'ummomin yankin da su taimaka wajen hana rikicin ƙara kamari, yana mai cewa batun yaƙi abu ne mai matuƙar muhimmanci.

    Rezaei ya gargɗii Amurka da cewa ta yi tsammanin sabbin hare-haren makamai masu linzami idan rikicin ya ci gaba.

  5. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'ƴan ta'adda' biyu da ceto mutum uku a Benue

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Whirl Stroke tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron al'umma na jihar Benue sun kashe wasu da ake zargin 'yan ta'adda biyu tare da ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

    A cewar sanarwar rundunar, an fara aikin ne da misalin ƙarfe 3 na safiyar ranar 16 ga Yulin 2026, inda sojojin suka bi ta Takum a jihar Taraba zuwa ƙauyukan Tse Togo da Utenge da ke kusa da sansanin Orter, inda aka ce waɗanda ake zargin 'yan ta'addan ne ke fakewa.

    "A yayin musayar wuta kuma sojojin suka samu nasarar kashe mutum biyu daga cikinsu." in ji sanarwar.

    Mutanen da aka ceto dukkaninsu mazauna ƙaramar hukumar Katsina-Ala ne in ji sanarwar.

    Rundunar ta ce wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin yayin artabun.

    Sojojin sun kuma ƙwato makamai da harsasai daban-daban da kayan soji yayin samamen.

  6. Kotu ta yi watsi da ƙarar PDP ɓangaren Turaki

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin jam'iyyar PDP suka shigar domin tilasta wa hukumar zaɓe ta INEC, ta amince da kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

    Alƙali Salim Ibrahim ya yanke hukuncin cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ƙarar. Saboda haka kotun ta ce ba ta da ikon sauraron shari'ar.

    Alƙalin ya ce masu ƙarar sun kasa tabbatar wa kotu cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar da suke goyon baya, ko kuma cewa suna da ikon shigar da ƙara a madadin jam'iyyar PDP.

    Shugaban kwamitin amintattu na PDP tsagin Turaki ƙarƙashin Sanata Adolphus Wabara, tare da wasu mambobin kwamitin ne suka garzaya kotu suna neman a umarci INEC ta sabunta bayananta tare da amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki.

    Sun kuma buƙaci kotun ta umarci hukumar zaɓen ta wallafa sunayen shugabannin riƙon ƙwaryar a shafinta na intanet.

    Sai dai wani tsagin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya nemi shiga shari'ar tare da ƙalubalantar ikon kotun, inda ya ce shi ne shugabancin PDP halastacce, kuma masu ƙarar ba su da hurumin shigar da ita a madadin jam'iyyar.

  7. Me ya bambanta ƴansandan jihohi da 'askarawan' da gwamnoni suka samar?

    Ana ci gaba da tattaunawa a Najeriya kan shirin kafa rundunar ƴansandan jihohi, bayan Majalisar Dokokin tarayyar kasar ta amince da ƙudurin dokar.

    Majalisar ta amince da ƙudurin ne bayan karatu na biyu, inda aka zaɓi amfani da ƙudurin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a maimakon wanda ƴan majalisa suka gabatar tun da farko.

    Buƙatar kafa ƴansandan jihohi dai ta daɗe tana cikin abubuwan da gwamnonin ƙasar ke nema. Sun yi ta jaddada cewa rashin ikon kafa rundunar ƴansanda ta jiha na hana su ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunansu.

    Tun kafin wannan yunƙuri, jihohi da dama sun riga sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida, kamar ƴan sa-kai, ƴan banga da kuma askarawa, domin taimakawa jami'an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi.

    Sai dai akwai masu nuna damuwa cewa idan aka kafa ƴansandan jihohi, za su iya kasancewa tamkar waɗannan rundunonin da ake da su yanzu, waɗanda ake yawan zargin su da rashin ƙwarewa da kuma cin zarafin jama'a a wasu lokuta.

  8. Iran ta ce ta kai hari kan wuraren adana man Amurka a Bahrain

    Sojojin Iran sun yi iƙirarin cewa sun kai hari kan wuraren ajiyar jiragen sama da tankunan adana man fetur a sansanin Sheikh Issa da ke Bahrain, wanda suka bayyana a matsayin sansanin Amurka, ta hanyar amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    A cikin sanarwar, sojojin sun kuma ce sun kai hare-hare kan gadoji da dama a Bahrain.

    Sai dai kawo yanzu, hukumomin Bahrain ko na Amurka ba su fitar da wata sanarwa ba game da girman ɓarnar da aka yi, ko kuma ko akwai waɗanda suka jikkata ko suka mutu sakamakon hare-haren.

  9. Hare-haren Amurka kan kayayyakin more rayuwar Iraniyawa laifin yaƙi ne - Iran

    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya aika wa Kwamitin Tsaro na MDD wasika inda ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Amurka ta kai kan kayayyakin more rayuwar fararen hula a Iran.

    Iravani ya ce hare-hare da ake ci gaba da kai wa wuraren fararen hula, musamman muhimman hanyoyin mota da na jirgin kasa, sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma sun kai matsayin laifin yaƙi.

    Jakadan ya kuma yi gargadin cewa idan Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro ba su dauki matakin da ya dace ba, Iran za ta ci gaba da amfani da haƙƙinta da dokokin kasa da kasa suka tanada domin kare ikon ƙasarta, mutuncin yankinta, al'ummarta da muhimman muradunta na kasa.

  10. Assalamu alaikum

    Mabiya shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar, hutun ƙarshen mako.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.