KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 27 ga watan Mayun 2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Haruna Ibrahim Kakangi

  1. Ghana ta kwashe ƴan ƙasarta kusan 800 daga Afirka ta Kudu

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'ai daga Ghana sun mayar da kusan 'yan ƙasar 800 zuwa gida daga Afirka ta Kudu.

    Hakan ya biyo bayan zanga zangar nuna ƙyama ga baƙin hauren da ake a wasu sassan biranen Afirka ta Kudu fiye da wata guda ke nan.

    Wakiliyar BBC ta ce ta ga yadda gwamman mutane ke fita daga motocin bas inda suka isa filin jirgin saman Tambo suna hawa jirgin zuwa Accra.

    Jakadan Ghana a Afirka ta Kudu ya ce gwamnatinsu na son tabbatar da cewa 'yan Ƙasarsu sun kuƁuta daga hare-haren da ake kai wa baƘin hauren.

    Ghana ta ce tana tabbatar da tsare lafiyar 'yan Ƙasarta.

    WaƊanda suke zanga zangar sun ce yawancin mutanen da ke shiga cikin Ƙasar ta Afirka ta Kudu ba bisa Ƙa'ida ba na mamaye musu guraben aiki a ma'aikatun gwamnati.

  2. Isra'ila ta yi iƙirarin kashe sabon kwamandan Hamas

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ce ta kashe wani Shugaban ɓangaren mayaƙan Hamas, Mohammed Odeh a wani hari da ta kai Gaza ranar Talata - kwanaki bayan mutuwar magabacinsa a wani hari makamancin wannan.

    Aƙalla Falasɗinawa uku aka kashe sannan gommai sun ji rauni a gagarumin harin na ranar Talata wanda ya faɗa kan wani gida a ɗaya daga cikin manyan kasuwannin birnin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.

    Sojojin Isra'ila sun ce an kai hari kan gine-ginen da ke zama maɓoyar Odeh bayan da aka bibiye shi tsawon watanni.

    Zuwa yanzu Hamas ba ta ce komai ba kan lamarin.

    Shi ne hari mafi muni da Isra'ila ta kai kan Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Hamas wadda ta fara aiki a Oktoba.

  3. Musulmi na bikin babbar sallah a faɗin duniya

    Al'ummar Musulmai a faɗin duniya na bikin idin Babbar Sallah, bayan hawan Arafah jiya Talata a Ƙasa Mai Tsarki.

    Ranar na cikin manyan ranakun bikin Musulunci biyu a shekara.

    Biki ne da akan yanka rago ko sa inda wasu ke bayar da naman sadaka ga mabuƙata.

    Musulmi na yin amfani da muhimmin lokacin wajen sada zumunci a tsakanin ƴan'uwa da abokan arziki.

    A bana ranar ta zo daidai da ranar yara ta duniya da ake yi duk 27 ga watan Mayu.

    Kazalika, sallar ta zo yayin da ake ci gaba da yin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

  4. Barka da Sallah

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan rana da Musulmi a faɗin duniya ke bikin sallah babba.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.