Shettima ya gabatar da jawabin Najeriya a taron BRICS

Asalin hoton, Kashim Shettima
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya gabatar da jawabin Najeriya a taron shugabannin ƙasashen BRICS na shekarar 2026 da ke gudana a New Delhi, India.
A cikin jawabin da ya gabatar a madadin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, Shettima ya yi kira da a gaggauta sake fasalin tsarin shugabancin duniya da cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, domin samar da tsarin da ya fi wakilci, adalci da kuma amsa buƙatun ƙasashe.

Asalin hoton, Kashim Shettima

Asalin hoton, Kashim Shettima
Ya ce Najeriya na goyon bayan tsarin da zai yi daidai da sauye-sauyen tattalin arziki daidai yawan jama'a na duniya.
Mataimakin shugaban ya kuma gayyaci masu zuba jari daga ƙasashen waje da su yi amfani da damarmakin zuba jari da ke Najeriya, yana mai cewa ƙasar na iya zama hanyar shiga babbar kasuwar Afirka a ƙarƙashin yarjejeniyar AfCFTA.

Asalin hoton, Kashim Shettima

Asalin hoton, Kashim Shettima
A gefe guda kuma, Najeriya da India sun sake tabbatar da aniyarsu ta ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu.
Ministarsu harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta gana da takwaranta na India, Dr. Jaishankar, a yayin taron, inda suka tattauna batutuwan kasuwanci, ilimi, al'adu da kuma harkokin ofishin jakadanci.
Sun kuma tattauna batun jin daɗin ƴan Najeriya da ke zaune a India, musamman waɗanda suka wuce wa'adin bizar su.

Asalin hoton, Kashim Shettima

Asalin hoton, Kashim Shettima
Ministar ta nemi a ƙara wa'adin afuwar da ake da shi, domin bai wa waɗanda abin ya shafa damar komawa Najeriya da kansu ba tare da fuskantar hukunci ba.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna yiwuwar kulla yarjejeniyar musayar mutanen da aka yanke wa hukunci a gidan yari, da kuma hanyoyin faɗaɗa kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen.
Taron na BRICS India ce ke karɓar baunci a wannan shekara.






















