KAI TSAYE, Muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 23 ga watan Yuli, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammad

  1. 'Amurka ta yi amfani da jirgin yaƙi na B-1 wajen kai wa Iran hari'

    Jirgin yaƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafar yaɗa labarai ta Axios a Amurka, ta ambato wasu jami'an ƙasar na cewa sojojin Amurka sun yi amfani da jirgin yaƙi ƙirar B-1 mai tafiyar dogon zango, domin kai hari kan wasu cibiyoyin Rundunar juyin juya halin Iran a ranar talata.

    A cewar rahoton, wannan ne karon farko da aka yi amfani da jirgin tun bayan dawowa yaƙin a kwanaki 12 da suka gabata.

    Kafar Axios ta ce jirgin na B-1 ya tashi daga sansanin sojin saman Amurka da ke Ingila, kuma an riƙa bibiyar tafiyarsa ta hanyar shafin kula da zirga-zirgar jirage.

    Rahoton ya ce jirgin, wanda zai iya ɗaukar bama-bamai 24 masu nauyin kilogiram 900 kowannensu, ko kuma manya-manyan makaman linzami masu dogon zango.

    Wannan al'amari ya nuna ƙaruwar ayyukan soijin Amurka a Iran.

    To sai dai rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ba ta sanar da amfani da jirgin ba, cikin sanarwar kai harin da ta fitar a ranar Talatar.

    A sanarwa tata, CENTCOM ta ce dakarunta sun ƙaddamar da hare-hare kan cibiyoyin sojin Iran, da kayayyakin aikinsu

  2. Dole Saudiyya ta amince da Isra'ila kafin mu cimma yarjejeniyar nukiliya - Trump

    Trump da yariman Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yarjejeniyar nukiliya tsakanin ƙasarsa da Saudiyya za ta fara aiki ne kawai idan Saudiyyar ta amince da shiga yarjejeniyar Abraham da aka fi sani da fi sani da Abraham Accords, wadda ke nufin amincewa da gwamnatin Isra'ila a hukumance.

    A baya-bayan ne dai Amurka da Saudiyya suka amince da ƙulla yarjejeniyar samar da nukiliya na zaman lafiya ga Saudiyya.

    To sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce ''Za a amince da Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Fasahar Nukiliya ta Farar Hula, wadda ta taƙaita ne ga amfani da makamashin nukiliya ba don harkokin soja ba, amma hakan ya dogara ne da shigar Saudiyya Yarjejenar Abraham''.

    Sharaɗin na Trump na zuwa ne bayan da masana suka yi gargaɗin cewa yarjejeniyar za ta iya ƙara hatsarin bazuwar makaman nukiliya a yankin Gabas ta Tsakiya da ke fama da rikice-rikice''.

    Batun nukiliya na daga cikin abubuwan da suka jima suna haɗa Amurka da Isra'ila faɗa da Iran.

    A 2020, Shugaba Trump ya samu nasarar cimma yarjejeniyar Abraham, wadda ta sa ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahraine suka kyautata alaƙar diplomasiyyarsu da Isra'ila.

    Daga kuma ƙasashen sudan da Moroko suka bi sahunsu.

  3. DSS ba ta gamsu da hukuncin da aka yanke wa waɗanda suka sace ɗaliban Oyo ba

    Jami'an DSS

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta ce za ta ɗaukaka kara game da hukuncin da kotu ta yanke wa wasu mutum uku da aka samu d alaifin hannu a sace ɗaliban jihar Oyo.

    A yau Alhamis ne Babbar koton Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutanen uku, yan asalin jihar Neja hukuncin daurin rai da rai bayan samunsu da laifi a garkuwa da ɗaliban.

    Sai dai hukumar ta DSS, wadda ta gurfanar da mutanen ta ce hukuncin da kotun ta yanke musu ya yi kaɗan idan aka kwatanta da laifin da suka aikata.

    Hukumar ta kafa hujja da kisan malaman makarantar biyu da masu garkuwar suka yi lokacin da suke hannunsu.

  4. An yanke wa waɗanda suka sace ɗaliban Oyo hukuncin ɗaurin rai da rai

    Oyo

    Asalin hoton, Attorney-General of di Federation (AGF)

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke wa wasu mutane uku hukuncin ɗaurin rai da rai da aka kama bisa hannu a garkuwa da ɗaliban jihar Oyo da malamansu a karamar hukumar Oriire.

    Alƙalin kotun Maishari'a Salim Ibrahim ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bayan da suka amsa duka laifukan da ake tuhumarsu.

    Mutanen uku su ne Abdulrazak Umar, da aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid da Yunusa Musa da aka fi sani da Yunusa Bin Musa da kuma Shamsu Adamu Sani da aka fi sani da Abu Itisar.

    Kotu ta samu mutanen uku waɗanda dukansu ƴan asalin jihar Neja ne da laifukan ɓoye bayanan mutane masu alaƙa da ta'addanci, da yin garkuwa da mutane da kuma amfani da dandalin saƙonni wajen horas da ayyukan ta'addanci.

    Maishari'a Salim Ibrahim ya ce mutanen uku ƴan ƙungiyar Darul Salam ne, mai biyayya ga ƙungiyar Ansaru.

    A makon da ya gabata ne Babbar Kotun Tarayyar ta yanke wa wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru da hukumar DSS ta kama hukunci.

  5. Ana taƙaddama kan rashin ganin shugaban Kamaru Paul Biya

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Kamaru Paul Biya, wanda shi ne mafi tsufa a duniya - kuma wanda ya bar ƙasar sama da kwana 40 da suka gabata - ya amince da karɓo bashi domin aiwatar da kwangiloli.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tsawon lokacin da ya kwashe ba tare da dawowa ƙasar ba.

    A wasu matakai daban-daban da ya ɗauka a ranar Laraba, shugaban mai shekara 93 ya buƙaci ministan tattalin arziki da ci gaban yankunan ƙasar ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin karɓar bashi daga ƙungiyar ci gaban ƙasashen duniya (IDA) da kuma Bankin Deutsche na Spaniya.

    Haka nan kuma shugaban ya naɗa wasu jami'ai biyu na hukumar kula da harkar man fetur da iskar gasa ta ƙasar duk a ranar guda.

    Sai dai kasancewar babu wanda ya sanya ido kan shugaban ƙasar tun daga ranar 7 ga watan Yuni, matakan da aka ce shugaban ya ɗauka sun tayar da ƙura, inda mutane da dama a ƙasar ke neman sanin inda shugaban yake da kuma gaskiyar bayani game da lafiyarsa.

    Sai dai na kusa da Biya sun bayyana tafiyar tasa zuwa ƙasashen waje a matsayin "taƙaitaccen hutu na ƙashin kai a nahiyar Turai", to sai dai daɗewar tasa ba tare da an gan shi ba na ci gaba da haifar da muhawara tsakanin al'ummar ƙasar.

    Lamarin ya haifar da raɗe-radi game da lafiyar shugaban ƙasar - wani abu da ba kasafai aka cika tattaunawa kansa ba a bayyane, a ƙasar, wadda Biya ya kwashe shekara 44 yana mulka.

    A ranar 17 ga watan Yuni, mujallar Jeune Afrique ta ruwaito cewa an kwantar da Paul Biya a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Geneva na ƙasar Switzerland bayan fama da wani zazzaɓi jim kadan bayan bikin zagayowar ranar ƴancin kan ƙasar a watan Mayu.

    Sai dai ministan yaɗa labarai na ƙasar Rene Emmanuel Sadi ya fito nan take ya ƙaryata rahoton a wata sanarwa da ya fitar washegari, inda ya bayyana labarin a matsayin maras tushe.

    Duk da cewa Sadi ya tabbatar da cewa Paul Biya yana birnin Geneva, amma ya ƙaryata batun cewa an kai shugaban ƙasar asibiti, kuma sannan babu wata matsala a game da lafiyarsa kamar yadda mujallar ta ruwaito.

    "Duk da cewa shugaban ƙasar zai iya yin amfani da damarsa a lokacin da yake hutu a Geneva domin ganin likita a duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, amma yana ci gaba da lura da al'amuran ƙasar yadda ya kamata kuma yana ɗaukar matakan da suka dace a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ya bayyana.

    Rashin ganin nasa na tsawon lokaci ya janyo martani daga jam'iyun adawa, inda wani ɗan majalisar dokokin ƙasar ya buƙaci majalisar tsarin mulkin ƙasar ta yi amfani da ƙarfinta wajen sauke shugaban ƙasar.

    Sai dai a martanin da ta mayar, jam'iyyar CPDM mai mulkin ƙasar ta yi watsi da batun, tare da cewa shugaban na kan muƙaminsa daram, sannan ta ƙara da cewa duk wani kalami irin hakan tamkar ƙirkirar doka ce da ba ta wanzuwa.

    "Babu wata doka ko tanadi a Kamaru da ya ƙayyade iyakar lokacin da shugaban ƙasa zai iya kwashewa ba ya ƙasar," in ji mai magana da yawun gwamnati a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya jaddada cewa Biya na ci gaba da aiki daga inda yake.

    A dokokin Kamaru, za a iya ayyana gurbi a muƙamin shugaban ƙasa ne kawai idan shugaban ya ajiye aiki don raɗin kansa, ko ya mutu ko kuma majalisar kundin tsarin mulki ta ayyana shi a matsayin wanda ba zai iya gudanar da ayyukan da suka rataya a kansa ba.

    Rashin ganin Biya na ƙara tayar da ƙura ne kasancewar hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake muhawara kan naɗa mataimakin shugaban ƙasar da kuma yin garanbawul ga majalisar zartarwa, wanda masharhanta ke ganin cewa har ma an makara.

    A tsawon mulkinsa, wanda ya fara tun a shekarar 1982, shugaban na Kamaru yakan yi tafiye-tafiye akai-akai da kwashe lokuta masu tsawo a ƙasashen turai, inda sau da dama hakan kan haifara da rade-radin mutuwarsa.

  6. Yadda aka yi wa manoma sama da 20 kisan gilla a Zamfara - Amnesty

    Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal

    Asalin hoton, FB/Dauda Lawal

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal

    Sama da mutum 20 ne mahara suka kashe a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ya daɗe yana fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

    Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba ya rutsa da manoma waɗanda suka raja'a wajen aikin gona.

    Wani wanda ya ga abin da ya faru ya shaida wa BBC cewa: "Muna gona muna aiki aka ce ga su nan sun taho, kafin mu ankara sun riga sun rufe mu, sun rufe ko ina, idan ka gudu sai su buge ka da mashin su harbe ka sannan su take ka.

    "Sun zo ne a babura sun kai 100, suka riƙa bin mutane suna kashewa, sannan suka tattara dabbobi suka tafi da su," in ji mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan.

    Ya ƙara da cewa maharan sun fito ne daga "wajen Jangebe", wani yanki na jihar ta Zamfara da ya yi ƙaurin suna kan matsalar tsaro.

    "A halin yanzu muna cikin jeji ne, da idona na ga gawarwaki sun kai 20".

    Ya ce ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙauyuka Sauna, Tudun Namale, Tsangaya, Mashekari da kuma Unguwar Shanu.

    A wani bayani da ta wallafa shafinta na facebook, ƙungiyar Amnesty International ta ce lamarin ya yi sanadin rayuka 24, yayin da mutane da dama suka tsira da munanan raunuka.

    "Wannan na nuni da cewa dabarar da ake amfani da ita wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar Zamfara ba ta aiki", in ji Amnesty.

    Ƙungiyar ta ce ƴan bindiga na kai hare-hare a ƙauyukan Zamfara a duk lokacin da suka ga dama, inda suke sanar da mazauna ƙauyuka a lokacin da za su kawo hari, sannan kuma sukan buƙaci a biya su maƙudan kuɗaɗe.

    Zamfara ta shafe sama da shekara 10 tana fama da matsalar ƴan fashin daji masu kai hare-hare suna kashe mutane da kuma garkuwa da wasu domin neman kudin fansa.

    Matsalar ta kuma shafi sauran jihohin yankin, kamar Katsina, Sokoto, Kebbi Kaduna da kuma Neja a arewa ta tsakiyar ƙasar.

    An yi amannar cewa akwai ƙungiyoyin yan bindiga da dama da suke cin karensu babu babbaka a dazukan da suka haɗa jihohin yankin har zuwa kudu maso yammacin ƙasar.

    A baya-bayan nan an samu lokutan da irin waɗannan mayaƙa ke kai hari a ƙauyuka suna kashe mutane tare da ƙona gidaje da kadarori.

    Hukumomi a ƙasar sun sha nanata cewa suna daukar matakai kan lamarin, amma har yanzu abin ya ci tura.

  7. Mun kai sabbin hare-hare kan sansanonin Amurka a Kuwait - Sojin Iran

    Sashen yaɗa labarai na rundunar juyin juya hali ta Iran ya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa ƙasar ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin sojin Amurka uku a ƙasar Kuwait.

    Bayanin ya ce sansanonin su ne: Sansanin sojin Ali al-Salem da kuma na Arifjan, wadanda aka yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai musu hari a yau.

    Sai kuma sansanin Doha, wanda ya ƙunshi rumbun ajiye makamai da kayan aiki na sojojin Amurka.

  8. An kwashe dare na 12 ana musayar wuta tsakanin Iran da Amurka

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump da jagoran Iran Mojtaba Khamenei

    Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare a kan Iran na dare na 12 a jere. Kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa an ji ƙarar fashewa a kusa da birnin Bushehr.

    Iran ma ta ci gaba da mayar da martani, inda ƙasar Kuwait ta ce garkuwarta ta sararin samaniya ta yi nasarar kakkaɓe wasu jirage marasa matuƙa da ta bayyana a matsayin na abokan gaba.

    Dakarun juyin-juya-hali na Iran sun yi ikirarin cewa wani jirgin dakon ɗanyen mai ya kama da wuta a wani yanki da aka dasa nakiyoyi a kusa da mashigar Hormuz, yayin da wasu jiragen dakon mai biyu suka juya baya.

    Jami’an tsaron Iran sun sake jaddada cewa ba za a bari wani jirgin dakon mai ya ratsa Mashigar ba, ba tare da haɗin kai ko amincewar Iran ba.

  9. Ƙungiyar Houthi mai goyon bayan Iran ta fara kai wa jiragen ruwa hari

    Yahya Saree, mai magana da yawun rundunar sojin ƙungiyar ƴan Houthi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Yahya Saree, mai magana da yawun rundunar sojin ƙungiyar ƴan Houthi

    Ƙungiyar Houthi da ke Yemen, wadda Iran ke mara wa baya, ta ce ta kai hari kan jiragen ruwa na dakon mai na Saudiyya guda biyu a tekun Maliya.

    Dama akwai rahotanni da ke cewa wasu jiragen ruwa na dakon mai na sauya hanya, bayan da mayaƙan Houthi suka gargaɗi jiragen ruwa da su kauce wa tashoshin ruwa na Saudiyya.

    Kamfanin dillancin labarai na hukumar Saudiyya ya tabbatar da cewa harin da aka kai ya samu ɗaya daga cikin jiragen, mai suna Encelia, har gobara ta tashi a cikinsa.

    Saudiyya ta bayyana harin a matsayin saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

    A halin yanzu, akwai ƙarin fargaba cewa matakin da mayakan Houthin ke ɗauka na hana zirga-zirgar jiragen ruwa zai iya haddasa tashin gwauron zabi a farashin man fetur a duniya.

  10. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye a wannan rana ta Alhamis - Tabawa ranar samu- inda muke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu kuma ku yi shiyarin.

    Haka nan za ku iya tofa albarkacin bakinku a shafukanmu na facebook, instagram, X da kuma YouTube.