Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/06/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/06/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

Matan Faransa na zanga-zanga adawa da manufofin jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi

...

Asalin hoton, Getty Images

Dubban mata a Faransa na zanga-zangar nuna adawa da manufofin jam'iyyar masu tsattauran ra'ayi a biranen ƙasar ciki har da Paris.

Jam'iyyar na kan gaba a zaɓen zagayen farko na majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar cikin mako, to sai dai ba lallai ne ta samu rinjaye a majalisar ba.

Masu zanga-zangar na fargabar cewa jam'iyyar ka iya tauye 'yancin mata, ciki har da tsiraru kamar 'yan ci-rani.

To sai dai jam'iyyar ta musanta iƙirarin tauye 'yancin mata da sauran haƙƙoƙinsu.

Jam'iyyar ta bayar da misalai kan alƙawuran da ta ɗauka na ƙarfafa hukunci kan laifukan da suka shafi jinsi.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa mata da dama ne suka zaɓi jam'iyyar a lokacin zaɓukan baya-bayan nan na majalisar tarayar Turai.