Hoton da aka ga ɗan wasan Ingila, Jude Bellingham yana rufe bakinsa yayin da yake magana da Jordan Ayew na Ghana ya jawo cece-kuce.
An kafa wata sabuwar doka a gasar kofin duniya ta 2026, wadda ta ce za a iya bai wa ɗan wasa jan kati idan ya rufe bakinsa yayin da yake magana da abokin hamayya.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ne ya nemi a kafa wannan doka bayan da aka hukunta ɗan wasan Benfica Gianluca Prestianni na dakatar da shi wasa shida daga hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA saboda amfani da kalaman nuna wariya ga dan wasan Real Madrid Vinicius Jr a wani wasan Champions League a watan Fabrairu.
Dan wasan Paraguay Miguel Almiron ya zama na farko da aka bai wa jan kati a gasar kofin duniya a bana, saboda aikata laifin rufa baki a wannan laifi a wasan da suka buga da Turkiyya, inda VAR ta ba da shawarar a kore shi.
To me ya sa ba a bai wa Bellingham jan kati ba, kuma ba a duba VAR ba a wasan da suka tashi 0-0 a Boston?
Dalili ana duba yanayin da aka rufe bakin shi ne muhimmi. Rufe baki gaba ɗaya ba a haramta ba, amma yin hakan yayin rigimar ko cece-kuce ko mayar da kalamai da wani ɗan wasa ne aka haramta.
Kafin gasar, shugaban alkalan FIFA Pierluigi Collina ya bayyana a sarari cewa:
“‘Yan wasa za su iya ci gaba da rufe bakinsu da hannu ko rigarsu idan suna tattaunawa da juna.
Amma idan maganar an yi don bakanta ran abokin hamayya, rufe baki yana nuna akwai wani laifi, kuma hukuncinsa jan kati ne.”
Me yasa jan katin Almiron ya bambanta?
A kusan kowane wasa a wannan gasar, za ka ga ƴan wasa suna magana suna rufe bakinsu — har ma alkalai ma suna yin hakan.
Abu mafi muhimmanci shi ne, babu fadin kalaman wariya ko rikici tsakanin Bellingham da Ayew — kawai suna tattaunawa ne a tsakaninsu, wannan ba laifi bane.
To me ya bambanta da na Almiron?
Yanayin wasan ne ya bambanta:
Dan wasan Paraguay Isidro Pitta ya fadi kasa, yana zargin Ismail Yuksek na Turkiyya ya yi masa keta
Wannan ya jawo hayaniya tsakanin ƴan wasa daga bangarorin biyu. A nan ne Almiron ya rufe bakinsa yayin da yake magana da Mert Muldur.
Ko da yake ba su yi rikicin kai tsaye ba, amma wasan ya shiga yanayi mai zafi da fuskantar kalubale.