Labarai da dumi-dumi, Mun lalata jirgin Amurka maras matuƙi a sararin samaniyar Qeshm - Iran
Dakarun Juyin Juya Halin Iran (IRGC) sun ce sun lalata wani jirgin sama maras matuƙi ƙirar MQ-9 mallakin rundunar sojin Amurka a sararin samaniyar tsibirin Qeshm.
Sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya ce da misalin karfe 10:12 na safiyar yau agogon ƙasar, sun harbo jirgin ne ta amfani da abin da suka kira "sabon tsarin kariyar sararin samaniya na zamani" na rundunar.
Sanarwar ta kuma ce wannan ne jirgin sama maras matuƙi na Amurka na nau'in MQ-9 na 53 da dakarun Iran suka ce sun lalata.