Dalilai 4 da suka sa farashin man fetur ya sake tashi a Najeriya

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Da alamu murna ce ke neman komawa ciki ga ƴan Najeriya.

Man fetur ya kai kusan naira 1,430 a birnin tarayyar ƙasar da wasu jihohi, inda wasu ƴan kasuwa ke danganta tashin farashin da rikicin Gabas ta Tsakiya, musamman halin da ake ciki a Mashigin Hormuz.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa sabon ƙarin farashin ya biyo bayan ƙarin naira 85 da matatar Dangote ta yi kan farashin man fetur da take sayarwa daga matatar, daga naira 1,265 zuwa naira 1,350 kan kowace lita, sakamakon tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Najeriya na cikin ƙasashen da ke da arzikin man fetur. Amma a wasu jihohin rahotanni sun ce farashin itar man fetur ya haura naira 1,500.

To ko me ya sa nan da nan wani ƙaramin sauyi ke sa ƴan ƙasar su ga canji a farashin man fetur idan wani abu ya faru?

1. Farashin kasuwannin duniya

Ɗanyen man Brent, wanda shi ne ma'aunin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, ya tashi daga kusan dala 107.92 zuwa dala 108.21 kan kowace ganga.

NAN ya ruwaito a ranar Lahadi a Abuja cewa wasu gidajen mai sun fara ƙara farashin man fetur daga naira 1,350 zuwa naira 1,395 kan kowace lita, yayin da wasu suka ƙara shi daga naira 1,350 har zuwa naira 1,430.

Farfesa Ahmed Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur a Abuja, ya ce abin da ke sa farashin ya taɓu shi ne idan wani abu ya faru a ƙasar da ake shigowa da ɗanyen mai daga cikinta, wanda hakan ke sa farashin ya ƙaru.

Ya ce ƴan kasuwa suna amfani da wannan damar wajen tsara farashin da zai ba su damar ci gaba da kasuwanci a nan gaba ba tare da yin asara ba. Ya ce yawanci suna amfani ne da farashin kasuwannin duniya, saboda idan ba su yi hakan ba, za su iya yin asara.

"Idan farashin ɗanyen mai ya yi sama, za su ƙara farashi, saboda idan ba su ƙara ba, ba za su iya siyowa ba," in ji shi.

A cewarsa, ƙasashen da ke iya bayar da tallafi ne ba su cika ganin irin wannan sauyi ba, wanda kuma lamarin ba haka yake ba a Najeriya.

"Tun da yanzu babu tallafi, dole ƴan Najeriya su riƙa ganin irin wannan sauyi a kai a kai."

Ya ce musamman yanzu da kasuwar duniya ta zama dunƙulalliya, ƙaramin sauyi na iya sa farashi ya tashi.

2. Bambancin tattalin arziki

Da muka tambayi masanin me ya sa wasu ƙasashen Afirka ba su cika taɓuwa idan aka samu irin wannan sauyi ba, ya ce tun da yanzu Najeriya ba ta biyan tallafin man fetur, dole ƴan ƙasar su fi jin wannan tasirin.

Farfesa Ahmed ya ce wasu ƙasashen suna da tattalin arziki mai ƙarfi fiye da na Najeriya, inda ya ce lamarin ya danganta daga ƙasa zuwa ƙasa.

"Akwai tattalin arzikin ƙasashen da yake da ƙarfi saboda suna fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, wanda ya sa darajar kuɗinsu take haɓaka idan ka kwatanta shi da dala," in ji shi.

Ya ce irin waɗannan ƙasashe, ko da ɗanyen man ya yi tsada, idan aka canza farashin zuwa kuɗin ƙasarsu, ba lallai a samu wani babban sauyi ba.

A Najeriya kuwa, in ji shi, idan ba ta samu isassun kuɗaɗen dalar Amurka ba, babu yadda za ta daidaita farashin, saboda tattalin arzikinta ba shi da ƙarfin da zai daƙile hauhawar farashin.

"Mu a nan Najeriya abu biyu ne suka haɗu, hauhawar farashin man fetur da kuma raguwar darajar naira," in ji Farfesa Ahmed.

3. Rashin darajar Naira

A Najeriya, masanin ya ce rashin darajar naira na sa ko da an samu ƙaramin sauyi, darajar kuɗin ba za ta iya kare martabarta da dala ba, saboda komai da dala ake ƙirga shi a kasuwar duniya, sannan a canza shi zuwa kuɗin ƙasa.

Ya ce darajar naira ba ta kai ƙarfin kuɗin wasu ƙasashe ba.

"Idan muka ce ba za mu sayar da mai a yadda kasuwannin duniya ke sayarwa ba..." Saboda haka, ya ce kuɗin dalar da Najeriya ke samu zai ragu.

Bugu da ƙari, masu saka hannun jari ƴan ƙasashen waje ne, inda suke kashe kuɗi da yawa.

"To idan har ba a daidaita shi ba ta yadda za su iya mayar da kuɗin da suka kashe, to za su janye," in ji shi.

Sannan man da ake samarwa zai yi ƙasa, in ji shi, haka kuma kuɗin ƙasashen waje da ake samu wajen kare darajar naira zai ragu, lamarin da zai iya jefa mutane cikin talauci fiye da yadda ake a yanzu.

4. Rikicin ƙasashen duniya

A baya-bayan nan, rikici a Gabas ta Tsakiya na ƙara tsananta, inda Mashigin Hormuz yake kusan a kulle, sannan kuma akwai batun mayaƙan Houthi da suka kai hare-hare a Saudiyya.

A baya-bayan nan sun ƙwace tashar ruwan Mocha da ke birnin Mocha, inda suka mamaye ta. Hanyar na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su kuma suke da alaƙa da Tekun Maliya.

Wasu na ganin wannan ma na daga cikin tsaikon da zai sa a ga tashin farashin cikin ƙanƙanin lokaci saboda zirga-zirgar ba ta gudana yadda ya kamata.

Farfesa Ahmed Adamu ya ce ba mamaki ba ne ƴan Najeriya su ga farashin man fetur na hawa yana sauka, saboda rashin jituwar da ake samu da kuma rikice-rikicen duniya.

Ya ce idan wani abu na yaƙi, rashin jituwa ko tsamin dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashe ya faru, hakan zai yi tasiri saboda ana iya rufe hanyoyin da ke sauƙaƙa zirga-zirgar.

Shin man fetur zai iya sauƙi a Najeriya?

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin da aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, farashin man fetur ya tashi daga ƙasa da naira 200 zuwa sama da naira 1,000 kan kowace lita, lamarin da ya haifar da ƙarin tsadar sufuri, abinci da sauran abubuwan rayuwa.

A baya dai, man fetur ya fara sauka a Najeriya har zuwa ƙasa da naira 1,200 a ƴan makonnin da suka gabata, lamarin da ya sa wasu suka fara hasashen cewa zai iya komawa ƙasa da naira 1,000 kan kowace lita, kamar yadda yake a farkon shekarar 2026.

A kullum fatan ƴan Najeriya dai shi ne su samun man fetur a ƙasar ya yi sauƙi sosai ta yadda za su saye shi a araha.

Sai dai Farfesa Ahmed Adamu ya ce a irin wannan lokaci ya kamata a daina maganar ya za a yi man fetur ɗin ya yi ƙasa.

Ya ce kamata ya yi a mayar da hankali ne wajen neman mafita ga ƙasar ta yadda ko an samu sauyi ƴan ƙasar ba za su gane ba.

"Ɗanyen man fetur idan ka ce ka ci gaba da dogaro a kanshi, zai ta baka wahala ne kawai. Dole sai an nemo mata wata madafa."

Mece ce mafita?

Farfesa Ahmed ya ce tun lokacin da aka cire tallafin man fetur a Najeriya bai kamata a miƙa wa gwamnoni kuɗi kawai su kashe ba.

A cewarsa kamata ya yi a karkatar da kuɗin wajen samar da makamashi da ci gaban ƙasa da wasu hanyoyin sufuri.

"Idan muka ce sai ya yi arha, can wani wuri zai ɓalle. Idan kuma muka barshi a haka ƴan ƙasa za su ci gaba da kuka," in ji shi.

Saboda haka ya ce kasuwa ce dole sai an barta ta yi halinta, kamata ya yi a kawo mata kishiya ta yadda ko da man fetur ya yi tsada, yan Najeriya ba za su sani ba.