Tinubu ya tafi hutun mako uku

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja domin fara hutun mako uku a Turai a matsayin wani ɓangare na hutunsa na shekara-shekara.
Sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar ta ce shugaban zai fara ziyartar birnin London na Birtaniya kafin ya ci gaba da hutun nasa.
A cewar mai bai wa shugaban shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, hutun zai kasance ne a matsayin hutun aiki, inda shugaban zai ci gaba da gudanar da wasu ayyukan gwamnati yayin da yake wajen ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala hutun domin shiga zafafan shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairun 2027.




















