KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na 21/05/2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman MINJIBIR

  1. Tinubu ya nada ɗan shekara 39 a matsayin shugaban JAMB

    ..

    Asalin hoton, Onanuga/X

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar da ke tsara jarrabawar shiga jami'a, JAMB.

    Aina wanda shekarunsa 39 ya maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede wanda wa'adinsa ke ƙarewa ranar 31 ga watan Yulin 2026.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya bayyana Aina a matsayin fitaccen masanin kuma ƙwararre da yake da gogayya a harkokin jarrabawa da intanet da kuma sauye-sauye a abubuwan da suka shafi al'umma.

  2. Ƙungiyar agaji ta zargi sojojin Isra'ila da azabtarwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƙungiyar ba da agaji ta Falasdinawa ta ce masu fafutuka da aka tsare daga wani jerin gwanon jiragen ruwan Gaza sun zargi sojojin Isra'ila da cin zarafi da kuma azabtarwa.

    An kai mutum uku daga cikinsu asibiti, ko da yake a halin yaznu an sallame su. Tun da farko dai Ministan Tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir ya sha suka bayan ya fitar da wani bidiyo inda ya ke yi wa masu fafutukar izgili yayin da ake tsare da su.

    Bidiyo ne na tsawon dakika talatin da takwas da ya nuna jerin wadanda aka tsare suna zaune a kasa a daure yayin da Ben Gvir ya ke musu dariya yana cewa maraba da zuwa Isra'ila mu ne masu iko a nan.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce abin da ministan aikata ya ci karo da dabi'un isra'ila.

  3. Al'ummar Diffa a Nijar na fuskantar barazanar ƙarancin abinci

    ..

    Asalin hoton, ORTN

    Manoma a jahar Diffa da ke jamhuriyar Nijar sun koka kan fuskantar wasu matsaloli guda da ke barazana ga samar da abinci a yankin.

    Manyan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya sun haɗa da rashin tsaro da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, da sauyin yanayi, da hare-haren da kwari ke kai wa muhimman amfanin gona, lamarin da ya haifar da karancin albarkatun noma a kasuwanni.

    Tuni dai manoman suka koka da matsalar suna masu cewa lamarin ya jefa su cikin halin ha'u'la'i.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da damuna ke ƙara ƙaratowa sannan kuma ake ta gyare-gyaren gonaki.

  4. Ana cece-kuce tsakanin Atiku da Amaechi kan takarar shugaban ƙasa a ADC

    ..

    Asalin hoton, bbc collage

    A Najeriya takaddama ta kaure tsakanin manyan masu neman takarar shugabancin kasar a jama'iyyar ADC Rotimi Amaechi da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar.

    An dai jiyo wasu kalamai daga bakin Amaechin, inda ya ce Atiku Abubakar ba mutum ne da zai iya lashe zaɓe ba, ko da kuwa ya samu takara a jama'iyyar.

    Amaechi ya kafa hujja da zaɓukan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya tsaya a baya, kuma ya sha kaye, yana mai cewa a yanzu kamata ya yi jam’iyyarsu ta mayar da hankali ga wanda jama’a za su iya zaɓa, ba wanda ya saɓa takara ba.

    Sai dai kuma ɓangaren Atiku sun ce Kalaman na Amaechi na "tsoro ne" saboda sun san cewa Atiku ya fi ƙarfinsu sannan zai fi samun karɓuwa daga yan Najeriya.

    Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya, Atiku Abubakar dai ya yi takarar shugaban ƙasa karo na huɗu kuma idan ya samu takarar a 2027, hakan zai kasance takararsa ta biyar kenan.

  5. Ƴan Ghana da ke Afirka ta Kudu za su koma gida

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Alhamis ɗin nan ne wata tawagar 'yan ci-rani 'yan asalin ƙasar Ghana da ke Afirka ta Kudu za su koma ƙasarsu.

    Suna tserewa ne daga zanga-zangar ƙin jinin baƙi a biranen Afirka ta Kudu, inda masu zanga-zangar ke zargin baƙi da asassa matsalar tabarbarewar tattalin arziki

    Gwamnatin Ghana dai ta ce yan kasarta guda dari uku ne da ke Afrika ta kudu suka mika bukatar komawa gida, masu zanga-zangar suna zargin bakin haure ne da ta'azzara matsalar karancin albashi da rashin aikin yi.

    Najeriya ma ta ce sama da ƴan kasarta 100 ne suka nemi a mayar da su gida. A na ta bangaren Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da duk wani cin zarafi da ake kai wa ƴan kasashen waje.

  6. Shugaban Cuba ya yi watsi da tuhumar da Amurka ta yi wa Raul Castro

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tsohon shugaban Cuba Raul Castro lokacin da yake bayani a Majalisar Dokoin ƙasar bayan da Diaz-Canel ya ci zaɓe a 2018 a Havana

    Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya yi watsi da tuhumar da Amurka ta yi wa magabacinsa Raul Castro a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.

    Zarge-zargen da a ke yi wa tsohon shugaban na Cuba mai shekara 94 sun samo asali ne daga wani lamari da ya faru a shekarar 1996 inda jiragen yakin Cuban suka harbo jiragen sama guda biyu da wata kungiyar yan sa kai ta 'yan gudun hijirar Cuban ke amfani da su.

    Ana tuhumar Raul Castro da laifuffuka hudu na kisan kai, amma manazarta sun ce wani yunkuri ne na Washington na tabbatar da sauyin gwamnati a Havana.

    Takunkuman da Amurka ta kakabawa tsibirin ya durkusar da tattalin arzikinsa baki daya.

    Shugaba Trump ya bayyana tuhumar a matsayin lamari mai cike da tarihi amma ya yi watsi da yiwuwar daukar matakin soji

  7. Ana samun hauhawar hannun jari a Asia saboda tsagaita yakin Iran

    An sami hauhawar darajar hannun jari a kasuwannin Asiya, sakamakon bunƙasar kamfanonin fasaha da fatan da ake da shi cewa nan ba da jimawa ba za a warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Kasuwar Nikkei ta Japan ta tashi da sama da kashi uku cikin ɗari, yayin da hannayen jarin kamfanonin Koriya ta Kudu suka tashi da kusan kashi biyar cikin ɗari.

    Muhimmin cigaban da aka samu a kamfanin kera-keren fasaha na Amurka , (Nvidia), da shawarar da ma'aikatan Samsung suka yanke na kin shiga yajin aiki, da shirin da ake yi na sayar da hannayen jari a kamfanonin SpaceX da OpenAI sun taimaka wurin bunkasa darajar hannayen jarin kamfanonin fasaha.

  8. Muna ƙoƙarin samun maganin cutar Ebola - Jami'in Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami'in ma'aikatar lafiya ta Amurka ya ce wata hukumar gwamnati tana aiki tare da wani ƙaramin kamfanin sarrafa magunguna don sarrafa wani maganin gwaji na cutar Ebola.

    Asali dai an kirkiri maganin ne domin yaki da wani na'uin cutar amma bayan gwaje-gwaje sun nuna cewa zai iya yin tasiri a kan nau'in Bundibugyo wanda a halin yanzu ake fama da shi a gabashin Kongo.

    Wani jami'in hukumar lafiya ta duniya, ya ce ana kuma nazari kan wata allurar rigakafi ta daban.

    Ya ce "Wancan wani aikin hadin gwiwa ne tsakanin jami'ar Oxford da cibiyar sarrafa maguguna ta India, kuma ana kan sarrfata a halin yanzu amma babu isasun bayanai a kan tasirinta".

    Sama da mutane 130 ne ake tunanin cutar ta kashe a gabashin Kongo, inda ake zargin mutane 600 sun kamu da cutar a lardin Ituri mai iyaka da Uganda da Sudan ta Kudu.

  9. Kamfanin SpaceX na Elon Musk na son tallata hajarsa a kasuwar Nasdaq

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin SpaceX na Elon Musk ya gabatar da takarda a hukumance a gaban masu kula da harkokin kuɗi na Amurka don neman izinin tallata hannun jarinsa a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nasdaq.

    Yana daya daga cikin tallar hannun jari da ya fi jan hankali a tarihi, kuma kamfanin yana shirin zama kamfani na farko da zai fara kasuwancin hannun jari da darajar dala trillian ɗaya.

    Wakiliyar BBC ta ce Ko da bayan siyar da hannayen jarin, ana sa ran Elon Musk zai ci gaba da kasancewa mai cikakken iko, har yanzu dai kamfanin bai bayyana adadin hannun jarin da yake shirin sayarwa ba da kuma a kan wani farashi.

    Takardun da kamfanin ya gabatar sun tabbatar da cewa SpaceX yanzu ya kunshi kamfanin kirkirarriyar basira na Elon Musk (XAI), da kuma dandalin sada zumunta na X wanda a baya aka sani da Twitter

  10. Iran ta ce tana yin duban tsanaki kan sabbin buƙatun Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce tana nazari kan sabbin shawarwarin da Amurka ta gabatar kan kawo ƙarshen yaƙin da take da Iran ɗin.

    Ana tunanin Pakistan ce ta gabatar da sabon daftarin ga shugabancin Iran, bayan ministan harkokin wajenta ya ziyarci Tehran a jiya Laraba.

    Shugaba Trump ya ce zai jira na kwanaki domin samun martanin Iran, amma ya sake yin barazanar ɗaukar matakin soji idan har Iran ba ta amince da daftarin ba.

    Tehran ta ɗauki wani mataki na ƙara tabbatar da ikonta a mashigar Hormuz inda ta buƙaci jiragen ruwa su yi aiki tare da wata sabuwar hukumar kula da mashigar da aka ƙirƙira.

  11. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da safiya da fatan kun wayi gari lafiya. Yau Alhamis, kuma kamar kowace rana mun dawo domin ci gaba a inda muka tsaya a shafinmu na kai tsaye da ke kawo muku wainar da ake toyawa dangane da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran.

    Har wayau, shafin yana kuma kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.