KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 10 - 16 Agusta 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku Labaran wasannin BBC Hausa na 10 - 16 Agusta 2026

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Sai da na amince na maye gurbin Sir Alex a Man United - Mourinho

    w

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan shekaru da dama na jita-jita, Jose Mourinho ya tabbatar da cewa ya amince ya maye gurbin Sir Alex Ferguson a Manchester United, kafin daga bisani ya sauya ra’ayi ya koma Chelsea.

    Lokacin da Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013 bayan shekaru 26 a Old Trafford, ya ba da shawarar a naɗa David Moyes, wanda a lokacin shi ne kocin Everton, a matsayin magajinsa.

    Wannan ne ya sa aka yi wa Moyes lakabi da “The Chosen One” wanda aka Zaɓa, har ma an rataye wani babban allo mai ɗauke da wannan suna a bangaren Stretford End na filin wasan kulob din.

    Da yake magana a cikin wani sabon shirin tarihin rayuwarsa da za a fara nunawa a Netflix daga 11 ga Agusta, Mourinho ya ce:“Lokacin da na bar Real Madrid, na amince da zuwa Manchester United domin maye gurbin Sir Alex.”

    Ferguson, wanda ya lashe Premier League 13 a matsayin kocin United, ya tabbatar da cewa an miƙa wa Mourinho aikin.

    Ya ce: “Na zaunar da shi na yi masa bayanin halin da ake ciki. A ganina, ya amince da karɓi aikin. Amma cikin sa’o’i kaɗan komai ya sauya.”

    Abin da ya sauya kuwa shi ne Mourinho ya ji cewa ba zai komawa Chelsea ba da aiki, inda a nan ne ya taba lashe kofunan Premier League a jere a shekarun 2005 da 2006.

    Ferguson ya ƙara da cewa: “A wani dare ya kira ni yana kuka, sai ya ce, ‘Alex, ba zan iya karɓar aikin nan ba. Na riga na yi wa Chelsea alkawari kuma ba zan karya alkawarina ba.’

    “Dalilin da ya ba ni na fahimta, amma duk da haka na ji ba dadi.”

    Mourinho, mai shekaru 63, ya ce ya ji matuƙar karramawa da aka ba shi damar maye gurbin Ferguson saboda: “Manchester United ƙungiya ce mai matuƙar jan hankali.”

    “Rashin damar zama kocin da zai gaji Sir Alex Ferguson abu ne mai raɗaɗi a gare ni, amma ban taɓa nadama ba domin shawara ce da na yanke a zuciyata.”

    Bayan komawarsa Stamford Bridge a shekarar 2013, Mourinho ya lashe kofina uku na Premier League tare da Kofin League Cup.

    A gefe guda kuma, an sallami David Moyes daga aikin bayan watanni goma kacal a matsayin kocin Manchester United.

    Daga baya, Mourinho ya samu wata dama ta biyu ta jagorantar United a shekarar 2016, inda ya maye gurbin Louis van Gaal.

    A tsawon shekaru biyu da rabi da ya yi a Old Trafford, Mourinho ya lashe League Cup da Europa League kafin a kore shi a watan Disamban 2018 biyo koma bayan sakamako da ƙungiyar ta samu.

  2. Bruno Guimarães ya kammala komawa Arsenal

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ,

    Ko shakka babu, mafi girman cinikin sauya kungiya da aka yi a ƙarshen makon nan shi ne Arsenal da ta ɗauki Bruno Guimarães daga Newcastle kan kuɗi fam miliyan 75.

    Dan wasan tsakiya na Brazil mai shekaru 28 ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru huɗu, tare da zaɓin ƙarin shekara guda, kuma ya bayyana wannan sauyin ƙungiya a matsayin ɗaya daga cikin “mafi wahalar hukunci” da ya taɓa yankewa a rayuwarsa.

    Guimarães ya koma Newcastle ne a watan Janairun 2022 lokacin da ƙungiyar ke fuskantar barazanar faduwa daga gasar Firimiya.

    Ya zama kyaftin na farko na Newcastle cikin shekaru saba’in da ya ɗaga wani babban kofin cikin gida, bayan da suka doke Liverpool a wasan ƙarshe na Kofin Carabao na shekarar 2025.

  3. Barkanmu da rana

    Masu bibiya barkanmu da wannan lokaci Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan kasancewa da ku a wannan makon domin kawo labarai da rahotannin wasanni daga nan BBC.

    Sai ku kasance da mu.