DR Congo da M23 sun amince da tsagaita wuta don ci gaba da tattaunawar zaman lafiya

Asalin hoton, Reuters
Tattaunawar zaman lafiya tsakanin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) da ƙungiyar ’yan tawaye ta AFC/M23 ta samu ɗan ci gaba, amma har yanzu akwai wasu batutuwan da ba a cimma matsaya a kansu ba.
A cewar wata sanarwar haɗin gwiwa, ɓangarorin biyu sun amince da wata sabuwar yarjejeniya ta tattaunawa da nufin kawo ƙarshen rikicin, yayin da faɗa ke ci gaba a gabashin DR Congo.
An cimma wannan matsayar ce bayan kwana biyar na tattaunawa a Switzerland, kuma ta ƙunshi matakai da lokutan da za a bi wajen ci gaba da tattaunawar, ƙarƙashin yarjejeniyar tsarin zaman lafiya da aka sanya hannu a Doha, Qatar, a bara.
An gudanar da sabon zagayen tattaunawar a Switzerland daga 17 zuwa 21 ga Agusta, tare da taimakon Qatar, Amurka, Togo a madadin Tarayyar Afirka, Switzerland da Hukumar Tarayyar Afirka.
Bangarorin biyu sun amince da fara aiki da tsarin Expanded Joint Verification Mechanism Plus (EJVM+), wani tsarin da aka ƙirƙira domin sa ido kan take dokokin tsagaita wuta.
An riga an kafa sakatariyar tsarin, kuma ana sa ran gudanar da aikin tabbatarwa na farko ranar Litinin a Minembwe, wani yanki na Kudancin Kivu da ya sha fama da yaƙe-yaƙe.
Sai dai har yanzu akwai rashin jituwa kan wasu batutuwa, ciki har da takunkuman da aka kakaba wa M23, sakin waɗanda ake tsare da su, da kuma lokacin aiwatar da sauye-sauyen siyasa.
Haka kuma, faɗa ya ci gaba a Arewa da Kudancin Kivu, duk da alkawuran tsagaita wuta da aka yi sau da dama. Gwamnatin Kongo da M23 suna zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar.























