KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 26 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. An kama ɗan ƙasar Thailand a Afirka ta Kudu yana ƙoƙarin safarar ƙwai aku 50

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama wani ɗan ƙasar Thailand a Afirka ta Kudu, yana ƙoƙarin safarar ƙwai 50 da ake zargin na wani nau'in aku ne da ke fuskantar barazanar bacewa, ta filin jirgin saman Johannesburg.

    Ma'aikatar Muhalli ta Afirka ta Kudu ta ce jami'an kwastam sun gano ƙwayayen a ɓoye cikin wata jaka da aka ƙera a matsayin na'urar dumama ƙwai, wadda mutumin ke ɗauke da ita a matsayin jakar hannu a cikin jirgi.

    Kamen ya biyo bayan wani makamancinsa da ya faru a filin jirgin a watan da ya gabata, lokacin da aka kama wani ɗan ƙasar Thailand ɗin da sama da ƙwai 400 na aku.

  2. Akalla mutane 160 sun mutu a mummunar ambaliyar Nepal

    Akalla mutane 160 ne suka mutu bayan wata mummunar ambaliyar ruwa ta afka wa yankunan arewacin Nepal da Tibet, kusa da iyakar kasashen biyu.

    Hukumomin Nepal sun ce mutane 157 sun mutu, yayin da China ta tabbatar da mutuwar wasu uku a yankin Tibet.

    Daruruwan mutane kuma ba a san inda suke ba, ciki har da 'yan kasashen waje da dama da ke ziyartar yankin domin yawon bude ido ko aikin hajji.

    Akwai yiwuwar wata babbar ambaliyar kankara da duwatsu daga tsauni ce ta haddasa ambaliyar, lamarin da ya sa ruwan kogin Bhote Koshi ya yi tashin gwauron zabi cikin kankanin lokaci.

    Ambaliyar ta shafe gidaje da kauyuka, tare da lalata hanyoyi, gadoji da wasu cibiyoyin samar da wutar lantarki.

    Hukumomi sun ce akalla gadoji 19 sun lalace ko kuma ruwa ya kwashe su.

  3. ADC ta buƙaci a kama shugaban ƙaramar hukumar Kuje

    Samuel Danjuma Shekwolo

    Asalin hoton, Kaura Peter Daudu/FB

    Jam'iyyar ADC a Najeriya, ta bukaci a kama shugaban karamar hukumar Kuje, Samuel Danjuma Shekwolo, bisa zargin yin barazanar korar mazauna yankin da suka ƙi zaɓar jam'iyyar APC.

    Jam'iyyar adawar ta ce kalaman shugaban na barazanar tilasta wa mutane barin gidajensu, tana mai cewa hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

    A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ji Mista Shekwolo yana cewa: “Na faɗa a karamar hukumata, ko dai ka yi APC ko kuma ka bar karamar hukumar. Ba na gardama da ku.”

    A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ADC, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya danganta kalaman da irin wanda Sanata Francis Fadahunsi na APC ya fada yayin zaɓen gwamnan Osun, inda aka zarge shi da yi wa masu zaɓen jam'iyyun adawa barazana.

    ADC ta ce kalaman shugaban karamar hukumar Kuje, wanda aka ɗora wa alhakin kare lafiyar mazauna yankin, barazana ce ta tilasta wa mutane tserewa daga yankin.

    ADC ta bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya da Hukumar DSS da su kama Mista Shekwolo tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

    Jam'iyyar ta ce bai kamata a gayyace shi kawai domin tattaunawa ba sannan a sake shi, tana mai cewa ya kamata a kama shi, a gurfanar da shi, sannan kotu ta yanke hukunci.

  4. Ranar Hausa: Maʼaikatan BBC sun faɗi kalaman gagara-gwari da suka sani

    Bayanan bidiyo, Waɗanne gagara-gwari kuka sani a Hausa?

    Albarkacin Ranar Hausa ta Duniya, maʼaikatan Sashen Hausa na BBC sun faɗi kalaman gagara-gwari da suka sani.

  5. Ba na tunanin jagoran Iran ya mutu; amma ya samu munanan raunuka - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai da tabbacin cewa jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya mutu amma ya ce ya samu munanan raunuka.

    Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wani mai gabatar da shirye-shirye na Amurka, Glenn Beck.

    Ya ce: “Ba na tunanin ya mutu. Ya samu mummunan rauni. Bangaren hagu na jikinsa, hannunsa, kafarsa, komai. Ya samu mummunan rauni, amma ba na tunanin ya mutu.”

    Ba a ga Mojtaba Khamenei a bainar jama'a ba tun bayan da ya karbi ragamar jagorancin Iran, sakamakon kisan mahaifinsa a watan Fabrairu.

    Sai dai aA hukumance, Mojtaba Khamenei na ci gaba da jagorantar Iran yayin da Amurka da Isra'ila ke kai hare-hare kan kasar.

    Trump ya sha bayyana cewa Amurka na samun nasara kan Iran.

    Sai dai har yanzu Amurka ba ta yi nasarar tilasta wa Iran bude mashigar tekun Hormuz ko mika kayayyakin nukiliyarta ba.

  6. Japan ta goyi bayan gina bututun mai da za su kauce wa mashigar Hormuz

    Japan

    Asalin hoton, Getty Images

    Japan ta sanar da goyon baya ga ayyukan gina bututun mai a Gabas ta Tsakiya da za su ba da damar fitar da ɗanyen mai ba tare da wucewa ta mashigar ruwan Hormuz ba, a wani ɓangare na sabon shirinta na ƙarfafa tsaron makamashi.

    Shirin ya kuma haɗa da nemo wasu hanyoyin shigo da mai daga wurare daban-daban bayan rikicin Iran da hare-haren Amurka da Isra’ila sun nuna irin haɗarin da ke tattare da dogaro da mashigar Hormuz.

    A shekarar 2025, kusan kashi 94 cikin 100 na ɗanyen man da Japan ke shigowa da shi ya fito ne daga Gabas ta Tsakiya, yayin da kashi 93 cikin 100 ke ratsawa ta mashigar.

    Japan na shirin tallafa wa kamfanoninta wajen biyan ƙarin kuɗin jigilar mai daga wasu hanyoyi da kuma goyon bayan ayyukan gina sabbin bututun mai.

  7. Harin Ukraine ya lalata rumbun ajiyar kamfanin sayar da kayayyaki mafi girma a Rasha

    Hukumomi a Rasha sun ce wani harin jirgin sama marar matuƙi na Ukraine ya lalata wani rumbun ajiya na kamfanin sayar da kayayyaki ta intanet mafi girma a Rasha, Wildberries.

    Gwamnan yankin Tambov, ya ce mutane biyu sun jikkata a harin, wanda ya haddasa wata gagarumar gobara a wurin ajiyar kayayyakin.

    Tun daga watan da ya gabata Ukraine ke kai hare-hare kan cibiyoyin Wildberries.

    A gefe guda kuma, rahotanni sun bayyana cewa hare-haren Rasha a birnin Cherni-hiv, da ke arewacin Kyiv, sun kashe wata mata da ƙaramin yaro.

  8. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 22, ɗaruruwan sun ɓace a Nepal

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 22 ne suka mutu, yayin da ɗaruruwa suka ɓace sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afka wa arewacin Nepal, ciki har da kusan masu yawon buɗe ido 300 ‘yan ƙasashen waje.

    Ministan harkokin wajen Nepal ya ce ana kyautata zaton wata girgizar ƙasa da ta afku da safiyar ranar ne wadda ta haddasa rushewar ƙanƙara a wani kogi da ke kusa da iyakar ƙasar da Tibet ta janyo ambaliyar.

    Ambaliyar ta share wasu ƙauyuka baki ɗaya tare da lalata tituna, gadoji da tashoshin samar da wutar lantarki, lamarin da ya haddasa gagarumar asara a yankin.

  9. Gwamnati ta umarci a sake duba kwangilolin hanyoyi kan cunkoson Benin-Asaba

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta umarci a sake duba yarjejeniyoyin bai wa kamfanoni kula da manyan hanyoyi bayan mummunanr cunkoson da ta addabi hanyar Benin zuwa Asaba a baya-bayan nan.

    Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana hakan bayan ziyarar duba hanyar, inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda kamfanin da aka ba aikin ke tafiyar da shi.

    Ya ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki kan duk wani kamfani da ayyukansa ke jefa masu amfani da hanyoyi cikin wahala.

    Umahi ya kuma ba da haƙuri ga matafiya da suka maƙale a hanyar na tsawon lokaci, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci ma'aikatar da ta ɗauki matakan gaggawa domin gyara hanyar da dawo da zirga-zirga yadda ya kamata.

  10. Diphtheria ta kashe yara 50 a Kano

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla yara 50 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar mashaƙo wato diphtheria a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, a cewar jami'ai.

    Mahukunta a jihar sun ce cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi shida, lamarin da ya ƙara haddasa damuwa kan lafiyar al'umma.

    Sun buƙaci hukumomin yankunan da abin ya shafa su tura ƙarin ma'aikatan lafiya tare da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaɗuwar cutar, musamman a wuraren da ke da haɗari.

    Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ƙwayoyin cuta ke haifarwa, kuma tana iya jawo mummunar rashin lafiya har ma da mutuwa, musamman ga yaran da ba su samu rigakafi ba.

  11. Makomar siyasata - Danjuma Goje

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Tsohon gwamnan jihar Gombe, Muhammad Ɗanjuma Goje ya ce ya ce ya ɗauki rashin samun takarar sanata a APC a matsayin ƙaddarar rayuwa. Sanata Goje ya kuma yi iƙirarin cewa Gwamna Inuwa Yahaya bai isa ya yi masa ritaya daga siyasa ba.

  12. Shugabannin Afirka sun nemi ƙarin kuɗaɗe domin yaƙi da cutar Ebola

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Dr. Jean Kaseya, tare da shugabannin ƙasashen Burundi, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya da Uganda, sun yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙara tallafin kuɗi domin daƙile yaɗuwar cutar Ebola.

    A wata maƙala da suka wallafa tare, shugabannin sun ce ya kamata gudunmawar kuɗaɗe ta yi daidai da saurin yaɗuwar cutar, wadda ta kashe fiye da mutum 2,600 tare da kama sama da mutum 5,500 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

    Sun ce jinkirin samar da kuɗaɗe na iya hana kai magani da kayan kariya ga masu aikin lafiya.

    Sun kuma buƙaci masu ba da tallafi su cika alƙawuran da suka ɗauka, waɗanda adadinsu ya kai kusan dala biliyan 1.3, domin ƙarfafa matakan da ake ɗauka na yaƙi da cutar.

  13. Me ya sa Atiku ya dage kan mayar da tallafin man fetur a Najeriya?

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB

    Bayanan hoto, Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar

    Batun cire tallafin man fetur na ci gaba da haifar da muhawara a Najeriya gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.

    Babban ɗan takara na hamayya, Atiku Abubakar ne ya tayar da ƙurar lokacin da ya sanar cewa zai mayar da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen ƙasar na 2027.

    Kalaman na tsohon mataimakin shugaban ƙasar a makon da ya gabata sun ƙara zafafa siyasar ƙasar, lamarin da ya kai ga shugaban Najeriya Bola Tinubu da kansa ya fito ya soki lamirin kalaman na Atiku.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  14. Rikici a Sudan ya kashe mutum 27 ciki har da yara huɗu

    Aƙalla mutum 27 ne suka mutu, ciki har da yara huɗu, sakamakon sabon rikici da ya auku a jihar Kordofan ta Kudu da ke Sudan.

    Rahotanni sun ce hare-haren sun faru ne a yankunan Qardud da Abu Hamama, inda al'ummar Otoro ke zaune, yayin da wasu mata suka jikkata.

    Ƙungiyar likitocin Sudan ta zargi ƙungiyar 'yan tawayen SPLM-N ƙarƙashin jagorancin Abdel Aziz al-Hilu da kai hare-haren, tana mai cewa an kai wa fararen hula harin ne a yayin da rikici tsakanin ƙungiyar da al'ummar Otoro ke ƙara kamari.

    Ƙungiyar ta ce hare-haren sun haddasa ƙaura mai yawa zuwa yankunan Abu Hitan da Kadugli.

    Ta kuma yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hari kan fararen hula bisa bambancin ƙabila na iya rikiɗewa zuwa wani babban rikicin ƙabilanci, tana mai bayyana hare-haren kan mata da yara marasa makami a matsayin karya dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa.

  15. Iran ta ce har yanzu ba a yanke hukunci kan zaɓen ƙananan hukumomin ƙasar ba

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Ministan harkokin cikin gida na Iran, Eskandar Momeni, ya ce gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da na birane zai dogara ne da amincewar majalisar ƙoli ta tsaron ƙasa.

    Ya bayyana cewa tun da majalisar ce ta yanke shawarar ɗage zaɓen a baya, ita ce za ta sake yanke hukunci kan lokacin gudanar da shi.

    An shirya gudanar da zaɓen ne a ranar 1 ga watan Mayu, amma aka ɗage shi saboda damuwa cewa yanayin zaɓen na iya haifar da rarrabuwar kawuna da saɓani a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale.

    Matakin ɗage zaɓen ya fuskanci suka daga wasu 'yan siyasa da tsoffin jami'ai.

    Shugaban Hukumar Sa-ido kan zaɓen majalisun ya ce an miƙa shawarar gudanar da zaɓen a ranar 14 ga Oktoba ga majalisar ƙolin domin ta yanke hukunci na ƙarshe.

  16. Ba za a iya cimma yarjejeniyar diflomasiyya da Iran ba - Netanyahu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ba ya ganin za a iya cimma yarjejeniyar diflomasiyya da shugabannin Iran, yana mai cewa yana da shakku kan yiwuwar sasanta saɓanin da ke tsakanin Tehran da ƙasashen Yamma ta hanyar tattaunawa.

    Netanyahu ya faɗi hakan ne bayan ganawarsa da shugaban Amurka Donald Trump, inda ya ce sun tattauna yiwuwar samar da mafita ta diflomasiyya game da Iran.

    Sai dai ya jaddada cewa zai yi wahala a kai ga wata yarjejeniya da shugabannin Iran ta hanayr diflomasiyya.

    Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da yunƙurin diflomasiyya daga masu shiga tsakani, ciki har da Pakistan, domin rage zaman ɗar-ɗar da ke tsakanin Iran da Amurka da kuma nemo hanyar warware taƙaddamar ta hanyar tattaunawa.

  17. Hausawa na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kai da ci gaban Najeriya - Tinubu

    ....

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce Hausawa na taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kai da ci gaban Najeriya, tare da yaba wa gudunmawar da al'ummar ke bayarwa wajen bunƙasa ƙasar.

    Tinubu ya faɗi hakan ne yayin da yake taya al'ummar Hausawa murnar ranar Hausa, wadda ake gudanarwa a masauratar Daura mai tarihi, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    Ya ce harshen Hausa ya bunƙasa sosai, kuma ya zama wani muhimmin harshen sadarwa da kasuwanci a sassa daban-daban na duniya.

    Shugaban ya kuma taya ɗaukacin al'ummar Hausawa murna, yana mai yi musu fatan alheri yayin bikin ranar Hausa.

  18. Ƙarin ƴan Najeriya 65 za su koma gida daga Afirka ta Kudu a yau Laraba

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta ce wasu ƙarin ƴan ƙasar 65 ne za su koma gida daga Afirka ta Kudu a yau Laraba, inda ake sa ran za su tashi daga filin jirgin OR Tambo da ke Johannesburg zuwa Legas.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa wasu mutane masu zaman kansu ne suka ɗauki nauyin tafiyar, kuma ana sa ran jirgin zai tashi da misalin ƙarfe 3:30 na rana agogon Afirka ta Kudu, sannan ya isa filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas da yamma.

    Matakin na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da nuna damuwa ƙyamar baƙi da hare-haren da ake kai musu da kuma tashin hankali da aka haifar musu a Afirka ta Kudu.

    A baya, gwamnatin Najeriya ta kwashe fiye da ƴan ƙasar 1,400 daga Afrika ta Kudu a lokutan da aka samu irin waɗannan rikice-rikice.

  19. Gobara ta hallaka jarirai 15 a asibiti a Pakistan

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla jarirai 15 ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a wani asibiti da ke birnin Islamabad na Pakistan, inda ɗaya kacal daga cikin jariran da ke sashen kula da jarirai aka samu nasarar cetowa da ransa.

    Rahotannin kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ce gobarar ta tashi ne bayan na'urar sanyaya ɗaki ta fashe a sashen kula da mata masu juna biyu na Cibiyar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Pakistan (PIMS).

    Gobarar ta bazu zuwa sashen jarirai, lamarin da ya haddasa asarar rayuka masu yawa.

    Jami'ai sun ce an kashe gobarar, kuma jami'an agajin gaggawa na ci gaba da aikin sanyaya wurin da kuma tantance irin ɓarnar da gobarar ta yi.

    Hukumomi sun kuma fara bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

  20. Wace ce Dolly Parton, fitacciyar mawaƙiyar Amurka da ta rasu?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitacciyar mawaƙiya, jaruma kuma marubuciyar waƙoƙi ta Amurka, Dolly Parton, ta rasu tana da shekara 80 a duniya.

    An haifi Dolly Rebecca Parton a ranar 19 ga Janairun 1946 a jihar Tennessee ta Amurka, inda ta taso cikin iyali mai yara 12.

    Tun tana ƙarama ta fara rubuta waƙoƙi kuma ta shiga harkar kiɗa, lamarin da ya sa daga baya ta zama ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan waƙoƙin country a tarihin Amurka.

    Dolly Parton ta yi fice da waƙoƙi irin su Jolene, I Will Always Love You da kuma 9 to 5, waɗanda suka samu karɓuwa a faɗin duniya.

    Baya ga harkar waƙa, ta yi fice a fina-finai da dama, sannan ta kafa cibiyar nishaɗi ta Dollywood da kuma shirin Imagination Library, wanda ke raba littattafai kyauta ga yara domin ƙarfafa karatu.

    A tsawon aikinta, ta lashe lambobin yabo da dama ciki har da Grammy, kuma ta sayar da sama da kwafi miliyan 100 na ƙundin waƙoƙinta.

    Mutuwar Dolly Parton ta jawo alhini daga magoya bayanta da masu sha'awar kiɗa a duniya, inda ake yi mata kallon ɗaya daga cikin fitattun mata da suka canza fagen waƙoƙin country.

    Ba saboda nasarorin da ta samu a harkar nishaɗi kaɗai aka santa ba, har ma saboda ayyukan jin ƙai da tallafin da ta riƙa bayarwa ga yara da al'ummomi masu buƙata.