Dangote na shirin gina katafariyar matatar mai a gabashin Afirka

Asalin hoton, Aliko Dangote
Hamshaƙin attajirin nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya bayyana shirin gina katafariyar matatar man fetur da za ta iya tace ganga 650,000 a kowace rana a gabashin Afirka.
Yayin da yake jawabi a wani babban taron masu ruwa da tsaki kan masana'antun Afirka, da ke gudana a birnin Nairobin Kenya, Dangote ya ce shirin wani mataki ne na bunƙasa masana'antu a nahiyar.
Taron - wanda manyan shugabannin Afirka da masu zuba jari da masu ruwa da tsaki kan harkar masana'antu suka halarta - an shirya shi ne domin magance matsalolin makamashi a nahiyar.
Dangote ya ce lokaci ya yi da Afirka za ta inganta masana'antunta an cikin gida, tare da rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙetare.
“Muna fitar da ma'adinai ba tare da mun sarrafa su ba, abin da hakan ke nufi shi ne idan kana fitar da ma'adinanka kana asarar ayyuka ne, kuma idan kana shigo da abubuwa, tamkar kana shigo da talauci ne zuwa ƙasarka'', in ji Dangote
Ya jaddada cewa bunƙasa masana'antu, musamman na tace mai da samar da taki da sauran abubuwan da ake samar wa daga man fetur, na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar talauci tare da samar da ayyuka a nahiyar.
Samar da matatar a gabashin Afirka na cikin wani ɓangare na zuba jarin dala biliyan 40 da kamfaninsa zai yi daga nan zuwa 2030.















