Tawagar Amurka na shirin tafiya Pakistan domin tattaunawa da Iran

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Washington na cewa wata tawagar Amurka na shirin tashi zuwa Pakistan domin gudanar da tattaunawar sulhu da Iran.
An ruwaito Shugaban Amurka, Donald Trump na cewa yana zaton a wannan mataki babu wanda zai yi wasa da batun na shiga sulhu.
Tehran ta ce har yanzu ba ta da wani shiri kan zagaye na gaba na tattaunawar, sai dai hakan ya bar kofar bude akan yiwuwar yanke shawara a minti na karshe domin halarta.
Tsagaita wutar yakin da ake yi a yanzu tsakanin Amurka da Iran na shirin karewa a ranar Laraba.
Wakiliyar BBC ta ce shugaban Amurka Donal Trump ya ce zai yi mutuƙar wuya ya amince a ƙara wa'adin tsagaita wutar, mutsawar ba a cimma matsaya a yarjejeniyar ba.

















