Aƙalla mutum 47 sun rasu sakamakon girgizar ƙasa a Indonesia

Asalin hoton, Getty Images
Kawo yanzu mai'akatan ceto a Indonesiya ba su isa yankin da ya yi kusa da wurin da girgizar ƙasa ta yi kamari ba wacce ta afakawa yankin da ke gabashin gabar tekun ƙasar da sanyin safiyar yau Asabar.
Zaftarewar ƙasa ta katse hanyoyi da hanyoyin sadarwa a yankin Nagekeo. Aƙalla mutum 47 ne suka rasa rayukansu a tsibirin Flores sakamakon girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.7, yayin da jami'an agajin gaggawa ke ci gaba da neman masu saura numfashi.
Wakilin BBC ya ce Girgizar ƙasar ta tada mutane daga barcinsu a yankuna da dama na wannan tsibiri mai tsaunuka. Sa'o'i kaɗan bayan haka kuma, wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.9 ta faru a tsibirin Sumatra da ke yammacin ƙasar.































