Caicedo ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Chelsea, Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Moisés Caicedo ya tsawaita kwantiragi mai tsoka ta ci gaba da taka leda a Chelsea.
Mai shekara 24 ya nemi sabunta yarjejeniyarsa bayan rawar da ya taka wajen taimaka wa Chelsea ta lashe Europa Conference League da kuma Club World Cup a kakar da ta gabata.
Tun farko ya amince da kwantiragin kaka bakwai da ya koma Stamford Bridge daga Brighton a 2023.
Rahotanni sun nuna cewa sabon kwantiragin zai karkare zuwa karshen kakar 2033.
Wannan yarjejeniya ita ce ta biyu a jerin sabbin kwantiragi da Chelsea ta yi da manyan ƴan wasanta, Kyaftin Reece James shi ne na farko da ya sabunta kwantiragi, yayin da kulob din ke ci gaba da tattaunawa da wasu ƴan wasa kafin ƙarshen kakar bana.
Haka kuma Chelsea ta karawa Cole Palme albashi.
Chelsea za ta karɓi bakuncin Manchester United a Premier League, yayin da ƙungiyar Stamford Bridge ke mataki na shida.












