Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 01/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 1/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Goba ta ƙona shaguna sama da 110 a Kano

    Akalla gine-gine 110 ne suka ƙone sakamakon gobarar da ta tashi a wasu sassan Kasuwar Katako ta Kofar Ruwa da ke jihar Kano a ranar Asabar.

    Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, PFS Kabiru Isah Jafaru, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Kano.

    Ya ce wani ɗan kasuwar katako mai suna Alhaji Abba ne ya bayar da rahoton aukuwar lamarin da misalin ƙarfe 7:39 na safe, wanda hakan ya sa aka gaggauta tura jami’an kashe gobara daga tashoshi daban-daban da ke faɗin birnin Kano.

    A cewarsa, da isar jami’an wurin, sun tarar da gobarar ta mamaye sassa da dama na kasuwar.

    “Gobarar ta shafi gine-gine na dindindin 75 da kuma gine-gine na wucin gadi 35 da ke cikin kasuwar katako,” in ji shi.

    Jafaru ya lura cewa jami’an hukumar sun samu nasarar shawo kan gobarar tare da hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan kasuwar.

    Ya ce har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, yayin da ake ci gaba da bincike.

    Ya kuma ce Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Sani Anas, ya yabawa jami’an kashe gobarar kan gaggawar da suka yi wajen kai ɗauki, tare da kira ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’i da su kasance cikin shiri da taka-tsantsan wajen kare afkuwar gobara, musamman a lokacin damina mai bushewa ta hunturu (harmattan).

    Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu asarar rai ko raunuka sakamakon gobarar ba.

  2. Yamaha ya janye daga gasar MotoGP ta Qatar kan rikicin Gabas ta Tsakiya

    Kamfanin Yamaha ya bayyana cewa ba zai halarci Gasar Grand Prix ta Qatar ba saboda abin da ya kira "halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya."

    Kamfanin na Japan ya sanar a ranar Lahadi cewa ƙungiyar Yamaha ba za ta yi tafiya zuwa Doha domin shiga tseren MotoGP na mako mai zuwa ba, sakamakon yanayin siyasa da tsaro da ake ciki a Gabas ta Tsakiya a halin yanzu.

    A gefe guda kuma, hukumar shirya gasar ta soki matakin da Yamaha ta ɗauka, tana mai bayyana shi a matsayin “abin takaici.”

    Wannan gasa ita ce zagaye na 20 na kakar wasannin MotoGP, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 6 zuwa 8 ga Nuwamba a filin tseren Lusail International Circuit da ke Qatar.

    Wannan ne karo na biyu cikin ‘yan kwanakin nan da rashin tabbas a yankin ya haifar da soke wani babban taron wasanni na ƙasa da ƙasa.

    A ranar 25 ga Oktoba, masu shirya gasar shekara-shekara ta Dakar Rally sun sanar da cewa ba za a gudanar da gasar a Saudiyya ba, matakin da suka ce an ɗauka ne sakamakon “abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a yankin.”

    Hukumar shirya gasar ta kuma sanar da cewa za a gudanar da zagayen na gaba, wanda aka tsara daga ranar 1 zuwa 15 ga Janairun 2027, a wata ƙasa maimakon Saudiyya.

  3. An tsaurara matakan tsaro domin daƙile zanga-zangar Faransa

    An tsaurara matakan tsaro tare da sanya dokar hana zirga-zirga a sassa daban-daban na Faransa, yayin da aka shiga karshen mako na uku a jere ana zanga-zanga.

    Kimanin mutum dubu 320 ne suka halarci zanga-zangar a jiya ranar Asabar, wadda galibi ta kasance cikin lumana, domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma rashin ingancin ayyukan gwamnati.

    Sai dai an kama sama da mutum 400 bayan arangama ta barke tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro a biranen Paris, Toulouse, Lyon da kuma Marseille 9 Marse.

    Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Laurent Nuñez, ya ce wani jami'in dan sanda ya samu raunuka bayan da aka jefa masa bam din kwalba mai.

    Ya kuma ce jami'an tsaro za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana matukar akwai bukatar hakan domin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda.

  4. Ba a lokacin Tinubu aka fara matsalar tsaro ba - Dogara

    Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya ce matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta sun fara ne tun kafin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai nuni da cewa ta’addanci, tayar da ƙayar baya da kuma fashin daji sun riga sun yi katutu a ƙasar kafin Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023.

    Dogara, wanda shi ne Shugaban Jami’ar Achievers da ke Owo a Jihar Ondo, ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye dalibai karo na 16 na jami’ar, inda dalibai 836 suka samu takardun shaidar karatu daban-daban.

    Ya ce matsalolin tsaron ƙasar sun samo asali ne daga shekaru na raunin tsaron kan iyakoki, yawaitar makamai ba bisa ƙa’ida ba, rashin aikin yi a tsakanin matasa da kuma yaɗuwar akidun tsattsauran ra’ayi.

    “Rashin tsaro a Najeriya bai fara da wannan gwamnati ba. Wannan ba uzuri ba ne, domin gaskiya ba ta bukatar kariya. Ta’addanci, tayar da ƙayar baya, fashin daji, garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci ba su zo a shekarar 2023 ba,” in ji shi.

    Dogara ya ƙara da cewa waɗannan ƙalubale sun bunƙasa tsawon shekaru masu yawa, yana mai jaddada cewa tushensu ya yi zurfi tun kafin Tinubu ya karɓi mulki a watan Mayun 2023.

    Sai dai ya lura cewa Tinubu ya kasance yana ɗaukar tsaron ƙasa a matsayin ɗaya daga cikin manyan nauyin da ke kan gwamnatinsa. Haka kuma ya taya waɗanda suka kammala karatunsu murna, yana cewa ƙasar na buƙatar baiwarsu, ƙirƙirarsu da sabbin fasahohinsu.

    A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Gudanarwar jami’ar, Farfesa Bode Ayorinde, ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen faɗaɗa damar samun ilimin boko na jami’a, amma ya nuna damuwa game da makomar waɗanda suka kammala karatu bayan sun bar makaranta.

    Ayorinde ya ambato alkaluman Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), waɗanda suka nuna cewa ya zuwa watan Yunin 2026 akwai jami’o’i 312 a ƙasar, da suka haɗa da jami’o’in tarayya 77, na jihohi 67 da kuma masu zaman kansu 168.

    Ya ce waɗannan cibiyoyi suna wakiltar babban zuba jari a fannin bunƙasa albarkatun ɗan Adam, inda iyaye, gwamnatoci da malamai ke yin sadaukarwa domin samar da ƙwararrun ma’aikata, amma ya tambayi irin damar da ke jiran waɗanda suka kammala karatu bayan sun gama karatunsu.

    Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Omolola Irinoye, ta ce jami’ar ta ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantaccen ilimi da ya haɗa da bunƙasa ilimi, ƙwarewar aiki, gina ɗabi’a da kuma ɗaukar nauyin zamantakewa tun bayan kafuwarta.

  5. Idan Amurka ta sake taɓa mu, za mu iya kai hari a duk inda take da sojoji - Iran

    Mohammad Akraminia, kakakin rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya ce idan aka sake samun wani yaƙi, "rikicin ba zai tsaya a yankin Yammacin Asiya kaɗai ba."

    A cewarsa, "wuraren da Amurka ke da cibiyoyi, kayan aiki, sojoji da muradunta, a duk inda za a iya kai musu hari, na iya zama abin hari."

    Da yake magana kan “ƙarfafa shirin aiki da kuma sabunta jerin manufofin da aka tanada domin kai hare-hare,” Mista Akraminia ya ce duk wa yaƙin da zai iya tasowa nan gaba na iya kasancewa "mai tsawo fiye da yaƙin da ya gabata."

    Kakakin rundunar sojin ya kuma ce: "Tun a baya aka fara sauya akidar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga ta kariya kawai zuwa wadda ta haɗa da kai farmaki, kuma hakan ya bayyana a aikace a yaƙin baya-bayan nan."

    Shafin yanar gizon hukuma na Mojtaba Khamenei ya ruwaito jiya cewa, a wani taro da kwamandojin rundunonin sojin Iran, an umarce su da su mayar da martani "cikin gaggawa kuma ba tare da wani iyakar yanki ba" ga duk wata barazana daga abokan gaba.

    An kuma ruwaito Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran yana cewa, idan aka sake kai wa Iran wani hari na soja ko kuma abin da ya bayyana a matsayin "ta'addanci", Iran ce za ta ƙayyade lokacin da kuma yanayin da rikicin zai ƙare.

  6. Aƙalla mutum 100,000 suka halarci zanga-zangar tsadar rayuwa a Jamus

    To ana gudanar da irin wannan zanga-zangar a wasu kasashen Turai, ciki har da Jamus, inda aka samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da kuma jami'an tsaro.

    A birnin Frankfurt, masu zanga-zangar sun fasa shaguna tare da farfasa tagogi, yayin da wasu suka rika jefa duwatsu da kuma bam din da ake hadawa da fetur.

    Hukumomi sun girke jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma a biranen Hamburg da Cologne domin dakile rikice-rikice.

    Kungiyar matasa mai suna "Gen Z regelt!", ta ce fiye da mutum dubu 100 ne suka halarci zanga-zangar lumana da aka gudanar a ranar Asabar a birane 34.

    Kamar sauran kungiyoyi masu irin wannan ra'ayi, kungiyar na fafutukar ganin an inganta ilimi da rage tsadar rayuwa, tare da nuna adawa da tilasta shiga aikin soja.

  7. Aƙalla mutum 100,000 uka halarci zanga-zangar tsadar rayuwa a Jamus

    To ana gudanar da irin wannan zanga-zangar a wasu kasashen Turai, ciki har da Jamus, inda aka samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da kuma jami'an tsaro.

    A birnin Frankfurt, masu zanga-zangar sun fasa shaguna tare da farfasa tagogi, yayin da wasu suka rika jefa duwatsu da kuma bam din da ake hadawa da fetur.

    Hukumomi sun girke jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma a biranen Hamburg da Cologne domin dakile rikice-rikice.

    Kungiyar matasa mai suna "Gen Z regelt!", ta ce fiye da mutum dubu 100 ne suka halarci zanga-zangar lumana da aka gudanar a ranar Asabar a birane 34.

    Kamar sauran kungiyoyi masu irin wannan ra'ayi, kungiyar na fafutukar ganin an inganta ilimi da rage tsadar rayuwa, tare da nuna adawa da tilasta shiga aikin soja.

  8. Aƙalla mutum 100,000 suka halarci zanga-zangar tsadar rayuwa a Jamus

    To ana gudanar da irin wannan zanga-zangar a wasu kasashen Turai, ciki har da Jamus, inda aka samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da kuma jami'an tsaro.

    A birnin Frankfurt, masu zanga-zangar sun fasa shaguna tare da farfasa tagogi, yayin da wasu suka rika jefa duwatsu da kuma bam din da ake hadawa da fetur.

    Hukumomi sun girke jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma a biranen Hamburg da Cologne domin dakile rikice-rikice.

    Kungiyar matasa mai suna "Gen Z regelt!", ta ce fiye da mutum dubu 100 ne suka halarci zanga-zangar lumana da aka gudanar a ranar Asabar a birane 34.

    Kamar sauran kungiyoyi masu irin wannan ra'ayi, kungiyar na fafutukar ganin an inganta ilimi da rage tsadar rayuwa, tare da nuna adawa da tilasta shiga aikin soja.

  9. FBI ta zargi Koriya ta Arewa ta hannu a satar kirifito a Binance

    Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI), ta zargi Koriya ta Arewa da hannu a satar kuɗaɗen kirifto da darajarsu ta haura dala biliyan shida daga kamfanin musayar kuɗaɗen kirifto na Binance a ranar Alhamis da ta gabata.

    Wakiliyar BBC ta ce FBI ta ce an ga jami'an wannan sashi suna karkatar da kadarorin, kuma ana sa ran za a ci gaba da halasta kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

    Ana ganin wannan na iya zama babbar satar kuɗaɗen kirifto da aka taba yi a tarihi.

    Tun da farko wasu sharhi kan harkokin intanet sun bayyana cewa suna zargin wata kungiyar masu kutse ta Koriya ta Arewa da ake kira TraderTraitor da aikata wannan aika aika.

    Sai dai gwamnatin Koriya ta Arewan ta musanta zargin cewa tana dogaro da laifukan yanar gizo wajen samar da kudaden gudanar da harkokinta.

  10. 'An samu raguwar hare-haren masu tada ƙayar baya da kashi 73.3% a Oktoba a Najeriya'

    Sojojin Najeriya sun ce hare-haren da masu tayar da ƙayar baya da sauran masu aikata laifuka suka kai a sassan ƙasar sun ragu da kashi 73.3 cikin ɗari a watan Oktoba idan aka kwatanta da watan Satumba, kamar yadda tashar talabijin mai zaman kanta ta Channels TV ta ruwaito a ranar 31 ga Oktoba.

    Kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce a ranar 30 ga Oktoba an samu hare-hare 269 a watan Oktoba, idan aka kwatanta da 367 da aka samu a watan Satumba, wanda ya nuna raguwar hare-hare 98.

    Ya ce wannan raguwar ta samo asali ne sakamakon ci gaba da gudanar da ayyukan soji a fannoni daban-daban na ƙasar.

    Dangane da rabe-raben alkaluman watan Oktoba, Operation Enduring Peace ce ta fi yawan hare-hare da aka samu da adadin 29, sai Operation Hadin Kai da hare-hare 27, sannan Operation Fansan Yamma da hare-hare 24.

    Haka kuma, Operation Whirl Stroke ta samu hare-hare 12, yayin da Operation Udo Ka ta samu 4, sannan Operation Delta Safe da Operation Savannah Shield suka samu hari guda ɗaya kowacce.

    Janar Onoja ya ce: "A lokacin da ake magana a kai, Rundunar Sojojin Najeriya (AFN) ta fuskanci jimillar hare-hare 98 a wuraren gudanar da ayyuka daban-daban."

    Ya kuma bayyana cewa sojoji sun kashe fiye da 'yan ta'adda da masu laifi 217, tare da kama mutane 333 da ake zargi, sannan sun kuɓutar da mutane 349 da aka yi garkuwa da su a cikin watan.

    A cewarsa, 'yan tada kayar baya 70 sun miƙa wuya ga sojoji, yayin da aka ƙwato makamai 105 da kuma alburusai 3,174.

    Janar Onoja ya kuma ce sojojin sun ƙwato lita 756,837 na ɗanyen man fetur da aka sace ko kayayyakinsa, tare da lalata matatun mai na haramtattu 49 a ayyukan da aka gudanar domin yaƙi da satar ɗanyen mai.

    Sojojin Najeriya sun ƙara kaimi wajen gudanar da hare-hare da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na ƙasar domin daƙile tashe-tashen hankula da hare-haren masu tayar da ƙayar baya da sauran masu aikata laifuka.

  11. An tsaurara matakan tsaro domin daƙile zanga-zangar Faransa

    An tsaurara matakan tsaro tare da sanya dokar hana zirga-zirga a sassa daban-daban na Faransa, yayin da aka shiga karshen mako na uku a jere ana zanga-zanga.

    Kimanin mutum dubu 320 ne suka halarci zanga-zangar a jiya ranar Asabar, wadda galibi ta kasance cikin lumana, domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma rashin ingancin ayyukan gwamnati.

    Sai dai an kama sama da mutum 400 bayan arangama ta barke tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro a biranen Paris, Toulouse, Lyon da kuma Marseille 9 Marse.

    Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Laurent Nuñez, ya ce wani jami'in dan sanda ya samu raunuka bayan da aka jefa masa bam din kwalba mai.

    Ya kuma ce jami'an tsaro za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana matukar akwai bukatar hakan domin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda.

  12. Kotu ta yi watsi da ƙarar ɓata suna da Trump ya shigar kan jaridar Wall Street

    Wata kotun Amurka ta yi watsi da ƙarar ɓata suna da shugaban ƙasar Donald Trump ya shigar kan jaridar Wall Street Journal da kuma attajirin nan mai kafafen yada labarai Rupert Mardoch.

    Jaridar ta wallafa rahoton cewa Mista Trump ya aike wa marigayi Jeffrey Epstein, wanda aka samu da hannu a laifukan cin zarafin yara ta hanyar lalata, wani sakon taya murnar ranar haihuwarsa mai dauke da kalamai masu nuna sha'awa, tare da hoton zanen siffar jikin mace tsirara.

    Fadar White House ta musanta ingancin wasikar, tana mai cewa Mista Trump ba shi ne ya zana hoton ba, kuma bai sanya hannu a kai ba.

    Alkalin da ya yanke hukuncin ya ce Mista Trump bai iya gabatar da hujjar da za ta nuna cewa an wallafa rahoton ba daidai ba.

  13. Gwaji ya nuna cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da Ebola a Najeriya

    Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce gwaje-gwajen ɗakin gwaji da aka gudanar kan samfurorin mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a jihar Adamawa sun nuna sakamakon da ke tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da cutar a jihar.

    Sanarwar da hukumar ta fitar a daren Asabar ta biyo bayan wani gargaɗi da ta bayar tun farko game da gano wasu mutane biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar a Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Babban daraktan NCDC, Dkta Jide Idris, ya ce hukumomin lafiya na jihar sun samu rahoto a ranar Juma’a bayan gano wasu mutane biyu da ke nuna alamomin da suka yi kama da na Ebola. Wannan ya sa aka killace su tare da fara daukar matakan da suka dace.

    “An tattara samfurori domin gudanar da gwaje-gwajen ɗakin gwaji don gano haƙiƙanin cutar da ke damun su. Abin farin ciki, sakamakon gwaje-gwajen sau biyu da aka yi ya nuna cewa ba su ɗauke da cutar Ebola,” in ji Dokta Jide.

    A halin yanzu, hukumomi na kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko hasashe marasa tushe game da yaɗuwar cutar.

  14. Tattaunawa da Iran na tafiya da kyau, amma ba su da amana - Trump

    Donald Trump ya ce: "Tattaunawar da ake yi da Iran na tafiya da kyau a wannan lokaci, amma babbar matsalar ita ce ba su da cikakkiyar amana. Sukan ƙulla yarjejeniya, sannan daga baya cikin sauƙi su saɓa alƙawuransu ko kuma su janye daga abin da suka amince da shi."

    Kalaman Mista Trump na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an Iran suka sha zargin gwamnatinsa da karya alƙawuran da ta ɗauka tare da kai wa Iran hare-hare a yayin da ake ci gaba da tattaunawa.

    Da yake magana da manema labarai a wurin shaƙatawarsa da ke Florida, Trump ya ce: "Mun lalata cibiyoyinsu na makamashin nukiliya. Har yanzu akwai wuri guda ko biyu da ya rage a kula da su, amma za mu iya yin hakan cikin mintuna 10."

    Ya kuma yi magana kan cibiyar Mount Klang, yana cewa: "Wataƙila ya kamata mu dubi wannan wurin ma; za mu iya kammala komai cikin gaggawa."

    Tun da farko, Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya ce har yanzu Donald Trump bai yanke hukuncin ko zai kaddamar da harin soja kan Iran ba.

    A gefe guda kuma, jami’an Iran sun yi gargadi a ranar Asabar cewa za su mayar da martani mai tsanani idan Amurka ta kai musu hari.

  15. Farawa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, Assalamu alaikum. A yau ma, kamar kullum, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa kamar a Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.