Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United na tuntuɓa kan Toney, Barcelona na sa ido kan Willian
Manchester United ta tuntuɓi Al-Ahli kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan ƙugiyar Ivan Toney, sai dai sun ƙare da tattunawa da ɗan wasan Leeds Dominic Calvert-Lewin. (Caught Offside)
Barcelona na bibiyar ɗan wasan Chelsea Estevao Willian, inda ta ke saon ganin ta dauko ɗan wasan mai shekaru 19. (Sport - in Spanish)
Ɗan wasan Sipaniya Fermin Lopez baya son barin Barcelona, duk da Manchester United da Chelsea na son daukarsa. (Fabrizio Romano)
Alamu na nuni cewar ɗan wasan Japan Wataru Endo, da takwaransa na Italiya Federico Chiesa, na iya barin Liverpool a shekara mai zuwa. (Echo)
Akwai yiwuwar ɗan wasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, ya iya barin ƙungiyar a watan Janairu. (Teamtalk)
Haka kuma har yanzu babu wani tabbaci na cewar Palace zata zuba kuɗin ta kan Mateta, a kakar siyen ƴan wasa ba, ko kuma ta ajiye shi har zuwa lokacin da kwantaraginsa za ta ƙare. (Football Insider)
Arsenal na ci gaba da tattaunawa da Real Madrid kan Endrick, duk da cewar Madrid ɗin ba ta sanar da cewar ɗan wasan zai bar ƙungiyar ba a wannan kakar ba. (Teamtalk)
Arsenal ta bi sahun Bournemouth wajen zawarcin ɗan wasan FaransaEli Junior Kroupi, idan Arsenal din ke sa ido kan ɗan wasan Eintracht Frankfurt Can Uzun. (Caught Offside)
Paris St-Germain na cikin jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Fransa Kroupi. (Goal)
Ɗan wasan Manchester United JJ Gabriel ya shirya tsaf don barin Trafford, inda ya ke dab da komawa Real Madrid. (Sport - in Spanish)
Everton ba za ta ɗauko dan wasan Amuraka Folarin Balogun ba daga Monaco a watan Janairu ba, biyobayan yadda ɗan wasan bai tabuka komai ba a wannan kaka ba. (Football Insider)