Mourinho da rikici - shin ana yi wa kocin Real Madrid mummunar fahimta?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 10

Magoya bayan Barcelona sun daɗe suna yi wa Jose Mourinho ba'a, inda kalmar da suka fi amfani da ita mai cewa traductor - kalmar Sifaniyanci da ke nufin mai fassara.

Wata hanya ce ta muzanta irin asalin da ya fito daga gare shi.

Yayin da yake koyon sana'ar da za ta zama aikinsa na gaba a matsayin mai fassara ga fitaccen koci Sir Bobby Robson Mourinho ya bi Robson daga Sporting zuwa Porto, kafin su koma Barcelona a shekarar 1996.

Shekaru huɗu bayan haka, Mourinho ya zama kocin Benfica, matakin farko na aikinsa a matakin horaswa wanda daga baya ya kai shi ga lashe Champions League sau biyu da kuma samun manyan nasarori a Ingila da Italiya da kuma Sifaniya.

A zahiri ya zarce matsayin mai fassara nesa ba kusa ba, har ma tun lokacin da yake a Barcelona.

Babban nasarar da kocin ɗan ƙasar Portugal ya samu a wurare daban-daban ita ce kyaun halayensa na hakika da ke gina nasarorinsa: mai himma, mai jajircewa, mai zurfin tunani, mai iya bunƙasa abuuwa koda a cikin yanayin rikici, kuma ƙwararre a dabarun wasan ƙwallon ƙafa.

A karshen makon da ya gabata, yayi amfani da kwakwalwarsa ta amfani da salo da dabarun da suka kai Real Madrid ta je har Camp Nou ta doke Barcelona 2-1 a wasan La Liga.

Yayin da duniyar ƙwallon ƙafa ke yabawa dabarun da Jose Mourinho ya yi amfani da su, lokaci ne da ya dace domin waiwayar shekara 26 da ya yi a aikin horaswa a tarihinsa.

A wasan na hamayya na El Clasico, Real Madrid ta buga karawar da salo da tsarin 4-4-2, duk da cewa dan kasar Brazil, Vinicius Jr bai buga wasan sa, saboda hukuncin dakatarwa.

Federico Valverde ya taka leda a matsayin mai tsaron baya daga gefen dama. An fara fafatawar da Bernardo Silva a matakin dan tsakiya tare da Aurelien Tchouameni. Arda Guler da Yan Diomande sun taka leda a gefen da suka buga, yayin da Jude Bellingham da Kylian Mbappe suka jagoranci kai hare-hare ƙungiyar.

Kamar yadda ya saba yi a manyan wasanni, Mourinho ya ɗorawa ɗaya daga cikin 'yan wasansa masu aiki tukuru alhakin tare fitaccen ɗan wasan abokan hamayya. A wannan karon, Silva ne aka ɗora wa aikin sa ido kusa da kusa da Pedri na Barcelona.

Ba aiki ne mai sauƙi ba, amma ya taimaka ƙwarai wajen rage tasirin ɗan wasan na Sifaniya a wasan.

Da yake lura da yadda Barcelona ke matsa lamba sosai da kuma yadda 'yan wasanta ke taruwa kusa da inda ƙwallo take, 'yan wasan Real Madrid sun riƙa jan abokan hamayyarsu zuwa gefen fili ta hagu da dama, kafin su yi amfani da sararin da ya buɗe a ɗaya gefen filin, ta hanyar kwarewa wajen yanka ko kuma dogayen passes masu sauya alkiblar wasa.

An lura da wannan salon da Real Madrid ke yi musamman lokacin da aka mayar da ƙwallo daga gefen dama zuwa gefen hagu, inda Marc Cucurella ke kutsawa ta bayan Lamine Yamal.

Bayan wasan, Jose Mourinho ya saɓa ɗabi'ar da yake yi a koda yaushe.

Domin baya yin bayani a bainar jama'a kan dabarun wasan da ya yi amfani da shi, amma a wannan karon ya fayyace yadda ya gina salon hare-haren da 'yan wasansa na tsakiyar suka ta yi da ya zama abin wahala da Barcelona ta kasa dakilewa.

Kasancewarsa ƙwararre wajen amfani da taron manema labarai a matsayin fayyace abin da ya faru a filin wasa, watakila Mourinho ya bayyana dabarunsa ne da fatan cewa abokan hamayyar Barcelona za su kula da su nan gaba idan sun kara haduwa.

Ƙwarewarsa wajen tsara yadda za a samu nasara a manyan wasanni ke sawa ake yaba wa Jose Mourinho yadda ya kamata, amma salon aikinsa gaba ɗaya ba ya samun yabo gwargwadon yadda ya cancanta.

A shekarun baya-bayan nan, masu horarwa da ke da tsayayyun dabaru da tsarin wasa ko takamaiman amfani da matsayin 'yan wasa a fili sun kasance waɗanda ake yabawa a matsayin hazikan koyar da wasan ƙwallon ƙafa.

Mourinho bai bi wannan hanya ba, inda ya fi karkata ga amfani da ƙwarewar 'yan wasansa tare da dabarun sauya salo gwargwadon ƙungiyar da yake jagoranta.

Wannan salon da ba shi da tsayayyen tsari sosai ya fi wahalar nazari daga wajen fili, abin da kan sa mutane su kasa fahimtar aikinsa yadda ya kamata.

Mourinho mai bin tsarin tactical periodisation ne, wata hanyar tunanin ƙwallon ƙafa da Vitor Frade ya assasa.

Yayin da Mourinho ke aiki tare da Sir Bobby Robson a Porto a tsakiyar shekarar 1990, Frade ma yana cikin tawagar masu horarwar.

Ta hanyar amfani da dabaru daga ilimin halayyar ɗan Adam, ilimin zamantakewa, ilimin tsarin jijiyoyin jiki da kuma ka'idar tsari aiki, tunanin Frade ya yi watsi da ra'ayin cewa bangarorin fasaha, dabara, ƙarfin jiki da tunanin ɗan wasa a ƙwallon ƙafa ya kamata a ɗauke su a matsayin abubuwa daban-daban.

Wani ɓangare na wannan tunanin shi ne cewa a lokacin wasa ba a amfani da waɗannan abubuwa daban-daban, sai dai dukkansu suna aiki ne lokaci guda.

Lokacin da Mourinho ya karɓi ragamar Real Madrid a wannan kakar, jaridar Athletic ta ruwaito cewa atisayen ƙungiyar ya koma gajeru, amma masu tsanani, kuma a kullum ana gudanar da su tare da amfani da ƙwallo.

A ƙwallon ƙafa, masu horarwa sun fi karkata zuwa ɗaya daga cikin hanyoyi biyu.

Wasu suna ƙoƙarin rage tasirin abubuwan da ba a za ta ba da zai iya faruwa a wasa, yayin da wasu, ciki har da masu bin tsarin tactical periodisation, suke amincewa da waɗannan abubuwan kuma su daidaita dabarunsu da su.

Jose Mourinho ya fara aikinsa na horaswa cikin nasara mai ban mamaki, inda ya lashe Uefa Cup da Champions League tare da Porto, ya mayar da Chelsea babbar ƙungiya a Ingila, ya jagoranci Inter zuwa lashe kofuna uku a kakar wasa guda, sannan ya lashe La Liga tare da Real Madrid.

Sai dai tsakanin 2019 da 2025, ya karɓi aikin horas da ƙungiyoyin da ba a sa tsammanin da ake yi wa ƙungiyoyin da ya jagoranta a farkon aikinsa ba.

Tun bayan da ya lashe EFL Cup da Europa League tare da Manchester United a 2017, kofin da ya lashe kawai shi ne Conference League da ya samu tare da Roma a 2022.

A cikin wannan shekaru goma, masu horarwar da suka fi samun nasara su ne waɗanda suka fi rage tasirin rudani da abubuwan da ba a za ta ba a wasa.

Yayin da magoya baya ke kallon wasanni masu kama da wasan dara, masu horarwa da ke nasara sun fi son ƙungiyoyinsu su riƙe ƙwallo na dogon lokaci, tare da tsara su cikin tsare-tsare da ya kamata da kuma rawar da kowane ɗan wasa zai taka, kamar 'yan wasan gefe ko masu tsaron bayan da ke matsawa cikin gurbin tsakiya.

Sau da yawa abokan hamayya kan rufe yankuna da yawa, inda 'yan wasa ke kula da wasu sassan fili, maimakon lura da mutum ɗaya.

Hakan yana ba ƙungiyar da ke kai hari damar tsara yadda 'yan wasanta za suke zuwa wuraren da za su samu rinjaye a wasu sassan filin wasan.

A kakar wasannin baya-bayan nan, an samu ƙaruwa a amfani da tsarin matsa lamba na ɗan wasa kan ɗan wasa (man-to-man pressing), wanda ya rage damar da ƙungiyoyi ke samu na ƙirƙirar rinjaye a wasu sassan fili.

Wannan matsa lambar na kuma sanya matsin lamba kai tsaye ga 'yan wasan da ke da ƙwallo, wanda ke sa su yanke shawara cikin gaggawa.

Hakan ya sa wasanni suka fi kama da masu rikice-rikice kuma marasa tabbas, wani yanayi da zai iya zama mai amfani ga Jose Mourinho.

Masu bin koyarwar Vitor Frade sun yi imanin cewa rikice-rikice da abubuwan da ba a za ta ba, ba za a iya raba su da wasan ƙwallon ƙafa ba.

Ta hanyar horaswa mai haɗa dukkan bangarorin wasan baki ɗaya, ana fatan 'yan wasa za su kasance cikin shiri mafi kyau wajen warware matsaloli a take yayin wasa.

Wataƙila wannan ne dalilin da ya sa ƙungiyoyin da Jose Mourinho ya horar suka saba yin fice a yanayi masu wahala, lokacin da ake kallonsu a matsayin ba za su iya tasiri ba a wasanni masu matuƙar muhimmanci, ko kuma idan wasa ya kauce daga tsarin da aka tsara tun kafin fara fafatawa.

Mourinho ba ya amfani da shawarar da 'yan wasansa za su yanke a fili. Maimakon haka, yana ƙoƙarin shirya su ne domin su iya samo mafita da kansu; kuma a ka'ida, idan ƙwararrun 'yan wasa ne, mafitar da za su samu ita ma za ta kasance mafi inganci.

Saboda haka ne a wasan da suka yi da Barcelona, muka ga fitattun 'yan wasa irin su Jude Bellingham da Kylian Mbappe da Bernardo Silva suka yi fice, kowannensu yana taka leda cikin salonsa na musamman, amma ta hanyar da ta haɗu wuri guda lokacin da muhimmancin wasan ya kai kololuwa.

Mbappe ya riƙa matsawa layin tsaron bayan Barcelona tare da kai hare-hare ta hanyar cin ƙwallaye.

Bellingham ya nuna kwazon neman ƙwallo, yayin da kuma yake nuna ƙwarewa da natsuwa wajen sarrafa ƙwallon da wuce da ita ta gefen abokan hamayya.

Shi kuwa Silva ya riƙa rage saurin wasan a lokacin da Barcelona ke matsa lamba sosai, kafin ya tura ƙwallo ga takwarorinsa da ke gaba, bayan abokan hamayyar sun riga sun matsa domin ƙwace ƙwallon.

Mourinho yana son dawowa da sake gina abin da ya riga ya fara.

Ya fara aikinsa na horaswa a Benfica, sannan ya sake koma wa kungiyar, bayan shekara 25 a watan Satumbar 2025.

Ya lashe gasar lig sau biyu a jere tare da Chelsea, kafin ya sake komawa Stamford Bridge shekaru shida bayan ya bar kungiyar da ya lashe kofinsa na uku.

Yanzu kuma, shekara 13 bayan wa'adinsa na farko da ya kare a Real Madrid, ya sake komawa Bernabeu domin wa'adi na biyu.

Saboda haka, daidai ne a ce yadda duniyar ƙwallon ƙafa ke sauyawa na iya ba shi wata dama ta sake gudanar da aiki, amma a wannan karon ta fuskar dabarunsa horarwa a wasan.