Amurka ta ƙara faɗaɗa takunkuman kasuwanci kan kayayyakin Kanada
Amurka ta faɗaɗa takunkuman kasuwanci kan kayayyakin Kanada, inda ta haramta shigar da wasu kayayyaki gaba ɗaya, yayin da saɓanin tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara kamari.
Sabbin matakan sun haɗa da hana shigar da barasa, kayayyakin madara da babura daga Kanada zuwa Amurka.
Shugaba Donald Trump ya zargi Kanada da nuna wariya ga Amurka, bayan da gwamnatin Kanada ta fara aiwatar da harajin ramuwar gayya na kashi 50 cikin 100, daidai da matakan da Washington ta ɗauka kan kayayyakin Kanada.
Ana sa ran sabbin takunkuman na Amurka, waɗanda suka haɗa da ƙara yawan kayayyakin Kanada da za a ƙaƙaba wa haraji, za su fara aiki a ƙarshen wannan watan.
Firaministan Kanada, Mark Carney, ya gargaɗi ƴan ƙasar cewa rage dogaro da makwabciyarsu Amurka ba zai rasa tasiri ga tattalin arzikin Kanada ba.
Sai dai ya ce, hakan shi ne mafi alheri fiye da ci gaba da sayen kayayyakin Amurka.