Ingila ta yi nasara a kan Mexico
Ingila ta nuna bajinta fiye da duk wasanninta na baya tun bayan fara Gasar Kofin Duniya ta bana inda ta yi galaba a kan Mexico a filin wasa na Azteca gaban cincirindon magoya bayan kasar mai masaukin baki.
Hakan ya sanya a yanzu Ingila za ta kara da Norway a matakin kwata-fainal.
Nasarar da Ingila ta samu da ci 2-3 ta zo ne duk kuwa da cewa an bai wa danwasanta Jarell Quansah katin kora bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Danwasa Jude Bellingham ne ya zura kwallo biyu kusa da kusa gabanin zuwa hutun rabin lokaci.
Sai dai Julian Quinones ya farke wa Mexico kwallo daya minti uku kafin zuwa hutun na rabin lokaci.
Ingila ta sake dawo da kwallo daya ta kafar Harry Kane bayan samun bugun fenariti, sai dai a cikin minti 10 bayan haka ita ma Mexico ta samu bugun fenariti inda ta sake farke kwallo ta biyu ta kafar danwasanta Jimenez.