Gasar Kofin Duniya: Ingila ta yi nasara kan Mexico - Norway ta cire Brazil

Wannan shi ne da zai ke kawo muku labarain wasanni sharhi da bayanai da suka shafi gasar cin kofin duniya 2026 da wasu batutuwan da suka shafi wasanni

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Haruna Kakangi tare da taimakon AI

  1. Ingila ta yi nasara a kan Mexico

    xxx

    Asalin hoton, Reuters

    Ingila ta nuna bajinta fiye da duk wasanninta na baya tun bayan fara Gasar Kofin Duniya ta bana inda ta yi galaba a kan Mexico a filin wasa na Azteca gaban cincirindon magoya bayan kasar mai masaukin baki.

    Hakan ya sanya a yanzu Ingila za ta kara da Norway a matakin kwata-fainal.

    Nasarar da Ingila ta samu da ci 2-3 ta zo ne duk kuwa da cewa an bai wa danwasanta Jarell Quansah katin kora bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Danwasa Jude Bellingham ne ya zura kwallo biyu kusa da kusa gabanin zuwa hutun rabin lokaci.

    Sai dai Julian Quinones ya farke wa Mexico kwallo daya minti uku kafin zuwa hutun na rabin lokaci.

    Ingila ta sake dawo da kwallo daya ta kafar Harry Kane bayan samun bugun fenariti, sai dai a cikin minti 10 bayan haka ita ma Mexico ta samu bugun fenariti inda ta sake farke kwallo ta biyu ta kafar danwasanta Jimenez.

  2. An tashi wasa: Norway ta kai kwata-fainal, Brazil 1-2 Norway

    Haaland ya zura kwallo biyu da ta kai Norway kwata-fainal.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Hawaye ke kwarara daga idon Neymar babu kakkautawa. Da alama wannan wasan shi ne na karshe ga Neymar a Gasar Kofin Duniya.

    To amma za a iya cewa Norway ta cancanci ta yi nasara a wannan wasa saboda ita ce ta fi shafa kwallo.

  3. Kwallo a raga: Brazil ta farke kwallo daya, Minti na 90+10: Brazil 1-2 Norway

    Neymar ya zura kwallo.

    Brazil ta farke kwallo daya bayan da Neymar ya zaunar da mai tsaron ragar Norway Orjan Nyland gefe daya.

    Amma dai babu sauran lokaci.

  4. Fenariti: Brazil ta samu fenariti, Minti na 90+9: Brazil 0-2 Norway

    An bai wa Brazil fenariti bayan Leo Ostigard ya bugi fuskar Casemiro da gwiwar hannunsa a lokacin da suka yi kokarin kara wa kwallo kai.

  5. Kwallo a raga: Haaland ya zura kwallo ta biyu, Minti na 90: Brazil 0-2 Norway

    Abin mamaki, Haaland ya zura kwallo ta biyu.

    Ko Brazil na da sauran dama kuwa?

    xx

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Kwallo a Raga: Norway ta zura kwallo, Minti na 79: Brazil 0-1 Norway

    Haaland ya jefa kwallo a raga.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Brazil ta saka Neymar, Minti na 68: Brazil 0-0 Norway

    Neymar lokaci ya yi!

    Brazil ta cire Rayan, an maye gurbinsa da Neymar.

    An kuma cire Gabriel Martinelli aka sako Danilo Santos.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Brazil ta cire Cunha, Minti 58: Brazil 0-0 Norway

    An cire Matheus Cunha an sako Endrick.

  9. An dawo daga hutun rabin lokaci, Brazil 0-0 Norway

    An dawo hutun rabin lokaci a wannan wasa tsakanin Brazil da Norway.

    Ko za a samu kasar da za ta yi nasara kafin minti 90?

    Norwaytasauyayanwasa biyu: An saka Oscar Bobb da Andreas Schjelderup, aka cire Alexander Sorloth da Antonio Nusa.

  10. Hutun rabin lokaci, Brazil 0-0 Norway

    An tafi hutun rabin lokaci ba tare da kowane daga cikin kasashen biyu ya samu damar zura kwallo a raga ba.

    Sai dai wasan ya yi zafi, inda daga bangaren Brazil ‘yanwasa irin su Martinelli da Vinicius suka rika kai farmaki, a bangaren Norway kuma Haaland da Ordegard sun samu dama, sai dai a karshe kwallo ba ta shiga raga ba.

    Brazil ta kai hari sau 10

    Norway ta kai hari sau 6

    Norway ta fi shafa kwallo, inda take da 64.9%, Brazil na da 35.1%.

  11. An barar da fenariti, Brazil 0-0 Norway

    Bruno Guimaraes Ya baras da fenariti.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Fenariti: Brazil ta samu bugun fenariti, Brazil 0-0 Norway

    Wannan babbar dama ce ga Brazil.

  13. An take wasa: Brazil 0-0 Norway

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    An take wasa tsakanin Brazil da Norway a matakin ‘yan 16. Duk kasar da ta yi nasara a tsakaninsu za ta kara da ko dai Ingila ko Mexico a matakin kwata-fainal.

    Yanwasan Brazil:

    Alisson, Santos, Gabriel, Marquinhos, Danilo, Martinelli, Casemiro, Guimaraes, Rayan, Vinicius, Cunha.

    Benci: Ederson Silva, Sandro, Neymar, Raphinha, Weverton, Bremer, Pereira, Fabinho, Danilo Santos, Endrick, Henrique, Ederson, Ibanez, Thiago.

    Yanwasan Norway:

    Nyland, Wolfe, Heggem, Ajer, Ryerson, Berg, Berge, Odegaard, Nusa, Sorloth, Haaland.

    Benci: Thorsby, Ositgard, Strand Larsen, Tangvik, Selvik, Aursnes, Bjorkan, Pedersen, Thorstvedt, Aasgaard, Schjelderup, Bobb, Hauge, Langas, Falchener.

  14. Gasar Kofin Duniya: Za a goge raini tsakanin Haaland da Gabriel

    Xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a yi baje-kolin daya daga cikin adawa mafi zafi ta gasar Premier Ingila a Gasar Kofin Duniya a daren ranar Lahadi sa’ilin da Brazil za ta kara da Norway a zagayen ‘yan 16.

    Zakakurin dan wasan gaba na Norway kuma dodon raga mai wasa a kungiyar Manchester City Erling Haaland zai yi gaba da gaba da bangon dutse na Brazill kuma mai taka wa ataku birki, dan wasan Arsenal, Gabriel Magalhaes.

    Za a yi karawar ne a filin wasa na New Jersey da ke New York.

    Haaland da Gabriel sun kasance manyan turaku a kungiyoyinsu, inda hakan ya sa suka zamo manyan abokan hamayya, inda lokaci-lokaci hamayyar tasu kan yi zafi har ta kai ga tayar da hakarkari.

    Wannan karo za su yi gaba da gaba a wasan da zai tantance wace kasa ce tsakanin Brazil da Norway za ta kai matakin kwata-fainal.

    Duk kasar da ta kai mataki na gaba a tsakaninsu za ta fafata ne da Ingila ko Mexico.

  15. Faransa ta doke Paraguay 1-0

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Faransa ta samu nasara kan Paraguay a zagayen ‘yan 16 na gasar kofin duniya da ke gudana a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Dan wasa Kylian Mbappe ne ya jefa kwallo daya tilo a wasan ta hanyar bugun fenariti a minti na 70, inda a karshe aka tashi Faransa na da ci daya, Paraguay na nema.

    Yanzu Faransa za ta kara ne da Moroko a matakin kwata-fainal, bayan da Morokon ta samu nasara kan mai masaukin baki Canada da ci 3-0.

  16. Morocco ta tsallake Kwata-Final bayan lallasa Canada da ci uku da nema

    Ƙasar Morocco ta samu nasarar tsallakawa zagayen wasannin Kwata-Final a gasar cin kofin duniya, bayan lallasa Canada da ci uku da nema

    are through to the last eight of the World Cup after a ruthless second-half performance in Houston!

  17. Canada 0-3 Morocco

    Morocco ta ƙara ƙwallo ta uku da hannu Soufiane Rahimi a minti 98 da fara wasa.

  18. Canada 0-2 Morocco

    Morocco ta ƙara zura ƙwallo ta biyu, inda ɗanwasan gaba Azzedine Ounahi ya sake jefa ƙwallo a ragar Canada a minti 82 da fara wasa.

    Yanzu dai alamu na nuna Morocco ta kama hanyar tsallakawa zuwa zagaye na gaba.

  19. Canada 0-1 Morocco

    Duniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Morocco ta zura ƙwallo ɗaya a ragar Canada.

    Ɗanwasan Morocco Azzedine Ounahi ya zura ƙwallo a minti 50 da fara wasa, wato jim kaɗa bayan komawa daga hutun rabin lokaci.

  20. Hutun rabin lokaci: Canada 0-0 Morocco

    Kofin duniya

    Asalin hoton, Getty Images

    An tafi hutun rabin lokaci Canada ɗaya daga cikin ƙasashe masu masauƙin baƙi da Morocco na canjaras babu ci.

    Sai dai Hausawa na cewa ba a sanin maci tuwo sai miya ta ƙare.

    A saurari yadda za ta kaya idan an koma filin wasa bayan hutun.