Hudson-Odai ya gama buga wa Forest wasannin kakar nan, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Callum Hudson-Odai ya gama buga wa Nottingham Forest tamaula a bana, bayan da aka yi masa tiyata kan raunin da ya ji.
Maishekara 25 ya ji raunin a karawar da Forest ta yi nasara a Porto a zagayen kwata fainal ranar Alhamis, wanda bai buga gasar Premier da Burnley .
Forest ta tabbatar da cewar an yi wa tsohon ɗan wasan Chelsea cikin nasara, kuma sai a cikin karshen kakar nan ake sa ran zai murmure.
Ƙungiyar da Vitor Pereira ke jan ragama tana da tazarar maki biyar tsakani da ƴan ukun karshen teburi, kuma za ta fafata da Sunderland da Chelsea da NewcastleUnited da Manchester United da kuma Bournemouth a sauran karawa biyar da ke gabanat.
Haka kuma za ta fafata da Aston Villa a zagayen daf da karshe a Europa League a wasan farko ranar 30 ga watan Afirilu.


















