KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 29/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammad da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Kotu ta hana INEC amincewa da babban taron ADC na ƙasa

    hoton alamar jamiyyar ADC

    Asalin hoton, ADC/X

    Wata babbar kotun Tarayya a Abuja ta hana INEC amincewa da babban taron ADC na ƙasa da ta gudanar a baya-bayan nan, sannan ta hana hukumar amincewa ko kuma halartar wani taro da ADC ɓangaren David Mark zai shirya.

    Mai shari'a Joyce Abdulmalik wadda ta yanke hukuncin, ta kuma dakatar da Sanata David Mark da sauran shugabbanin jamiyyar daga shiga ayyukan zaɓɓaɓun shugabannin jamiyyar a jihohi.

    Mai magana da yawun tsagin na Mark, Faisal Kabir ya ce hukuncin bai ba su mamaki ba, amma dole ƴan adawa su fitar da ƴan takara ko ta yaya ne.

  2. Farashin ɗanyan mai ya sake tashi a kasuwannin duniya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyan mai ya sake tashi a kasuwannin duniya, bayan rahotannin cewa Amurka na shirin tsawaita toshe tashohin jiragen ruwan Iran.

    Farashin ɗanyan man Brent ya haura zuwa dala ɗari da sha biyar duk ganga.

    Hakan na nuna ƙaruwar dala biyar kan yadda farashin yake a yammacin jiya Talata.

    Iran ta dakatar da sufurin jirage ta Mashigar Hormuz, muhimmiyar hanyar da aƙalla kashi ɗaya cikin biyar na mai da iskar gas da ake amfani da su a duniya ke bi.

    Mashigar na ci gaba da kasance a rufe duk da tsagaita faɗa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.

  3. Iran ta yanke hukuncin kisa kan fiye da mutum ashirin tun soma yaƙi -MDD

    wani mutum zai rataya kansa, da idonsa rufe da farin ƙyalle

    Asalin hoton, EPA

    Majalisar ɗinkin duniya ta ce tun soma yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, gwamnatin Iran ta yanke hukuncin kisa kan aƙalla mutum ashirin da ɗaya, tare da kama fiye da dubu huɗu.

    An kama da dama daga cikinsu ƙarƙashin dokar tsaro ta ƙasar mai cike ta taƙaddama.

    Sanarwar Majalisar ɗinkin duniyar ta ce an da dama daga cikin fursunonin na fuskantar azabtarwa, wani lokacin kuma a ɓatar da su, yayin da a wau lokutan kuma akan nuna su a talibijin suna amsa aikata laifuka, da kuma barazanar zartar musu da hukuncin kisa.

    Shugaban hukumar kare haƙƙin biladama na Majalisar Volker Turk ya ce ana take wa Iraniyawa haƙƙinsu ta munanan hanyoyi, ya kuma yi Allawadai da katse intanet da gwamnatin ƙasar ta yi.

  4. Jakadiyar Amurka a Ukraine ta ajiye aiki

    Muƙadashiyyar jakadan Amurka a Ukraine ta ajiye aikin ta, a yayin da rahotanni ke cewa ta fusata ne da matsayar Trump kan rikicin da ake yi a can.

    Julie Davies ta soma aikin ne ƙasa da shekara guda, kuma rahotanni na cewa tana ganin Mista Trump ya gaza wajen bai wa Ukraine tallafin da take buƙata.

    Wanda ya gabaceta ma ajiye aikinsa ya yi, inda yake zargin cewa Amurka na lallaɓa Rasha.

    Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta musanta cewa an samu wani rashin jituwa, inda ta jaddada cewa Ms Davis ta yi ritaya ne kawai.

  5. Faransa ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke Mali su gaggauta ficewa

    Titi da ababen hawa na wucewa, sai hayaƙi da ke tashi a nesa

    Asalin hoton, Getty Images

    Faransa ta yi kira ga ƴan ƙasarta da ke Mali da su yi gaggawar ficewa.

    Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana cewa rashin tsaron da ake fama da shi a ƙasar bayan munanan hare haren da mayaƙa masu iƙirarin jihadi ƴan awaren Tuareg suka kai a ƙarshen mako ne yasa ta ɗauki matakin.

    Irin girman harin da mayaƙan suka kai, da kuma janyewar sojojin Mali da na hayar Rasha daga wasu garuruwa ne suka sanya fargaba kan ƙarfin gwamnatin mulkin sojin ƙasar ƙarƙashin Kanal Assimi Goita.

    A jiya Talata, shugaban mulkin sojin yayi wa ƴan ƙasar jawabi, inda ya tabbatar musu cewa an shawo kan lamarin.

    An kuma ga hotunansa tare da jakadan Rasha a ƙasar, da kuma lokacin da ya kai ziyara asibiti.

  6. Najeriya ta buƙaci Afirka ta Kudu ta kare ƴan ƙasarta daga hare haren ƙyamar baƙi

    Yan Afirka ta Kudu suna zanga zanga

    Asalin hoton, BBC/Thuthuka Zondi

    Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NIDCOM) ta buƙaci gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi gaggawar bai wa ƴan Najeriya da sauran ƴan ƙasashen Afirka da ke ƙasar kariya, a yayin da ake samun rahotannin hare haren nuna ƙyamar baƙi da yi musu barazana da kuma tsangwamarsu.

    A cikin wata sanarwa da shugabar hukumar Abike Dabiri-Erewa ta sanya wa hannu, ta bayyana damuwa kan yadda lamarin kai hari kan ƴan ƙasar ke ƙara ta'azzara duk da tattaunawa tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu.

    '' A yayin da mutane da dama ke sa ran samun kwanciyar hankali bayan tattaunawa tsakanin gwamnatocin biyu, lamarin na ƙara tsananta ne,'' in ji ta.

    Hukumar ta ce tana samun rahotannin cewa yara ƴan Najeriya na tsoron zuwa makaranta, yayin da ƴan kasuwa ke ta rufe shagunansu saboda tsoron a kai musu hari, ko a sace kayayyakinsu.

    Ta kuma ce rahotanni sun bayyana an kai sabbin hare hare cikin sa'oi 72 da suka gabata.

    NIDCOM ta shawarci ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu su kasance masu bin doka da oda, kuma su ƙauracewa wuraren da aka fi samun tashin hankalin musamman cikin dare, inda kuma ta tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin haɗin gwiwa tsakanin ofishin jakadancin Najeriya a Pretoria da Johannesburg da kuma ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar domin shawo kan lamari.

  7. 'Yadda na rasa hannuna ɗaya a wajen aiki'

    A ranar 28 ga Afrilu, ana bikin World Day for Safety and Health at Work domin tunatar da duniya cewa irin waɗannan haɗurra ana iya kauce musu.

    Wannan rana, wadda International Labour Organization ta assasa, na ƙarfafa muhimmancin kare ma’aikata daga haɗurran da za a iya hana farawarsu.

    Abubakar Hamza, wani tsohon ma'aikacin wani kamfani ne wanda ya rasa hannunsa ɗaya a lokacin da yake aikin gyara shinkafa.

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyon
  8. Amfani da cin zarafi a matsayin makamin yaƙi a Sudan na shafar lafiyar ƙwaƙwalwar mata -MDD

    Yadda ake yawaita amfani da fyade da sauran nau'ikan cin zarafin mata a matsayin makamin yaƙi a Sudan ya haifar da babbar matsalar ƙwakwalwa a tsakanin mata da 'yan mata.

    Asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa nuna ƙyama da ƙarancin ƙwararrun ma'aikatan kiwon lafiya na kara ta'azzara lamarin.

    Jami'ai sun ce da yawa daga cikin waɗanda lamarin ya shafa na fama a matsalar ƙwaƙwalwar ba tare da sanar da kowa ba, kuma suna bukatar tallafi cikin gaggawa.

    Sukan fuskanci ƙalubale wajen samun kulawa, inda zuwa asibiti ke kasancewa abu mai hatari , yayin da rahotanni ke cewa wasu asibitoci na ƙarƙashin ikon ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

  9. Yadda IS ta kai mummunan hari a Adamawa

    Kalla bidiyon bayanin yadda IS ta kai mummunan hari a Adamawa

    Bayanan bidiyo, Latsa abin da ke sama domin kallon bidiyon
  10. Isra'ila na ci gaba da zafafa hare harenta a kudancin Lebanon duk da tsagaita wuta

    hayaki ya turnuƙe sararin samaniya

    Asalin hoton, Abbas Fakih / AFP via Getty Images

    Isra'ila ta zafafa hare haren da take kai wa a kudancin Lebanon, inda ta ce tana kai harin ne kan sansanonin Hezbollah.

    Rundunar IDF ta ce ta kai hari kan wata hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Hezbollah a birnin Qantara mai tsawon Kilomita biyu, ta hanyar amfani da tan ɗari huɗu na abubuwan fashewa.

    Bidiyon da aka wallafa a intanet sun nuna yadda aka lalata birnin bakiɗaya, da yadda wuta da hayaƙi suka cika sararin samaniya.

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce hare haren Isra'ila na ci gaba da rutsawa da fararen hula da kuma ma'aikatan ceto.

    Ƙasashen biyu dai na ƙarƙashin wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tangal-tangal, wadda hare haren baya bayan nan ke barazanar sake raunata ta.

  11. Saurin da lalacewar dajin Amazon ke yi ya ragu a shekarar 2025 - Bincike

    dajin Amazon

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani bincike da masana kimiyya na Amurka suka gudanar ya gano cewa saurin da lalacewar dajin Amazon ke yi ya ragu a shekarar 2025, bayan asarar da ba a taba samun irinta ba a tarihi a 2024.

    Masu binciken sun ce hakan ya fi nasaba da kokarin da ƙasar Brazil ta yi na dakile sare dazuzzuka a yankin Amazon.

    Sai dai binciken, wanda cibiyar World Resources Institute da kuma jami'ar Maryland suka gudanar ya kiyasta cewa har yanzu ana asarar kusan murabba'in kilomita dubu arba’in da uku na tsofaffin dazuzzukan.

    Wannan yanki ya yi daidai da girman ƙasar Denmark, ko kuma daidai da bacewar filayen ƙwallon ƙafa goma sha ɗaya a kowane minti.

    Binciken ya nuna cewa duk da cewa tsauraran dokokin kare muhalli na iya yin tasiri, har yanzu asarar filayen dazukan ta zarce wadda ake samu shekaru goma da suka gabata yawa.

    Masana kimiyyar sun kuma yi gargadin cewa ƙaruwar yanayin zafi na iya ƙara haddasa gobarar daji a ƙarshen wannan shekara.

  12. Mun ci galaba kan abokan gabanmu da ƙarfin soji - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    A yayin da ya ke karɓar baƙuncin Sarki Charles na 3, Shugaban Amurka Donald Trump ya ɗan yi tsokaci game da rikicin Gabas ta Tsakiya, inda ya ce Amurka na ‘ƙoƙari’ a yaƙinta da Iran.

    ‘’ Mun ci galaba kan abokan gaban mu da ƙarfin soji’’ in ji shi, ba tare da ambato Iran ba.

    Ya kuma ƙara da cewa ‘’ ba za mu taɓa bari abokan gaban mu su mallaki makaman nukiliya ba, Charles ma ya yarda da hakan, fiye ma da ni’’.

  13. Yan sanda sun kama wanda ake zargi da shirya harin bom mafi muni a Colombia

    yansandan colombia

    Asalin hoton, Getty Images

    Yan sandan Colombia sun ce sun kama wani uban daba da ake zargi da shirya harin bom mafi muni da aka kai wa fararen hula a ƙasar cikin shekaru da dama.

    A ranar Asabar ne mutane 21 suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a harin da aka kai kan wata babbar hanya a kudu maso yammacin Colombia.

    Wakilin BBC ya ce sojojin Colombia sun haɗa kai da ’yan sanda a wani samame da suka kai domin cafke José Vitoncó a birnin Palmira da ke yammacin ƙasar.

    Shugaban ƙasar, Gustavo Petro, ya bayyana harin a matsayin “na ta’addanci”, yana mai cewa wata ƙungiyar masu safarar hodar iblis ce ta kai shi, wadda ke da alaƙa da Iván Mordisco, wanda ake nema ruwa a jallo a ƙasar.

  14. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da kasancewa damu a shafinmu na BBC hausa kai tsaye na yau Laraba.

    Kamar dai yadda aka saba wannan shafi ne da zai kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, da Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu, kuma za ku bibiye mu a shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook, X, Instagram da kuma YouTube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.